Connect with us

WASANNI

Enyimba Ta Lallasa Wikki Tourist Ta Bauchi

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International ta yi nasarar doke kungiyar Wikki Tourist ta garin Bauchi da ci 3-0 a kwantan wasan gasar Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Laraba a jihar Abia.

Enyimba ta fara cin kwallo ta hannun Stanley Dimgba daf da za a je hutun rabin lokaci a gumurzun da suka yi a Aba wasan daya bawa kungiyar ta Enyimba wahala da farko kamar ba zata iya zura kwall a raga ba.

Bayan da kungiyoyin suka koma zango na biyu ne Enyimba ta kara kwallo ta biyu ta hannun Austin Oladapo sannan Bictor Mbaoma ya ci ta uku wanda hakan ya bawa kungiyar ta Enyimba nasara daci uku babu ko daya..

Usman Abdallah tsohon kocin Enyimba shi ne ya ja ragamar Wikki zuwa Aba, inda ta yi rashin nasara inda a cikin watan Janairun daya gabata Enyimba da Abdallah suka raba gari, inda ta maye gurbinsa da Fatai Osho.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta  Rangers International dake jihar Enugu cin Jigawa Golden Stars ta yi daci 1-0, kuma Dauda Madaki ne ya ci kwallon saura minti 20 a tashi daga karawar da akayi a jihar Enugu.

Sai kuma daya kwantan wasan da aka buga tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Akwa United da Dakkada 2-2 suka tashi a wasan nasu wanda kowacce kungiya taso ta samu nasara musamman a karshen lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: