Connect with us

WASANNI

Chelsea Ta Sayi Hakim Ziyech Daga Ajax

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta amince da sayan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ajax, Hakim Ziyech, akan kudi fam miliyan 38 a bana kamar yadda kungiyar ta Ajad ta bayyana a jiya Alhamis.

Dan wasan mai shekara 26, yana daga cikin ‘yan wasan da kociyan kungiyar Frank Lampard ya so ya buga wa Chelsea wasa a Janairun nan sai dai kuma Ajad ce ba ta sayar wa da Chelsea dan wasan ba, ganin tana fatan lashe kofin kasar Netherlands a bana.

Dan wasan na tawagar Morocco shi ne zai zama na farko da Lampard zai kai Chelsea, tun bayan da aka amince kungiyar ta sayi ‘yan kwallo kuma kungiyar ta yiwa mai koyarwar alkawarin zata bashi makudan kudade domin gyara tawagar tasa.

A baya ne hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta dakatar da Chelsea daga sayen ‘yan kwallo, bayan da aka sameta da laifin karya ka’idar sayen matasan ‘yan wasa kuma sai da kungiyar tayi kakar wasa daya da rabi bata sayi dan wasa ko daya ba

An alakanta Chelsea da sayen ‘yan wasa da dama a watan Janairu ciki har da dan kwallon Paris St-Germain, Edinson Cabani da na Napoli, Dries Mertens sai dai har aka rufe kasuwar babu wanda kungiyar ta samu damar kulla yarjejeniya dashi acikinsu.

Mai koyarwa Lampard ya fuskanci dalilin da ya sa suka kasa sayen ‘yan kwallo a Janairu da ya hada cewar kungiyoyi ne suka ki amincewa su sayar, ba laifin masu sayo ‘yan wasa a Chelsea ba ne.

Kuma dan wasa Ziyech yana daya daga cikin wadanda suka ci wa kungiyar kwallon kafa ta Ajad kwallaye a wasan da suka tashi da Chelsea 4-4 a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a cikin watan Nuwamban shekarar data gabata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: