Connect with us

WASANNI

An Hana Ighalo Shiga Filin Daukar Horo Saboda Coronavirus

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa an hana sabon dan wasan Manchester United, Odion Ighalo, shiga filin daukar horo na kungiyar saboda tsoron cutar numfashi ta Coronavirus wadda ta samo asali daga kasar China.

A ranar da za’a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta watan Janairun da ta gabata ne dai Ighalo ya koma Manchester United daga kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua wadda take kasar China.

Ighalo bai je wasannin atisaye da kungiyar ta yi a Spaniya ba, sakamakon tsoron yada cutar coronavirus dalilin da aka hana shi takardar izinin shiga kasar kuma ya zauna a kasar Ingila domin ci gaba da daukar horo shi kadai.

Tsohon dan kwallon Watford din ya koma buga gasar China a shekarar 2017, inda ya fara da kungiyar Changchun Yatai sai dai bayan da ya buga kakar wasa biyu sai ya koma Shanghai Shenhua wadda ya buga wa wasanni 19 ya kuma ci kwallo 10.

Sai dai kamar yadda rahotanni daga kasar ta Ingila suka bayyana, Ighalo baya samun damar shiga filin daukar horon kungiyar saboda tsoron kada ya yada cutar ta Coronabirus kafin ‘yan wasan kungiyar su dawo daga kasar Sipaniya.

Amma kuma duk da haka, tsohon dan wasan tawagar Super Eagles din yana cikin ‘yan wasan da za su fuskanci kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a gasar firimiya ranar Litinin kamar yadda kociyan Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: