Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Abubuwan Da Allah Ya Ba Annabi Muhammadu (SAW) Shi Kadai (1)

Published

on

A uzu billahi minas shaidanin rajim. Bismillahir rahmanir Rahim. Wa Sallallahu ala Nabiyyil Karim. Masu karatu assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barkatuh.

Kwana biyu mun yi karatun cewa duk wani abu da Allah ya ba Annabawa, Allah ya ba Annabi Muhammadu (SAW) irinsa, sannan shi kuma Allah ya kebance shi da nasa shi kadai wanda bai ba Annabawa ba. Imamu Suyudi ya yi litafin Khasa’isul Kubra wanda a ciki sai da ya kawo abubuwa duba da Allah ya ba Annabi Muhammadu (SAW) shi kadai.

Shehu Sukairajul Ayyashi, shi ma ya fitar da Khasa’isu (kebance-kebance) na Annabi (SAW) guda dari biyar. Shehunmu Yusufun Nabahani shi ma a cikin littafinsa Anwarul Muhammadiyya ya fitar da wani abu daga cikin abubuwan da Manzon Allah (SAW) ya kebanta da su shi kadai wanda a ciki za mu dora karatunmu a kai, in sha Allahu.

Nabahani yake cewa, yana daga abin da Manzon Allah (SAW) ya kebanta da su na daga Mu’ujizozi da abubuwan da Allah ya daukaka Manzon Allah da shi a kan sauran Annabawa na daga girmamawa wadanda sun fi rana fitowa a fili. Allah ta’ala ya kebanci Annabi Muhammadu da abubuwan da bai taba ba wani Annabi da ya zo kafin shi ba (SAW). Haka nan duk abin da aka kebanci wani Annabi da shi sai ka ga an bawa Annabinmu irin nasa. Idan an ce an bawa Annabawa Annabta, to Annabinmu (SAW) an ba shi wannan Annabtar tun Annabi Adamu (AS) yana tsakanin rai da yunbunsa (tun kafin a busa masa rai), amma kowane Annabi sai da ya zo a zamaninsa tukuna sannan aka ba shi Annabtar da, idan Manzo ne kuma sai lokacin aikensa ya yi ake ba shi Manzanci. Galibi ma sai sun cika shekara arba’in da haihuwa kafin a ba su, amma Annabinmu (SAW) tun Azal aka ba shi Annabta. Yayin da aka ba Annabi (SAW) wannan matsayi, sai muka san cewa shi ne yake wa dukkan halitta madadi kuma ya kasance cikakke (a wurin Allah) tun kafin a yi su (Annabawa).

Imamul Busiri ya ce, “duk wata Mu’ujiza da Annabawa manya suka zo da ita sun same ta ne daga hasken Manzon Allah. Domin shi Annabi Muhammadu (SAW) shi ne rana (wurin falala), sauran Annabawa kuma su ne Taurarinta”. Masu ilimin abin (na rana da wata) sun ce dukkan Taurari har da Wata idan rana ta fito suna daukar haskensu ne daga gare ta, wato za su yi cajin batirinsu, da wannan cajin ne suke ba mutane haske da daddare idan duhu ya yi. Ko da rana suna nan, amma hasken rana ya shafe su. To, kowane Annabi da ya zo ya dibi haskensa ne daga na Annabi Muhammadu (SAW). Malam Danmarzuki ya ce, abin da (Imamul Busiri) yake nufi shi ne, kowace Mu’ujiza da kowane Annabi ya zo da ita, ta sami wannan Annabin ne daga hasken Annabi Muhammadu (SAW).

Annabi Adamu (AS), Allah ya girmama shi da abubuwa da yawa. Allah ya ce ya gina shi ne da hannayensa guda na kudura (yadda ya dace shi SWT). Allah ya ce wa Ibilis “don me ka ki yin sujada ga abin da na halitta da hannayena guda biyu?”, wannan girma ne kwarai da gaske. Misalin yadda za a fahimci wannan, duk in ka je super market (babban kanti) za ka yi sayayya, idan ka dauko abu sai ka duba ka ga a ina aka kera ko sarrafa wannan abin, a nan za ka san girmansa da darajarsa. To, idan kana so ka san girman Dan Adam sai ka duba cewa daga wace ma’aikata aka kera shi, Allah ya ce da hannayensa guda biyu (yadda ya dace da shi SWT). Don haka ba ka taba jin mutum yana cikin tafiya haka kawai ka ga hannunsa ya fadi ba, ko hancinsa, ko idonsa ba, domin ya dauru da notin Allah. Amma abubuwan da ba Allah ne ya kera su ba kamar mota, ana cikin tafiya sai ka ga tayarta ta fita ko wani abu ya cire. Saboda haka fadar da Allah ya yi cewa ya halicci Annabi Adamu da hannunsa girmamawa ce sosai. Amma kuma da aka zo wurin Annabi Muhammadu (SAW), sai Allah Ta’ala ya ce, “Ba ni ne (gabadayana) na yalwata kirjinka ba?”, ma’anar yalwata kirji ‘sanya dabi’un Annabta’. Allah ya rantse da dabi’un Manzon Allah (SAW) kyawawa, inda ya ce wallahi ya Rasulallah kana kan dabi’u masu girma, a cikin Suratu Nuun. Allah Ta’ala ya nuna sanya wa Manzon Allah (SAW) dabi’u masu girman nan a kirjinsa da dukkan kansa (SWT) ya yi. Ita kuwa halittar Annabi Adamu (AS) da hannaye biyu ne aka yi. Ta nan Malamai suka ce lallai kyawawan dabi’u su ne cikar Dan Adam, domin komai kyan mutum in ba shi da dabi’u masu kyau ya zama banza, ya yi kyan dan maciji.

Haka nan Malamai sun ce a halittar da Allah ya yi wa Annabi Adamu ya ba wa wasu dama suna sarrafa ta. Za ka ga likitoci tun suna yi wa mutane wani sashe na jiki da roba ko katako, yanzu fasaha ta kai har suna datse gabar wani su sanya wa wani, kamar yadda suke cire kodar mutum mai lafiya su dasa wa wani mara lafiya. Amma ba ka taba jin an ce ga wani yaro ya lalace ya zama dan iska an kai shi wurin likita ya yi masa tiyata ya cire masa iskancin nan ba ya sa masa halin kirki.

Yana daga abin da Allah Ta’ala ya bawa Annabi Adamu (AS) ya hori Mala’iku su yi sujada gare shi. Dangane da wannan, Malam Fakruddinir Razi ya ce a cikin Tafsirinsa, an hori Mala’iku su yi wa Annabi Adamu sujada ne saboda hasken Annabi Muhammadu (SAW) yana kan goshinsa. A lokacin da Allah ya umurci Mala’iku su yi wa Annabi Adamu sujada duk sun yi sai Ibilisu ne ya ki yi. Allah ya tambayi Ibilisu, shin ka ki yin sujada ne ga abin da na halitta da hannayena guda biyu (yadda ya dace da Allah) saboda girman kai ko kuma don kana cikin Mala’iku Alliyai (madaukaka) ne da ban umurce su yi ba? (Malam Tafsiri da yawa suna da maganganu a kan shin su wane ne Alliyna). Sujadar Annabi Adamu ba dukkan Mala’iku suka yi ba, tun da ga nau’in Alliyna ba su ba, sannan ga Ibilis shi ma bai yi ba. Amma idan aka zo wajen Manzon Allah (SAW), Imamu Sahalu Ibn Muhammadu ya ce, wannan girmamawa da Allah ya yi wa Manzon Allah da fadinsa na cewa, “Allah da Mala’iku suna yi wa Annabi Salati. Ya ku wadanda suka yi Imani ku yi Salati gare shi..” kuma da fi’ili mudari’i (aikin da ake cigaba da yi babu tsayawa) ya daukaka fiye da na sujada. Domin waccan sujadar an yi an gama tuntuni, amma Salatin da Allah da Mala’iku da Muminai suke yi wa Manzon Allah (SAW) ana cigaba da yi babu tsayawa kuma ba adadi. Ka ga ba za a hada da abin da Allah ya ba Annabi Adamu (AS) ba, domin wanda aka ba Annabi (SAW) shi ya fi cika, saboda Allah yana cikin masu yi, na Annabi Adamu (AS) kuma Allah ba ya cikin wadanda suka yi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: