Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Jam’iyyar APC Ta Najeriya Ta Nuna Goyon Baya Ga Sin Wajen Yaki Da Cutar Numfashi

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin tarayyar Najeriya Adams Aliyu Oshiomhole ya aikawa hukumar tuntubar kasashen waje ta kwamitin tsakiya ta JKS ta kasar Sin wani sako, inda ya bayyana goyon bayan kasarsa ga yaki da cutar numfashi da kasar ke yi.

Adams Aliyu Oshiomhole ya nuna cewa, kamar yadda shugaban kasarsa Buhari ya bayyana cewa, matakan da Sin ta ke dauka na tinkarar cutar abin koyi ne ga sauran kasashen duniya. APC ta yi imanin cewa, gwamnatin Sin na da cikakken karfin shawo kan da kuma magance cutar. Yana kuma fatan gwamnatin kasar Sin da jama’arta za su cimma nasarar wannan yaki da ma hanzarta dawo da zaman rayuwar yau da kullum yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Amina Xu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: