Connect with us

BABBAN BANGO

Kwalliya Za Ta Biya Kudin Sabulu Wajen Dakile Yaduwar Cutar Coronavirus A Kasar Sin

Published

on

Kowa ya sani, kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen hana yaduwar cutar numfashin da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa a halin yanzu.

Cutar coronavirus, cuta ce mai yaduwa tsakanin jamaa, musamman idan ka taba ruwan da ya fito daga baki ko hancin mutanen da suka kamu da cutar, kai ma za ka kamu da ita. Mutanen da suka kamu da irin wannan cuta, su kan ji zazzabi da yin tari har ma su kan gamu da wahalar numfashi sosai. Har yanzu masana kimiyya da fasaha na kokarin gudanar da bincike game da ainihin musabbabin kamuwa da cutar, kuma ana ta gudanar da gwaje-gwaje cikin gaggawa domin samar da magani da allurar rigakafin irin wannan cuta.

Cutar coronavirus ta bulla tun farkon farawa a wani birni mai suna Wuhan, babban birni ne na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, inda a yanzu cutar ta fi Kamari. A jiya Alhamis ne hukumar lafiya a lardin, ta ba da rahoton sabbin mutane 14,840 da aka tabbatar sun kamu da cutar, kana wasu mutane 242 suka mutu a shekaranjiya wato ranar Laraba. Wannan shi ne adadi mafi yawa da aka samu a rana tun bullar wannan annoba.

Hukumar ta ce, adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar, ya hada da mutane 13,332 da aka tantance a asibiti aka kuma tabbatar sun kamu da cutar. Gaba daya adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin Hubei ya kai 48,206. Ya zuwa ranar Laraba, mutane 1,310 ne cutar ta halaka a lardin.

Alkaluma na nuna cewa, galibin wadanda bincike suka tabbatar sun kamu da cutar, sun fito ne daga lardin Hubei, ciki har da wadanda cutar ta halaka. A cewar hukumar, duk wadanda ake zaton sun kamu da cutar numfashi bayan gudanar da bincike na kimiyya, ana daukarsu a matsayin wadanda suka kamu da cutar. Hukumar lafiyar lardin ta kuma bayyana cewa, an sake gudanar da binciken ne, don baiwa wadanda aka gano suna dauke da cutar damar samun magani a kan lokaci, ta yadda za a inganta matakan ba da jinya ga wadanda ake kula da su.

Wasu mutane na shakkun cewa, ko bullar wannan cuta za ta kawo mummunar illa ga tattalin arziki gami da zaman rayuwar al’ummar kasar Sin? Game da wannan batu, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasarsa za ta karfafa matakan daidaita tattalin arziki da dawo da aikin kamfanonin samar da kayayyaki da rabawa da samar da muhimman kayayyaki, don daidaita ci gaban jin dadin jama’a da tattalin arziki, a daidai lokacin da kasar take ci gaba daukar matakan yaki da annobar numfashi da ta bulla a kasar.

An bayyana wadannan matakai ne, yayin taron majalisar gudanarwar kasar na ranar Talata da firaminista Li ya jagoranta. Taron ya kuma bayyana bukatar karfafawa kamfanonin gwiwar dawo wa bakin aiki bisa tsarin da ya dace. A halin yanzu abu mafi muhimmanci da ya dace ga lardin Hubei shi ne, ya mayar da hankali wajen dakile wannan annoba, yayin da ake kokarin tabbatar da ganin kamfanoni sun dawo da aikin samar da muhimman kayayyakin hana yaduwar cutar da na hidimomi da ake bukata a manyan birane.

Haka kuma an bukaci sauran lardunan kasar, da su dauki managartan matakai na kandagarki da hana yaduwar cutar bisa yanayin da suke ciki. Kana a galibin birane da sauran lardunan dake da karancin wadanda suka kamu da cutar, ya kamata gwamnatocin kananan hukumomi, da su tsara matakan dawo da ayyukan kamfanonin samar da kayayyaki yadda ya kamata.

Taron ya kuma bukaci masu samar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya, da su hanzarta dawowa bakin aiki gadan-gadan, don biyan bukatun matakan yaki da wannan annoba. Sannan wajibi ne bangarorin sufuri, da muhimman tashoshin tsare-tsare da gudanar da ayyukansu ba tare da barin jama’a suna taruwa ba. Sannan za a iya dawo da hidimomin jiragen kasa da motocin sufuri na jama’a bisa tsari a wuraren da annobar ba ta yi tsanani ba.

Bugu da kari, taron ya bukaci, rassan gwamnatoci na kasa, da su bullo da matakai na musamman, don taimakawa kamfanoni jure illar bullar wannan annoba, ta yadda za su magance matsalolin da harkokin kasuwancinsu za su fuskanta, musamman kananan kamfanoni da masu zaman kansu. Haka kuma ya kamata a aiwatar da matakai na wucin gadi, don taimakawa harkokin kasuwanci, ciki har da rage ko dauke kudin haya ga kamfanonin gwamnati masu zaman kansu, da rage kudaden haya da inganta manufofin rage kudaden haraji.

A halin yanzu gwamnatin kasar Sin na kara daukar wasu kwararan matakai domin shawo kan wannan annoba a birnin Wuhan da duk fadin lardin na Hubei. Rahotanni daga hukumar dake jagorantar matakan kandagarkin cutar numfashi ta birnin Wuhan sun bayyana a Laraba cewa, a halin yanzu, an bude asibitocin wucin gadi guda 7 da cibiyoyin bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar numfashi sama da guda 40, a birnin na Wuhan, lamarin da ya kyautata tsarin ganowa da bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar.

Haka kuma, akwai maaikatan lafiya da nas-nas 4,966 dake aiki a wadannan asibitocin wucin gadi guda 7, inda suka fara karbar wadanda suka kamu da cutar numfashi tun daga ranar 6 ga wata, kana ya zuwa karfe 7 na ranar 12 ga wata, gaba daya, an kwantar da wadanda suka kamu da cutar 4,313 a asibitocin da aka tanada.

Bugu da kari, a halin yanzu, akwai cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar numfashi sama da guda 40 da aka samar, ciki har da asibitin Huoshenshan da na Leishenshan, gaba daya akwai gidajen kwantar da marasa lafiya guda dubu 12, kuma za a yi amfani da su wajen jinyar marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani.

Ban da haka kuma, birnin Wuhan ya karfafa aikin binciken dukkan mazauna birnin bisa manufar bincken ko wane gida, da ko wane mutum, da kuma a ko wace rana. Kana, ya zuwa karfe 5 na yammacin ranar 11 ga wata, gaba daya, an tantance magidanta fiye da miliyan 4, ciki har da mutane fiye da miliyan 10. Muna fatan kwalliya za ta biya kudin sabulu wajen kawar da wannan cuta baki daya daga birnin Wuhan da ma lardin Hubei baki daya.

A dayan bangaren kuma, abun matukar farin ciki shi ne, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a sauran sassan kasar Sin ya yi ta raguwa a ‘yan kwanakin nan, wato ban da shi lardin Hubei. Wannan ya danganta ne sosai da irin managartan matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka, ciki har da fadakar da jama’a kan ilimin da ya shafi kandagarkin cutar, da kiransu sanya abun rufe baki da hanci idan suka fita daga cikin gida, da kaucewa taron jama’a da sauransu.

A halin yanzu kuma, lokacin da ake kokarin fadakar da al’umma kan muhimmancin hana yaduwar cutar, ana kuma amfani da fasahohin zamani da dama a wannan fanni. Ga wani misali a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang, inda Zheng wei mai kula da kamfanin kadarori a birnin ya samu wani gajeren sakon dake cewa, akwai wani magidanci da aka ce yana dauke da kwayar cutar coronavirus a lardin Hubei, kuma ya yi amfani da katinsa na shiga rukinin gidaje. Kuma watakila ya dawo gida daga Hubei, don haka ana bukatar ya je ya duba shi ko yana cikin koshin lafiya ko yana bukatar taimako.

Wani tsari na gargadi dake iya musayar muhimman bayanai tsakanin tsarin tsaro na sirri na rukunin gidajen jamaa na Hangzhou mai suna City Brain wata manhaja da kamfanin Alibaba ya hada da nufin inganta tsarin sanya ido a birnin ne yake aika wannan sako kai tsaye.

Muhimman bayanai daga kimanin hukumomin gwamnati da na kasuwanci 80 ne ke shiga rumbun manhajar na City Brain a kowace rana. Birnin na Hangzhou ya kaddamar da tsarin kandagarki da kariya ta hanyar amfani da wannan manhaja, a daidai gabar da ake fama da cutar numfashi. Ta hanyar hada kai da manyan kamfanonin wayoyin salula guda uku, sabon tsarin, zai iya aika sanarwa ba kawai ga yan asalin Hubei dake Hangzhou ba, har ma da daukacin Sinawa ko matafiya da suka ziyarci Wuhan a baya-bayan nan, don tunatar da su daukar matakai da zarar sun isa Hangzhou.

Muna da yakinin cewa, ta hanyar daukar irin wadannan matakai na kandagarkin yaduwar cutar numfashi ta coronavirus, da cikakken goyon-baya gami da tallafin da kasashen duniya suka ba mu, ciki har da kasashen Afirka daban-daban, gwamnatin kasar Sin da jama’arta za su samu galaba kan yakin da suke na kawar da cutar baki daya daga duk fadin kasar. Allah ya taimaka!

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: