Connect with us

WASIKU

‘Akwai Abin Da Aka Yi Wa Gurguwar Fahimta Bisa Dora Talauci A Arewa’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.

Dan Arewa ba rago bane sam. Amma akasarinsu ba su da burin samun gagarimin arziki sai dai su ce rufin asiri. Sun dauki wadatar zuci a matsayin rage buri. Wannan ya sa da zaran ya cimma wani karamin burinsa kamar daki ko gidan da zai saka matarsa sai kawai ya yi sakwa-sakwa da hanyoyin neman arziki. Idan har ana son maganin talauci a Arewa sai an ilmatar da su hakikanin ma’anar “wadatar zuci” cewa ba yana nufin rage buri bane, a’a yana nufin ka wadatu da halal, ka wadatu da naka kada ka saci na wani.

Malaman addini na da matukar rawa da za su taka a kan wannan ilmantarwan.

 

Sako daga Sani Yushau Salsabil (sys).

08037864862

 

“Yunkurin Tayar Da Bom A Majami’a: Ko Mutane Sun Koyi Darasi?”

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.

A lokacin da muka zo kammala karatu a tsangayar Mass Communication, na nemi shugaban tsangayarmu (department) da ya amince na yi “project” a kan yanda ‘ƴan jarida suke siffanta ta’addanci (Media Framing of Insurgency) da kuma tasirin shi ga al’umma.

A wannan lokaci wanda zai lura da bincike ne a kan wannan darasi da na zaba shi ne shugaban department. Kuma na yi sa’a ya amince min da wannan topic cikin gaggawa kuma ya tabbatar min yana da manufa a cikin Project dina.

Dalilin da ya sa na zabi wannan topic shi ne, yanda ‘yan jarida suka dukufa wajen siffanta ayyukan ta’addanci da fahimtar su, a madadin su bar jama’a su yi alkalancin abu yanda ya zo musu.

A takaice Framing bai tsaya ga interpretation ba, abu ne wanda ya kai ga redefinition of phenomenon. Wato sake bai wa wani abu ma’ana na daban saboda fahimta (understading).

A ilimin tunanin Dan’adam, Psychology, fahimta fuska ce. Bambamcw-bambamcen mutane na tasiri kwarai ga fahimtar mutum. Kazalika manyan abubuwa na rayuwa kamar su tushen ilimi da addani da bangarenci da dai sauran su suna shafan fahimtar mutum. Wannan ya sa fahimta wanda a wasu wuraren zamu iya kiran shi ra’ayi, ba zai taba zama garkiyan lamari ba.

A tsawon lokacin da fitinar Boko Haram ya fara a Nijeriya, manyan Jaridu wadanda mafi yawancin su, suna yankunan kudancin kasar nan ne sun bai wa fitinar ma’anar addini. Wanda abin da kungiyar take ikirari kenan.

Amma idan mutum ya yi zurfi cikin nazarin al’amuran da suka faru ta hanyar tattara bayanai daga ingantattun majiya, za ka fahimci cewa babu bangare guda daya daga cikin addinin Musulmai ko Kirista da Boko Haram take karewa martaba. A zahiri kungiyar na ikirarin kafa shari’ar musulunci ne a kasar nan, amma idan ka bincika sai ka ga barnar da kungiyar take yi wa musulunci ya ninka barnar ta a kowani bangare. Saboda wannan ita ce kungiya da ta fara da kashe manyan malaman addini, wanda kuma wannan shi ne hanya mafi sauki na jefa al’umma cikin rudani ta hanyar tilasta musu maraici a ilimi.

Haka kuma kungiya ce da ta bi masallatai tana sanya Bama-bamai tana kashe masallata. Ni da kaina Allah ne ya kare ni, amman sun taba dasa bom a masallacin da muka je budewa. Amma a hakan ‘yan jaridu suka ci gaba da alakanta kungiyar da musulunci, wanda kuma hakan ya kara surantawa wadanda suka jahilci abun a matsayin cewa, Biko Haram suna kare martabar musulmai ne.

Wannan ne ya sa lokacin da aka kama wani matashi Kirista, Samuel, zai tayar da bam a Coci, wasu suka dauka cewa Musulmi ne kawai zai iya aikata irin wannan. Saboda daman an siffanta musu musulunci da ta’addanci.

Amma shi ta’addanci na dan ta’adda babu ruwan shi da addini ko siyasa ko kabila ko jinsi ko yanki. Sai gashi ya bayyana Samuel fastor ne mai jiran gádo.

Wannan yana nuna dole mutane su yi taka tsantsan wajen daukan labari daga jaridu, su yi bincike a kan kowani labara, saboda ‘yan jarida na yandu ba masu bicike ba ne.

Sako daga Mahmud Isa, Yola.

 

08106792663

 

“Ko Buhari Ya Manta Da Dalilin Da Ya Sa ‘Yan Nijeriya Suka Zabe Shi” Assalamu alaikum, LEADERSHIP AYAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke ci mana tuwo a kwarya tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku adu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya.

Idan maye ya manta to… A gaskiya mu koma baya mi yi nazari! masu mulki suna kwashe dukiyar kasa, talakawa na shan wahala, sai talaka da mai mulki ba sa jituwa. Buhari ya zo ya ce, zai taimaka wa talakan Nijeriya idan ya sami darewa karagar mulki. Sai suka yarda da shi har Allah ya bada nasara, talakawa sun sa rai su ga alkawari ya cika, sai suka ji shiru, ga shi lokaci ya ta fi.

Shawarata ga gwamnatin Baba Buhari shi ne, Nijeriya muna da komai abu daya muka rasa shi ne, kyakkyawar dabi’a, ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen cusa wa al’umma kishin kasa. Idan al’umma ta zama mai kishi, to akwai yiwuyaar tsaro zai samu, sannan arzuki zai bunkasa, kuma kasa za ta zauna lafiya. Shawara ta biyu, gwamnatin Baba Buhari, ta yi sulhu tsakanin talakawa da masu mulki, saboda talakawa sun zabi Buhari ne dan ya karbo dukiyar da aka sata, ya ba su a matsayinsu na ‘yan kasa, sai dai hakan bai samu ba saboda dan zaki ya girma. Ya kamata a yi sulhu da manya na kasa, domin shi ne mafita, saboda su suke da kudi, suke da yara a cikin gwamnati soja da ‘yan sanda da mukamai na siyasa, sannan suke da kasuwanci. Idan fada ya fi karfinka sai ka maida shi wasa. Na gode, Allah ya taimaki wa masu kishin kasa.

Sako daga Khalid Abubakar.

07039631828.

 

“Kira Ga Shugaban Kasa”

Assalamu alaikum, LEADERSHIP AYAU JUMA’A. Edita dan Allah ina so ka bani dama domin in yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, masamman a kan wannan kungiya ta tsaro da wasu daga cikin gwamnonin kudancin kasar nan suka kafa wato amotekun kuma yanzu gashi gwamnonin arewacin kasar nan suma za su kafa tasu kungiyar ta wadda suka sanyacwa suna “shege kafasa”. Nan gaba kadan bangaren inyamurai suma sai sun kafa tasu. An ya wadannan kungiyoyi za su zama alkhairi ga kasa kuwa?

Dan haka ya kamata shugaban kasa ya gaggauta rushe wadannan kungiyoyi, domin yin hakan zai iya bai wa masu ikirarin raba kasar nan biyu damar aiwatar da mammunar manufarsu ta yin amfani da wadannan kungiyoyi. Allah ya sa ka duba maganata da idon basira, amin.

Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura.

08164205067
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: