Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Yari Ta Azabtar Da Al’ummar Zamfara – Gwamna Matawalle

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Hon. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya tabbatar da cewa gwamnatin tsohon Gwamna Abdulaziz Yari Abubukar  ta azabbatar da al’ummar jihar bisa jefa su cikin kuncin rayuwa da talauci .

Gwamnna Matawallen Maradun ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsar mutane dubu hamsin ‘yan  Jami’yyar APC daga Kanan hukumomin Gummi, Bakura da Maru da suka dawo Jamiyyar PDP a gidan Gwamnati da ke Gusau .

Hon. Matawallen Maradun ya bayyana cewa , “tsohon Gwamna Abdulaziz  Yari ya butulce dan yayi gwamna na tsawon shekaru takwas ,duk da yake mu ‘yan adawa muka barshi ya yi mulkinsa lafiya babu adawa, sai gashi yanzu ya zo yana adawa da gwamnatin da Allah ya kawo .

“Kuma duk ‘yan takarar Gwamna a lokacin irin su Sanata Kabiru Marafa, da tsahon Gwamna Sanata Ahmad Sani Yariman Bakora da Dakta Dauda Lawal Dare da su malam Ibrahim Wakala mataimakinsa, sun hakura sun mika wuya amma shi ya ki yarda da hukuncin Allah. Dan haka mun san halinka ya jawo maka na girman kai da dagawa da jin kafi wani ya sanya ka halin da kake ciki, muna tausaya maka Abudulaziz Yari”.

Gwamna Matawallen Maradun kara da cewa, “wuya ta sanya tsohon Gwamna Yari ya sallama wa Adam Oshimhole da ya yi ayanzu dan ya ga uwar bari, bayan ya nuna cewa su ba komai ba ne. wannan ya isheka ishara a cewar  gwaman.

Da ya koma kan dubun dubatar ‘yan jam’iyyar APC da suka dawo PDP Gwamna Matawallen Maradun ya tabbatar masu da cewa ,lallai jamiyyar PDP zata tafi dasu kada da kafada dan samun cigaban alummar jihar ta Zamfara .kuma ya jinjina masu da suka yarda da hukunci Allah kuma suka bi gwamnatin zabin Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: