Connect with us

LABARAI

FRCN Ta Karrama Shugabar Hukumar NPA

Published

on

A ranar Alhamis ne hukumar gidan radion Nijeriya FRCN ta mika wa
Shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa ‘Nigerian Ports Authority
(NPA)’, Hajiya Hadiza Bala Usman lambar girmamawa saboda jajircewarta
wajen aiki tukuru da kishin kasa, musammam yadda matakan da take dauka
suka taimaka wajen yi wa Nijeriya tsimin miliyoyin daloli a ‘yan
shekarun nan tun daga lokacin data kama ragamar shugabanci a hukumar.
Sakataren gewamnatin jihar Osun, Prince Wole Oyebamiji ne ya mika mata
lambar girmamawar a taron wannan shekarar 2020 na ranar radio na
duniya da hykumar gidan radion tarayya ta shirya a Legas.
Baban Manaja mai kula watsa labarai da tsare tsare na NPA, Mista Adams
Jatto ya karbi lambar a madadin Hajiya Hadiza Bala Usman a wajen
taron, ta kuma mika godiyarta ga hukumar FRCN, ta kuma yi alkawarin
cigaba da iyakar kokoarinta na ganin an samu cigaban da ya kamata a
NPA, ta kuma nemi goyon bayan dukkan masu ruwa da tsari don a samu
nasara da ya kamata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: