Connect with us

RAHOTANNI

’Yan Bindiga Sun Kone Mutum 20 Da Ransu A Karamar Hukumar Giwa

Published

on

‘Yan bindiga sun kone kimanin mutum 20  tare da yin harbin kan mai uwa da wabi lokacin da su ka kai hari a kauyen Bakali da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kulle wasu mutane daga cikin wanda harin ya rutsa ne a daki kana suka  banka masa wuta suka kone kurmus.

Ya zuwa hada wannan rahoho dai komai ya lafa kuma shugaban karamar hukumar da DPO na yankin su na kai-komo a kan lamari, don kwantarwa da jama’a  hankula, kuma wadanda su ka gudu su na komawa gidajensu.

Wani mazaunin yankin da kwanansa na gaba cewa ya yi kimanin ‘yan bindiga 100 su ka yi wa kauyen dirar mikiya.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ya zanta da dan majisar jiha mai kula da yankin da lamarin ya faru wato Giwa ta Yamma ta wayar salula, Hon. Rilwanu Aminu Gadagau, inda ya ce, “an kai harin ne ranar Talata da misalin karfe hudu na asubahi, inda su ka banka wa buhunhunan hatsi da ababen hawa da babura wuta wanda ya zuwa yanzu ba za a iya gane iya asarar da a ka yi ba.”

Kuma ya ce, “a yau Laraba ne a ka yi jana’izar mutanen guda 20 a kauyen na Bakali, kuma shida daga cikin mutanen an yi jana’idarsu ne a garinsu.”

Hon. Gadagau ya ce, lamarin abin tausayawa ne matuka, amma ya roki Allah ya kawo karshen lamarin a kasa bakidaya.

Karshe ya mika sakon ta’aziyyarsa da iyalan wadanda su ka riga mu gidan gaisuwa kuma ya ce za su bayar da kulawa idan Allaha ya so.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: