Connect with us

ADABI

Daga Littafin Bakar Guguwa (23)

Published

on

“Me kake so ka fadan ya Nauman? Jamila ba bakuwa bace ko menene zaka iya fada a gabanta” murmushi yayi tare da fadin “wannan magana ce tsakanin yaya da kanwarsa, ina so kiyi hakuri ki fara rakata idan kin dawo sai mu tattauna kan maganar” ranta a bace take kallonsa jamila dake tsaye tana saurararsu murmushi kawai tayi tare da cewa “ba sai kin raka ni ba, ki tsaya ki saurare shi kawata ni zan tafi” tayi gaba, da sauri Zarah ta bita a baya yayin da zuciyarta take cike da damuwa kirjinta nata bugawa dan tsoron abinda zai ce yazo. Ganin hakan yasa jamila fada mata cewa “ki danne zuciyarki ko me zai sanar da ke ki tsaya ki saurare shi kiyi kamar dai yadda na baki shawara dazu, in kikai hakan zai fi.” godiya zarah tayi mata ganin yadda take kokarin kyautata mata, sai da suka shafe tsawo mintuna suna dada tattaunawa a waje sannan Jamila ta tafi. Duk dadewar da suka yi Nauman na tsaye yana jiran karasowar ta, mamaki ne ya kamata ganin yadda ya bata lokacinsa a banza daura fuska tayi yayin da take karasawa inda yake tsaye tana isa tace “to gani ya Nauman me kake so ka fadan” ji yayi ya kasa maganar ya bita da kallo kawai ta kuma magana “ko ka fasa fadan maganar da kace zaka fadan?” har yanzu shuru yayi ganin ba shida ta cewa yasa ta juya tare da fadin “bari na tafi tunda ba kada abin fada” da sauri yace “karki tafi Zarah haba kanwata” murmushin takaici tayi musamman yadda taji ya kirata da kanwarsa ta tsaya tana kallonsa cike da rashin fahimtar inda ya dosa “ina jinka sauri nake” a hankali ya runka magana ba tare daya kalli kwayar idonta ba “daman ina so na fada miki cewa….” ta tsure shi da kallo tana suararensa “ka fada mini me?” ya kuma maimaitawa cikin muryarsa ta in-ina “daman ina so na fada miki cewa ina sonki” bakin nasa ta bi da kallo yayin da yake furta kalmar sa’annan tayi murmushin takaici “hmm kana sona?” shima murmushi yayi na farin ciki tare da rausaya kai “kwarai” sai da tayi ajjiyar zuciya me karfi kafin tace “sai dai kuma ka makaro ya Nauman dan wani tuni ya ruga ka na ruga dana mallakawa mamallakin zuciyar zuciyarsa sai dai kuma ka nemo ta wata amma banda tawa” dai-dai nan ta fara wani tunanin na daban jikinta ne yayi sanyi bayan data gama furta kalmomin ba komai ta fara tunani ba sai inda zata ga Najeeb a guje ta karasa gida ta bar shi nan tsaye baki bude yana mamakin irin maganar data furta masa shikkenan tana nufin ya rasa ta? Abune wanda ba zai taba sakuwa ba, zuciyarsa ce take raya masa hakan, ya daure fuska ya futa daga gidan. Zarah na shiga bata kalli inda mommy take zaune ba, kai tsaye dakinta ta wuce tana kuka, Hajjiya Usaina dake zaune tana jiran karasowar Abban Zarah ta ganta ta shigo tana kuka ganin Zarah na kuka yasa ta bita da kallo tare da fadin “lafiya?” wucewa Zarah tayi ba tare data tsaya ba ta nufi dakinta, Hajjiya Usaina ta gama lura da irin halin da ‘yarta take ciki na damuwa sai dai kuma ta kasa yi mata bayanin komai ta mike da nufi shiga dakin Zarah kenan ta ji yo sallamar Abban Zarah ya dawo fasa shiga tayi ta isa inda yake ta karbi jakar hannunsa tare da yi masa sannu da zuwa suka karasa sashin sa.

______★

Haj.Saratu na tare da kawarta Hajiya Hafsatu suna hira a falo ta mike ta nufi kitchen dan duba girkin data dora shigarta keda wuya ta jiyo muryar Yesmin na rafka sallama da sauri ta fito daga kitchen cike da mamakin dawowarta Yesmin ta shigo hannunta ruke da jakar kayanta, mamaki ya kara kama Hajjiya Saratu tace “lafiya? ya naga kin dawo ke da kika ce kwana biyu zaki? meya faru kika dawo?” ala dole Yesmin ta saki ranta dan kar Hajjiya Saratu ta gane damuwar dake fuskarta tace “fasawa nayi sabida munyi waya da fadila tace zata zo, naga ba dadi tazo taga bana nan gari ya gari shiyasa na dawo” sai a lokacin zuciyar Hajjiya tayi sanyi jin yadda tayi mata bayani tace “kinyi tunani sosai amma dai ba da kanki kika tawo ba ko?” dariyar yake Yesmin ta kuma yi sannan tace “ba ni kadai na tawo ba Isah driber na yiwa waya yaje ya dauken” sosai Hajjiya tayi farin ciki tace “shiga ciki ki ajjiye kayan naki nima yanzu zan shigo” Safara’u me aiki ce ta tawo da sauri ta karbi jakar hannun Yesmin suka karasa ciki. Tana shiga taci karo da Hajjiya Hafsatu zaune ta kurawa TV’n dake falon idanu, durkusawa Yesmin tayi har kasa ta gaida ita fuskarta cike da walwala ta amsa daga nan Yesmin ta wuce daki, Hajjiya ce ta shigo ta nemi waje ta zauna Haj.Hafsatu tace “sannu da aiki, kina kokari ga ‘yar aiki amma kike shiga kitchen da kanki? Shiyasa fa ‘yan aikin suke sangarcewa suna samun damammaki da yawa, nifa kin ganni nan? babu wata ‘yar aiki da zan dauko na barta ta huta ni na aikatu” duk wannan bayanin da take Hajjiya Saratu murmushi take tana saurararta har sai da ta zo dai-dai nan a zancenta sannan tace “Hmm.. Ba wai haka bane bana barinta tayi masa girki idan iya namu ne sai tayi amma na mijina bana bari tayi masa komai da kaina nake masa shi kansa baya yarda yaci girkin da ba ni na girka ba” dariya Hajjiya Hafsatu tayi “shiyasa ni ba ruwana da wata ‘yar aiki ni da kaina ya wadatar ba sai na janyowa kaina abinda yafi karfi na ba, zancen kuma baya son cin duk girkin da ba naki ba hhh…bar maza Hajjiya Saratu ba’a yabonsu dan muddin kika yabi namiji yanzu yasa kiji kunya dan sai su baki mamakin da baki taba tsammani ba, nifa ko ba zan taba yadda da dadin bakin da namiji ba yana fadan ta ke wucewa ta daya kunnen zaki yi mamakin namijin da zai ce shi baya son abu kaza sai na matarsa. a waje in kika ga yadda yake sai kin ruke baki ni ai naga darasi irinsu masu cika bakin sunfi kowa tsiya ke dai kawai ki iya takun ki” shuru Hajjiya Saratu tayi tana sauraranta har ta gama sannan tace “Allah ko?” tace “sosai ma ba ga sa’adatu ba mijinta ba irin yabonta da baya yi yana cewa har abada ba zai tabai mata kishiya ba kullum yana nan-nan da ita duk inda ta shiga tana cika bakin irin son da yake mata da kuma cewar da yayi ba shi ba yi mata kishiya karshe sai ranar daurin aurensa da aka taru za’a dunguma gidan su amaryar taji labari kinga ai namiji ba abin yarda bane” mamaki ne ya kama Hajjiya Saratu tace “maganarki da kamshin gaskiya ni kaina wani lokacin in na zauna ina nazari sai wata zuciyar tace mun ki kyale kawai insha Allahu ba zaki samu wata matsala ba sai kiga na ware” Hajjiya Hafsatu tace “sai dai addu’a zamu runka taya su da shi kin san ance addu’a takobin mumuni, hmm naga Yesmin ta girma yarinya ta zama budurwa yanzu tana wanne ajji ne?” “yanzu tana ss 1 bata dade da shiga ajin ba, Yesmin nada garin jiki girman kawai ne duk babu wani shekaru” “duk da haka in akai mata aure tsaf! zata zauna” murmushi Hajjiya Saratu tayi ” aure kuma? Ai tayi yarinta da yawa” dariya Hajjiya Hafsatu tayi “Me zai hana ta zauna? ake yiwa ‘yan shekara sha biyu ma bare ita?” fidda idanu Hajjiya Saratu tayi tare da fadin “ko dai baki ganta sosai ba ne?” nan ta kwalawa Yesmin kira dai-dai lokacin da Yesmin take gurshekan kuka jiyo kiran da ake mata yasa ta tsaida kukan da take tare da share hawayen dake kwaranyowa daga idanuwa ta zuwa kuncinta tunda ta shiga ta dauki mintuna tana kuka tun lokacin data shiga dakin ta fada gado ta fara tuna abubuwan da suka faru tsakanin Ya Imran da kuma Jamila taji ta tsane jamila bata son lokacin data fara zubda hawaye masu zafi daga cikin idanuwanta ba har ta ara gurshekan kuka. Sai da ta goge fuskarta tas dan kar a gane tayi kuka tukkunna ta futa ba tare data kalle su ba ta durkusa kasa “gani” binta da kalli Hajjiya Hafsatu tayi sannan tayi dariya tace “masha’Allah yarinya ta girma wallahi ta girma ta isa aure” gaban Yesmin ne ya yanke ya fadi cikin zuciyarta tace “lafiya to?” hajjiya na kallonta tace “ya naga kamar idonki yayi ja?” da sauri Yesmin tace “na fara bacci ne” Hajjiya tace “ok shiyasa, tashi ki je kiyi kwanciyarki” Yesmin ta mike ta koma Hajjiya saratu tace “yanzu kin yarda da ni?” Hafsatu tace “hmm na fada miki yarinya ta girma ta isah aure” dariya Hajjiya saratu tayi, Hajjiya hafsatu ce ta kuma magana “nace me zai hana a kara dankon zumunci?” cikin rashin fahimta Hajjiya Saratu ta ce “dankon zumunci a ina?” dariya Hajjiya Hafsatu ta tuntsire da shi “ina nufin Salim da Yesmin me zai hana mu kulla aure tsakaninsu kinga zumuncin mu sai ya dada kulluwa fiye da yanzu” shuru Hajjiya saratu ta danyi bayan wasu ‘yan dakiku tace “kuma fa kin kawo shawara, amma kina ganin hakan ba zai iya kawo mana wata matsalarba?” dariya Hajjiya Hafsatu ta sake yi tare da fadin “matsala kuma? Insha Allahu babu wata matsala” murmushi Hajjiya Saratu tayi yayin da take cewa “Allah ya yarda kinga kuwa da nafi kowa farin ciki wanda ka sani ai yafi wanda baka sani ba, in ya dawo zamu tattauna da shi akan maganar” haka dai suka ci gaba da hira yayin da ita kuma Yesmin take can kwance cikin daki tana ci gaba da gurshekan kuka Kan lamuran Ya Imran.

Yesmin bata taba sanin Ya Imran yayanta ne na jini ba kuma babu wanda ya taba fada mata hakan, hasalima bata san Hajjiya Saratu ba ita ta haifeta ba duk ganin da takewa Hajjiya Usaina matsayin yar mahaifiyarta take ba wai wadda ta haifeta da cikinta ba, haka ma Zarah da Imran tunaninta duk ‘ya’yan yar babarta ne bata taba sanin ‘yan uwanta ne na jini ba. Tun tasowar Yesmin babu namijin daya taba kwanta mata a iya shekarunta face Ya Imran shi kadaine wanda zuciyarta take muradi take kuma farin cikin gani, tun bayan daya tafi bautar kasar take kewarsa farin cikinta be wuce na ya dawo ta ganshi ba, a bacci ko a farke shi kadai take iya gani, tunaninta ma shi ne, ko a makaranta in suna hira da kawayenta labarin Imran kawai take basu ta ruga data gama kamuwa da soyayyarsa, ta kuma gama tsara rayuwarta da shi, haka zuwan da take gidan su tana zuwane dan kawai taga Ya Imran shiyasa ma bayan daya tafi suka daina ganinta akai-akai sai a yanzu daya dawo, sai dai kuma dawowar tasa be zame mata farin ciki ba face bacin rai, musamman yadda taga ya kamu da son wata daban ba ita ba wannan shi ne babban dalilin daya bata mata rai har ya sata kuka wanda kuma shi yasa ta kasa daurewa har tayi tawowarta gida sai dai duk da cewa ta dawo gida hakan be sa zuciyarta ta sassauta daga irin radadin daya addabeta ba, ta kasa tsaida zuciyarta waje daya wajen saka mata wasu abubuwan da bata tunanin faruwarsu, haka ta ci gaba da tunani gami da sake-sake hadi da tunane-tunane da gurshekan kuka wanda ta kasa tsayarwa, ta kai har dare tana cikin wannan hali ba tare da kowa ya sani ba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: