Connect with us

Uncategorized

Dan Shekara 12 Ya Rataye Kansa A Imo

Published

on

An samu firgici da tashin hankali a jiya a yankin Agboala Ishiala cikin garin Umudi a qaramar hukumar Nkwerre ta Jihar Imo, lokacin da wani yaro dan shekara 12 ya rataye kansa. Yaron mai sunsa Kasarachi Odurukwe, dalibi dan aji shida a makarantar firamare a yankin Umudi, ya kashe kansa ne sakamakon mutuwar iyayensa. Ana zargin yaron ya rataye kansa ne a wata bishiya. An bayyana cewa, yaron she ne babba a cikin yara a gidansu, suna saune ne wajen ‘yar’uwar mahaifiyarsu a yankin Agboala Ishiala tan lokacin da iyayensu suka mutu. Shi dai yaron ya dade yana fada wa abokansa cewa, yana so ya mutu domin ya sami mahaifiyarsa a gidan aljanna, haka kuma yana yawan cewa, ya gaji da zama a wannan gidan duniya.

Kwana daya kafin faruwar lamarin, Kasarachi ya buqaci qannansa guda biyu tare da wasu yara guda biyu su bi shi zuwa rafi dibo ruwa. Lokacin da suka isa rafin, Kasarachi ya taimaka wa sauran yaran cika bokitin ruwansu, sannan ya saka sanda mai tsawo yana duba zirfin rafin. Sai dai bai gamsu da zurfin rafin ba, shi ya sa ya yi amfani da igiya wajen rataye kansa a bishiyan goro. Lokacin da ya yi yunqurin kashe kansa na farko da na biyu, sai abokansa suka roqe shi a kan ya daina hakan, sai ya bayyana musu cewa, yana so ya rataye kansa a saman bishiyar goro saboda ya mutu. Lokacin da Kasarachi ya samu nasarar rataye kansa, sai sauran abokansa suka gudu zuwa gida domin su kai wa iyalansa da shugabannin qauyen rahoton faruwar lamarin, inda daga baya aka kira ‘yan sanda.‘Yan sanda ne suka taimaka aka sako da gawarsa qasa, inda aka ijiye ta a dakin ijiye gawarwaki da ke cikin asibiti. An samu batura a jikin mamacin wanda idan an hana shi rataye kansa zai sha su a matsayin guba.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, inda ya yi alqawarin zai sake wayyayarsa idan ya samu cikakken bayani daga jami’an ‘yan sandar qauyen Nkwerre, amma har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton bai tuntube shi ba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: