Connect with us

NOMA

Kungiyar Manoman Kashu Ta Bukaci CBN Ya Sanya Manomansa A ‘Anchor Borrowers’

Published

on

Kungiyar Manoman Cashew da sarrafa shi ta kasa (ACFAP), ta yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya sanya Manoman Cashew na kasar a cikin shirin sa na aikin noma na ‘Anchor Borrowers’.

A cewar kungiyar, noman cashew na taimakawa kan kara tattalin arziki, samar da ayyukan yi.

Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja, inda Unekwuojo Edime ya ci gaba da cewa, kungiyar ta na son yin hadaka da shirin aikin noma (NIRSAL), da kuma hukumar Inshorar aikin noma na (NAIC), musamman don gyara wuraren yin noman da ake dasu a kasar nan da kuma kara fadada kadada -kadada da ake dasu a Nijeriya.

Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime ya kara da cewa, a kungiyance, muna kara daukaka noman Cashew ne, tare da mayar da hankali kan, inganta nomansa, samar da ayyukan yi, da kuma kara habaka tattalin arziki.

Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime ya ci gaba da cewa, kungiyar don a magance dukkan kalubalen da ake fuskanta a fannin, kalubalen, zata yi hadaka da gwamnati a dukkan cikin shirye-shiryen ta data tsara na bayar da dauki a fannin aikin noma, tare da bukatar a sanya noman Cashew a cikin shirin aikin noma na Bankin CBN na ‘Anchor Borrowers’.

A cewar Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime, ta hanyar hadakar za kuma a samu damar yin amfani da ingantaccen Irin na Cashew da kuma lura dashi yadda ya dace, zai taimaka sosai, wajen kara bunkasa noman sa a Nijeriya da kuma rage tafka asara wajen noman sa a kasar.

Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime kungiyar ta kuma yi amfani da shirin hangami kan shuka yayan itatuwa da Ma’aikatar kula da Muhalli ta tarayya take kanyi a karkashin aikin shuka yayan itatuwa na (GGP) yadda kungiyar zata bayar da nata gudunmawar wajen cimma nasarar aikin a kasar nan.

A cewar Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime, kungiyar ta manoman Cashew ta kasa, zata kara mayar da hankali a wannan lokacin, musammanndon taga ta amfana da dukkan daukin da gwamnatin tarayya ta samar a kasar nan aikin noma, musamman don kungiyar ta bayar da nata gudunmawar wajen bunkasa fannin aikin noma da kuma samar da dimbun ayyukan yi ga yan Nijeriya ta fannin na noma tare da kuma kara inganta walwala da jin dadin yayan kungiyar.

Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime ya kara da cewa, za’a iya cimma hakan ne ta hanyar kara fadada shirin aikin noma na babban bankin Nijeriya CBN wato na shirin Anchor Borrowers da kuma damar da NIRSAL ta tanadar a fannin na aikin noma wajen zuba jari.

Shugaban kungiyar ta kasa Injiniya Unekwuojo Edime ya sanar da cewa, akwai dimbin kungiyoyin manoman Cashew da dama da suka jima a kasar nan, inda ya bayyana cewa, sai dai suna samun komawa saboda irin ayyukan yan nakama dake saye kusan daukacin Cashew da manoman a kasar nan suka girbe a cikin farashi mai sauki, inda su kuma suke sayarwa a asuwanni da tsada.

Idan za a iya tunawa, a kwanan baya an ruwaito Manoman Cashew da kuma masu fitar dashi daga kasar nan zuwa kasuwannin duniya, suna shirin tara kudaden shiga da suka kai dala miliyan 350 a shekarar 2020 ta hanyar fitar dashi zuwa waje.

Sai dai, manoman sun yi nuni da cewa, in har sun samu yin girbi mai dimbin yawa na Cashew din da suka shuka a cikin wannan shekara, musamman idan akayi la’akari da yanayi yake da kyau a bana muna sa ran tara dala miliyan 350.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: