Connect with us

LABARAI

INEC Ta Shelanta Daukar Sabbin Ma’aikata

Published

on

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa INEC a ranar Litinin ne ta bude babi domin fara daukar sabbin ma’aikata da suka hada da jami’an rijista na yankuna, jami’an gudanarwa, manyan jami’ai a dukkanin kananan hukumomi da suke fadin kasar nan.

Hukumar ta bukaci dukkanin masu sha’awar aiki da ita da su latsa shafinta na www.inecnigeria.org  ko kuma kai tsaye su ratsa cikin shafinta na daukar aiki ta www.inecrecruitment.com domin cike bukatar daukar aikin ga wadanda suka dace.

Kamar yadda sanarwar da ta wallafa a jaridu ke nuni, tana neman wadanda basu zarce shekaru 35 ba, masu bukatar aiki su kasance suna da shaidar karatu na kasa ko ND dukkaninsu suna da zarafin neman aiki da hukumar INEC.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: