Connect with us

FITATTUN MATA

Laila Dogonyaro: Jarumar Kare Hakkin Dan Adama

Published

on

Ko-kun-san?

Laila Dogonyaro ‘yar Nijeriya ce mai fafutukar kare hakkin bil-adama ta shugabanci Majalisar Kungiyoyin Mata a Nijeriya, wato National Council of Women’s Societies (NCWS) tana cikin matan da suka kirkiri Jam’iyyar Matan Arewa da nufin taimaka wa iyalai matalauta a arewacin Nijeriya; jajirtacciyar ‘yar kare hakkin bil-adama ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata rayuwar jama’a wanda har ta zama tauraruwa a arewacin kasar nan. hazikancinta har ma ya sanya ake mata lakabi da ‘mace mai kamar maza’.

 

Wace Ce Laila Dogonyaro (OON)?

An dai haife ta ne a birnin Kano a 1944, Mahaifiyarta asalin Hausa-Fulani ce, ta yi karatun firamaredinta a St. Loius Primary school, da ke Kano. Sai dai kuma an mata aure a lokacin da take yarinya ba tare da jinkirta ko ta zurfafa karatunta a lokacin ba domin an yi mata aure ne tana da shekaru 13 kacal a duniya. Hakan ya faru ne kuma a sakamakon a zamanin da ta zo, a arewacin Nijeriya ana mutunta aurar da yara mata kanana da wuri. Mijinta ya manyanta a lokacin da aka aurar da ita wato Alhaji Ahmed Gumau wanda yayi aiki da G.B Ollivant.

Laila ta kasance shugaban Majalisar Kungiyoyin Mata a Nijeriya wato (National Council of Women’s Socienties) daga shekarar 1993 zuwa 1995. A farkon saba’inoni 1970s ta kasance sakatariyar Jam’iyyar Matan Arewa.

Hajiya Laila ta shafe kusan dukkanin rayuwarta ne a jihar Kaduna, ta sake komawa garinta na haihuwa jihar Kano daga bisani ta zauna a Garki wanda har ma ta samu sarautar Garkuwan Garki bisa kokarinta wanda Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani ya nadata. Ta shafe kusan dukkanin rayuwarta wurin taimaka wa rayuwar mata karkara, kiyaye hakkokin da kare hakkin al’umma, karfafan jama’a musamman ta fuskacin koyar da sana’o’in dogaru da kai garesu.

Bisa himmarta, an bata lambar yabo ta Officer of the Order of the Niger (OON) a shekarar 2001.

A shekarar 1963, ta zama cikakkiyar mambar jam’iyyar Matan Arewa, kungiyar mata da ta yi hadaka da NPC da zimmar tabbatar da kula da walwalar iyalan talakawa da suke arewacin Nijeriya. Kungiyar ta gina makarantu, cibiyoyin zana jarabawar WAEC da baiwa mata damar amfana da su a yankin. Laila Dogonyaro ta fara shiga hidimar siyasa ne a shekarar 1977, a lokacin da ta nemi takarar mazabar Tundun Wada, tasirin da maza suka fi yi a hidimar siyasa a wancan lokacin ya hana mata kaiwa ga nasara. A shekarar 1979 ta zama mambar jam’iyyar National Party of Nigeria.

Daga shekarar 1985 zuwa 1993 ta kasance shugaban NCWS ta jiha. Ta zo ta zama shugaban kungiyar na kasa baki daya a shekarar 1993. A shekarar 1998 ta fara tafiyar da kungiyarta mai zaman kanta wato ‘Women’s Opinion Leaders Forum’ (WOLF).

Hajiya Laila Dogonyaro ta shahara wurin fafutukar kare hakkin mata, musamman ganin an ilimantar da su da karfafansu. Sai dai duk da wannan jarumta da kokarin nata, Hajiya Laila ta rigamu gidan gaskiya (rasuwa) tana da shekaru 67 a duniya tun shekarar 2011. Ta yi fama da cutar sikari, inda ya rasu a ranar 28 ga watan Afrilun 2011 a asibitin Malam Aminu Kano bayan gajeren rashin lafiya da ta yi fama da shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: