Connect with us

JIYA DA YAU

Karin Abubuwan Da Ke Haifar Da Rashin Tsaro A Kasar Hausa Da Sauran Yankuna

Published

on

A baya mun ga yadda jahilci da talauci suke zama babbar barazana ga kasashen da suka yi katutu a rayuwar al’ummar kasashen. Don haka idan aka kalli kididdiga ta tsakanin talakawa da masu kudi a kasar nan za a ga cewa kaso kusan saba’in cikin dari ko sama da haka talakawa ne a kasar da take da yalwar arziki na Dan Adam da ma’adanan kasa da na ruwa.

Hakazalika, mun ga yadda illar jahilci yake, da illar talauci ga rayuwar al’umma. Yanzu za mu kalli yadda tsarin tsaro yake, da daukar jami’an tsaron da kuma yadda barin iyakokin kasa ta ci barkatai suke za ma barazana ga tsaron kasa.

Tsarin tsaro da daukar jami’an tsaro yake a kasar nan.

Kamar yadda muka sani harkar tafiyar da tsaro a kasa ko yankin kasa, alhaki ne na al’umma bakidaya, wato dai kama-kama ake a gudu tare a tsira tare. Tsarin tafiyar da tsaro ya hada da samawa su Kansu jami’an tsaron kayan aiki na zamani wanda zai taimaka musu Wajen samun saukin tafiyar da ayyukansu domin Samar da tsaro a kasa baki daya. Ko da ba a samu damar sama musu kayan aikin irin nazamani irin nasun ma a sama musu isasshe. Hakazalika, yana daga cikin tsarin tsaron kasa ko yanki na kasa, shi ne a kula da hakkokin jami’an tsaron da suka shafi albashinsu a kyautata shi, da alawus-alawus shi ma a kyautata shi. A rinka ba su horarwa ta musamman da suka shafi kwarewar aikinsu da sanin shi kansa makamar aikin. Amma a yau a tsarin tsaron kasar nan su Kansu jami’an tsaron ba su isa ba, domin in aka hada auna yawan jami’an tsaron kasar nan da al’ummar wannan kasa za mu ga cewa akwai bukatar kara yawan jami’an tsaron domin tabbatar da tsaro a wannan kasa. Sannan in muka duba yanayi da su Kansu jami’an tsaron suke ciki, a wasu lokuta akwai hali na rashin tabbas da ya shafi rayuwar aikinsu, don haka yakamata a Samar wa jami’an tsaron kasar nan da yanayi mai kyau da halin tabbas a cikin rayuwarsu.

Hanyar Da Ake bi Wajen Daukar Jami’an Tsaro

Ita kanta wannan hanyar yakamata a yi duba a kanta, domin a da in an tashi daukan ma’aikatan tsaro ana kwatanta adalci wajen duba cancanta da dacewar Wanda yakamata a dauka. Misali, za a buga a jaridu ko yada a gidajen yada labarai cewa za a dau ma’aikatan tsaro nau’i kaza ga mai sha’awa, mutane za su nuna sha’awarsu ta hanyar aika takardunsa da makamanta abin da yakamata ya yi na Na nuna sha’awarsa, bayan an gama za a zo in jarabawa za a yi, za a yi, don haka daga karshe za a kafe sunayen wadanda suka yi nasara kuma su za a dauka. Amma daga baya siyasa ta zo ta lalata al’amuran daukar jami’an tsaro a kasar nan, ta damalmala al’amuran, inda ake bin tsarin nan na kura da shan bugu gardi da kwashe kudi. Domin wadanda za a yi wa jarabawar daukar aikin daban Wanda za a dauka daban. A mafi yawancin lokuta za ka ga cewa sai bayan an yi jarabawar an yi sikirinin sai ka ga an canja sunayen wadancan da suka sha wahala da sunayen masu ido da kwalli. A irin wannan tsarin ne za ka ga an yi kitso-da-kwarkwata, ma’ana an dauki baragurbi wadanda a karan Kansu suna bukatar aikin jami’an tsaron ya yi aiki a Kansu, amma a ce su ne za su bayar da tsaro?

Wannan ne ya sa za ka ji an ce an kama Jami’in tsaro a harkar ta’addanci ko kuma abin da bai dace a ce Jami’in tsaro ya aikata ba. A wasu lokutan shi kansa rarraba jami’an tsaro zuwa wajen ayyukansu na yau da kullum, shi ma yana bukatar gyara, domin an fi karkatar da zukatan jami’an tsaron a kan me za su samu a kan wacce gudunmawa za su ba wa tsaron kasa? Ma’ana dai za ka ga ma su uwa a gindin murhu su ake turawa in kogin yake gudanawa suna kwarfewa, in kuma ba haka in kana so a kai ka irin wannan Wajen sai ka yinkura ka yi wani abun za a tura ka. Don haka za ka cewa a maimakon su dukufa Wajen bayar da tsaro a kasa, sai su dukufa wajen bayar da kariya ga aljihunansu. Kowa ya San abin da yake faruwa a kasar nan, ba ga jami’an ‘Yan sanda ba, ba ga Sojoji ba ko Jami’an Hana-fasa kauri ko na Shigi-da-fici ba da sauran jami’an da ke da alhakin tabbatar da tsaro, cewa in za ka dauko mutuwa ba makami ba ko wani abin da aka haramta a wasu lokutan sai a kai su inda ake so a kai saboda karbar naira goma ko ashirin ko kuma hamsin ko Dari. Da wannan ne a lokuta da dama za ka ji an ce Jami’in Dan sanda ya harbe direban mota a kan ya hana shi cin-hanci, ko ma ka ji an ce Jami’in soja ne ya aikata irin wannan aika-aikar.

Domin gujewa irin wannan cakwakiyar yakamata a ce tantance su wa da wa yakamata su kasance suna tace wadanda yakamata su za ma jami’an tsaro a matakin farko? Na farko dai a matakin gari ko unguwa ko kuma yanki yakamata a ce akwai

  1. Shugabannin addini

  2. Dattawan gari

  3. Iyayen kasa.

Shugabannin addini suna taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar al’umma Wajen gyara tarbiyya da rayuwar al’umma, don haka yakamata a shigo da su Wajen bayar da shaida a kan duk Wanda yake da sha’awar za ma daya daga cikin Jami’in tsaro, domin su sun wane ne yake da tarbiyar da ya dace ya zama mai ba da tsaro ba mai ba da tsoro ba.

Dattawan gari su ma yana da kyau a sa su cikin kwamiti na sikirin a kowanne yanki ko gari domin su suka San asali da tarbiyyar duk wani Wanda ya taso a gari ko unguwa don haka za su Iya bayar da shaidar cewa wane ya cancanci ya zama Jami’in tsaro ko akasin haka.

Iyayen kasa, su ne uwa-Uba domin su ne masu alhakin kula da me ke zuwa, da me ke dawowa a cikin talakawansu, don haka duk wani Mutumin kirki sun San shi, haka ma Wanda ba na kirki ba shi ma suna an kare da shi. Da wannan ne za a Iya rage shigar bare gurbi aikin Samar da tsaro.

Barin Iyakokin Kasa Barkatai Ita ma Barazanace Ga Tsaron Kasa

Maganar iyakoki musamman na kan kasa, maganace da ba Iya kasashen Afirka ta tsaya ba a’a har manyan kasashe tana damu, kamar rigimar Amurka da Meziko Wanda har takai shugaban Amurka yana magana a kan zai gina Katanga a tsakaninsu. Haka akwai sa -toka, sa-katsi a kan maganar iyakoki na kasa ba na ruwa ba a tsakanin kasashe.

A duk lokacin da kasa ta yadda ta bar iyakokin kasarta a bude, yakan Iya zama barazana ta fuskar tsaron kasa, domin ta wannan iyakokin ne ake shigo da duk wani kayan laifi da suka kunshi makamai da kwayoyi haramtattu, da kayan fasa-kwauri da kan Iya zama zagon kasa ga tsarin tattalin arzikin kasa. Da wannan ne yakamata a ce an tsaurara matakan tsaro a kasa, shi ne gwamnati ta Samar da isassun jami’an tsaro, masu kishin kasa da isassun kayan aiki na zamani da wadata su da isasshen albashi don tabbatar da tsaro a iyakokin kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: