Connect with us

MANYAN LABARAI

Yakamata Duniyar Kwallon Kafa Ta Yi Wani Abu Kan Lafiyar Pele – Ronaldo

Published

on

Yakamata Duniyar Kwallon Kafa Ta Yi Wani Abu Kan Lafiyar Pele – Ronaldo

 

Tsohon dan wasan Brazil, Ronaldo, ya yi kira ga duniyar kwallon kafa da ta tashi tsaye, domin ganin ta tunkari halin da tsohon gwarzon duniya Pele ya ke ciki, saboda ganin ya cigaba da rayuwa cikin farin ciki.

Rahotanni daga Brazil na nuna cewar tsohon tauraron kwallon kafar duniya, Pele, na fama da tsananin rashin lafiya; abinda ke hana shi fitowa daga gidansa, saboda yadda ba ya iya tafiya da kafafuwansa har sai an tura shi a keken guragu.

Dan tsohon tauraron kwallon kafar, Edinho ya ce, mahaifinsa mai shekaru 79 na fama da matsalar motsa kugunsa, abinda ke sa shi yawan tunani da ke shafar lafiyarsa bakidaya kuma ya na bukatar kulawa ta musamman.

Edinho ya ce, Pele na matukar jin kunyar fita bainar jama’a ana tura shi a keken guragu, la’akari da yadda ya yi rayuwar sa a matsayin Tauraro a fagen kwallon kafa, wanda ake girmamawa a kowacce kasa da ke duniya.

Har yanzu mutane da dama na kallon Pele a matsayin dan kwallon da ya fi kowa fice a fagen kwallon kafar duniya, kuma har ya zuwa yau shi ne dan wasa daya tilo da ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku a rayuwar sa, a shekarar 1958 da 1962 da kuma 1970.

Ya zuwa yanzu dai Pele ya takaita fita bainar jama’a tun bayan ziyarar da ya kai Paris a watan Afrilun bara, inda ya halarci wani biki tare da tauraron kwallon kafar Faransa Kylian Mbappe sannan a shekarar 2014 an kwantar da shi a asibiti saboda matsalar cutar koda wadda ta shafi mafitsarar sa.

Rahotanni sun ce yanzu haka tsohon gwarzon dan wasa na da koda guda daya ne, bayan karya kashin hakarkarin sa wanda ya tilasta cire masa kodar kuma Edinho ya ce mahaifin na sa na cikin yanayi mai kyau a yanzu haka.

Sai dai Ronaldo, wanda akayi hasashen banda Pele babu kamarsa a Brazil din ya bayyana cewa akwai bukatar duniya ta shiga rayuwar Pele domin sanya farin ciki a rayuwarsa saboda kada ciwon damuwa ya kamashi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: