Connect with us

WASANNI

Dembele Zai Yi Jinyar Watanni Shida

Published

on

A ranar Talata likitoci suka yi wa dan wasa Ousmane Dembele aiki kan raunin da ya ji a kafarsa, sun kuma ce zai yi jinyar watanni shida kafin ya samu lafiyar da zai koma fili domin ci gaba da buga wasa.

Likitan da ya ja ragamar aiki, Dakta Lasse Lempainen ya ce raunin ya yi muni, kuma shi ne ya yi masa aiki a wanda ya yi wata hudu kan ya koma buga wasa a shekara ta 2017, wato farkon zuwansa kungiyar ta Barcelona.

Kuma wannan ne karo na uku da Dembele ke jin rauni da yake jinya mai tsawo tun komawarsa Barcelona a shekarar 2017 wanda hakan yasa shugabannin kungiyar suka fara tunanin rabuwa da dan wasan.

Barcelona ta dauki dan kwallon daga Borussia Dortmund, Ousmane akan kudin da ake cewa ya kai sama da fam miliyan 135 hakan ya sa dan kwallon ya zama na biyu mafi tsada a duniya a tarihin kwallon kafa da aka saya a lokacin, bayan Neymar da ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 daga Barcelona.

Dembele ya yi wa Barcelona wasanni tara a kakar bana, inda ya ci mata kwallo daya a fafatawa da ta ci Sebille 4-0 ranar 16 ga watan Oktoba sai dai tun daga wannan lokacin bai sake bugawa kungiyar wasa ba.

Tuni dai kungiyar ta shirya rabuwa da dan wasan idan an kammala kakar wasa saboda kamar yadda kungiyar take ganin yana jawo mata asara saboda baya buga wasa bayan saboda hakan ta sayo shi sannan kuma dan wasan ba zai buga wasan cin kofin nahiyar turai ba wanda kasarsa ta Faransa zata fafata a karshen wannan kakar
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: