Connect with us

JAKAR MAGORI

Uba Ya Yi Wa ’Yar Shekaru 13 Ciki

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Ogun ta samu nasarar cafke wani magidanci mai suna Kayode Oladeinde, wanda yake zaune a kan titin Olope da ke yankin Ogijo, bisa laifin yi wa yarinyarsa mai shekaru 13 ciki. An dai cafke Oladeinde dan shekara 50 bayan da matarsa ta kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sandar Ogijo da ke cikin karamar hukumar Obafemi Owode ta jihar.

Majiyarmu ta ruwaito mana cewa, matar ta sami labarin lamarin ne lokacin da yarinyarta ta bayyana mata cewa, Oladeinde yana saduwa da ita.

Oyeyemi ya bayyana cewa, lokacin da aka tuhume shi, Oladeinde ya amince da laifinsa, inda ya bukaci yarinyar da mahaifiyarsa su yafe shi. A cewar Oyeyemi, matar Oladeinde ta bayyana wa ‘yan sanda cewa, yarinyarta ta fada mata cewa, tun a ranar 4 ga watan Fabrairu wanda ake zargi ya fara yin lalata da ita, sakamakon haka, a yanzu tana da juna biyu. Matar ta kara da cewa, majinta yana bai wa yarinyar wasu magunguna, inda yake ta kwanciya da ita har sai da ta sami juna biyu. Lamarin ya sa yarinyar ta ke ta jubar da jini. “Lokacin da ‘yan sanda suka sami rahoton lamarin, nan take DPO na yankin Ogijo, CSP Suleiman Muhammad ya tura yaransa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka sami nasarar damke wanda ake zargi,” in ji Oyeyemi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: