Connect with us

JAKAR MAGORI

Fannin Noma Ya Samar Da Ayyukan Yi – FAK

Published

on

Mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel ya sanar da cewa,

Sai dai, Mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel ya yi nuni da cewa, irin wadannan kasashen, musamman dake a nahiyar Afirka, sun samu nasarar hakan ne ta hanyar yin amfani da jami’oin su dake a yankin na Afrika wajen gudanar da buncike a kan yadda zasu bunkasa fannin nasu da kuma samar da ayyukan yi ga alumomin su.

Ya ce, “Kasashen suna da sama da kashi 60 na alumomin su da suke a nahiyar Afirka wadanda kuma suka rungumi fannin aikin noma, hakan ya taimaka masu matuka wajen kara samar da dimbin ayyukan yi, musamman ga matasa.”

Ya yi nuni da cewa, idan jami’oin kasar nan basu bai wa bincike mahimmanci ba da kuma samar da dabaru za’aci gaba da barin fannin aikin noma a baya a Nijeriya duk da cewar Nijeriya Allah ya wadace tad a kasar yin noma mai kyau, inda har za’a iya fitar da amfanin gonar da ke a ke nomawa a kasar zuwa kasuwanni duniya.

Mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel ya sanar da cewa, nasarar nahiyar Afirka na muradun karni na ya danganta ne kan irin yadda a ka mayar da hankali wajen magance kaulubalen da ake fuskanata.

A cewar Mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel, kasashen dake a nahiyar Afrika har yanzu an barsu a baya wajen yin amfani da fasaha don bunkasa fannin noma a kasashen nasu.

Dakta Abebe Haile-Gabriel ya ci gaba da cewa, dumamar yanayi yana daya daga cikin kalubalen da manoma suke fuskanta a lokacin da suka yi girbin amfanin gonanak su, inda ya yi nuni da cewa, wannna matsala ce da jami’oin zasu iya shawo kanta amma idan jami’oin sun mayar da hankali wajen gudanar da yin bincike da kuma mayar da hanakli wajen yin amfani da fasaha a fannin noma.

Ya sanar da cewa, shigo da dabarun noma na zamani zuwa kasar nan, zai taimaka wajen bunkasa samar da abici da kuma kawar da yunwa, musamman a karkara.

Ya jadda da cewa, ya zama wajibi jami’oin mu su mayar da hankali wajen gudanar da bincike don a kara bunkasa fannin noma a Nijjeriya.

Ya ce, hukumar ta FAO na kan shirin fara horasa da daliban da aka yayae daga jami’oin koyon aikin noma, inda zasu shafe watanni shida a horasawar yadda zasu bazama gudanar da yin bincike a fannin. Ya yi nuni da cewa, jami’o zasu taimaka matuka wajen gudanar da bincike a fannin na noma.

A cewar hukumar ta na akan gaba wajen samar da tsare-trsaren bunkasa fannin noma ta hanyar aikin noma ta fasahar zamani a nahiyar Afirka.

A karshe, mataimakin Darakta kuma wakilin yanki a nahiyar Afrika a sashen abinci da amfanin goma na hukumar FAK Dakta Abebe Haile-Gabriel ya ce, “Muna akan gaba wajen samar da tsare-trsaren bunkasa fannin noma ta hanyar aikin noma ta fasahar zamani a nahiyar Afirka.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: