Connect with us

LABARAI

Gwanatin Kano Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan Hudu Kan Ayyuka Na Musamman

Published

on

A ranar Juma’ar da ta gabata, zaman Majalisar Zartarwar Jihar Kano, ya amince da fitar da tsabar kudi har Naira biliyan 4,332,4407,468, domin aiwatar da manyan ayyuka a Jihar Kano. Jawabin hakan, na kunshe ne cikin jawabin da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya bayyana ga mane ma Labarai jim kadan bayan fitowa daga zaman mako-mako da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano. Muhammad Garba ya kara da cewa, an amince da fitar da Naira Biliyan 2.750,400, wanda aka ware domin inganta harkokin samar da ruwan sha a Jihar Kano, yayin da aka ware Naira  Miliyan 150,000,000, domin zama wani bangare na samar da tsaftar muhalli da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma a fadin Jihar Kano tare da hadin guiwar Hukumar EU da Kuma UNICEF. Haka zalika, “an ware Naira Miliyan 26,950,000, domin gudanar da kididdigar gidaje a Jihar Kano tare da ware Naira Miliyan 89,303,734, domin daga darajar Asibitin Kafin Mai Yaki da ke Karamar Hukumar Kiru.” Kwamishinan ya cigaba da cewa, kamar yadda ake murnar zagayowar ranar mata ta duniya ta shekara 2020, Majalisar Zartarwar ta amince da kashe Naira Miliyan 24,750,000, domin gudanar da tsare-tsaren bikin tare da tallafawa mata 1,500. Haka zalika, Majalisar akan sauran bukatun da aka gabatar a gabanta, tare da amincewa da fitar da kason da ake bukata, domin aiwatar da waccan bukata cikin gaggawa. Cikin abubuwan da aka amince da su, har da kashe Naira Miliyan 441,816,140.05, domin ciyar da Makarantun Kwana guda uku, wadanda suka hada da Makarantar Bilingual, Niamey da ke Kasar Niger, gyaran motocin daukar dalibai mata 57, gina Makarantun Islamiyyu masu zaman kansu da ke Unguwar Gyadi-Gyadi/Ja’oji, samar da tsarin bayar da tallafin karatu, don biyan jarrabawar NECO/NBAIS/SSCE. Sauran kudaden da aka amince da kashe su, akwai Naira Miliyan 413,413,321.86, domin ingnata harkokin sadarwa (Intenet), samar da Kwamfutoci da kayan gyaranta, horar da Malaman Ilimin Manya a Ma’aikatar Ilimi, gina sabbin ajujuwa guda uku, gyaran karin wasu ajujuwan da bandakuna a wasu zababbun Makarantun jeka ka dawo da Makarantun Kwana tare da gyara wasu daga cikin gidajen Malamai. Haka nan, zaman Majalisar Zartarwar ya kuma amince da sabunta wasu gine-gine a gidajen lura da Marayu da ke Mariri, sai kuma daga daraja tare da inganta Sakandiren Kimiyya da Fasaha da ke Sakarma, a Karamar Hukumar Kiru tare da samar da karin tallafi ga kungiyar gudanar da Masabakar Alkur’ani ta kasa na shekarar 2019/2020, wanda aka gudanar a Jihar Legas.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: