Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kone Iyalin Gida Na Mutum 16 A Kaduna

Published

on

Kimanin iyalan wani gida su 16 ne wasu ‘yan bindiga suka tattara su a cikin daki guda sannan suka banka masu wuta inda suka kone kurmus a wani farmaki da ‘yan bindigar suka kai a kauyan Bakali, da ke gundumar Fatika, a karamar hukumar Giwa, ta Jihar Kaduna.

An bayar da rahoton ‘yan bindigar sun kai farmaki a kauyan ne a ranar Talata da misalin karfe 4 na yammaci, inda ba tare da bata lokaci ba su ka shiga cinna wuta a buhunan hatsi, motoci da baburan hawa da suka taras a kauyan.

An ce ‘yan bindigar sun tattara iyalan wani gida guda ne su 16 a cikin wani daki sannan suka cinna masu wuta har sai da suka kone kurmus.

Wani mazaunin kauyan mai suna, Alhaji Sani Bakali, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin ga wakilinmu ya ce, sama da ‘yan bindiga 100 ne su ka kewaye kauyan na su inda kuma su ka shiga aikata ta’asar.

Kawo lokacin hada wannan rahoton ‘yan sanda bas u fitar da wani bayani ba a kan faruwan lamarin.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: