Connect with us

LABARAI

Gwamnan Kogi Ya Mika Sunayen Mahukuntan Hukumar Zaben Jihar Ga Majalisa

Published

on

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a jiya alhamis ya aika da sunayen mutane takwas wadanda yake son nadawa mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta Jiha (SIECOM) ga majalisar dokokin jihar domin tantance su da kuma tabbatar da su. Wata sanarwa da jami’in hulda da ‘yan jaridu na gwamnan, Mallam Onogwu Muhammed ya sanya wa hannu a Lokoja, ta ce tsohon kantomar riko na karamar hukumar Lokoja, Alhaji Lawal Shiru ne zai shugabanci hukumar a yayin da Mista Ozobehe Enesi zai kasance sakataren hukumar. Sauran mambobin hukumar sun hada da Adaji Ainoko, Musa Adama( Babakeke), Funsho Olorunfemi, Chogudo Yakubu Musa, Labaran Oyigebe da kuma Abdulkarim Jamiu. Aika sunayen da gwamnan ya yi dai-dai yake da sashi na 197, karamin sashi na 1, sakin Layi (b) cikin baka na kundi tsarin mulkin 1999, wanda aka yi yi wa kwaskwarima. Hukumar ta SIECOM na da alhakin gudanar da sahihan zabuka a kananan hukumomi a Jihar Kogi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: