Connect with us

LABARAI

Mafita A Kan Kazantar Rashin Tsaro A Nijeriya – Majalisar Shari’a

Published

on

Majalisar koli ta harkokin shari’ar Musulunci a Nijeriya, reshen Jihar Kaduna, ta yi Allah wadai da ta’addancin da ke faruwa a jihar da ma kasar baki daya.

Majalisar ta yi wannan kira ne a yayin taron manema labarai da ta yi a Kaduna jiya Alhamis.

Sakataren Majalisar, Sheikh Abdulkareem Hashim Bindawa, ya ce dole majalisa ta yi Allah wadai da ta’adanci duba da yadda mutane musamman na wasu kananan hukumomin jihar ta Kaduna ke fuskantar matsalar tsaro.

Sheikh Abdulkareem ya kara da cewa, suna masu alhini tare da jajantawa al’ummomin kananan hukumomin Chikun, Igabi, Kajuru, da Birnin Gwari, kan ayyukan ‘yan ta’adda da ya addabi wuraren su.

A cewarsa, “dole ne al’ummar musulmi su koma ga Allah ta hanyar yawan tuba tare da rokon Allah a kan ya yaye mana wannan Masifar, sannan kuma mu dai na aikata ayyukan sabo.

“Domin yawan saba wa Allah na daya daga cikin dalilan da suka sa muka tsinci kan mu a cikin wannan hali na rashin zaman lafiya.”

“Ya kamata jama’a su hada kansu su bi hanyoyin neman yardar Allah wajen maganin masifu, kamar su karatun al’kur’ani, nafilfili, istighfari, kunuti, da makamantansu.” A cewarsa.

A bisa wadannan dalilan ne ya sanya majalisar ta yi kira ga jama’a da su hada kansu wajen ganin sun samar da ingantaccen bayanai bisa ayyukan masu ba da bayanai ga ‘yan ta’adda wadanda ko shakka babu su na zaune a cikinsu.

 

Sakataren ya kuma kara da cewa” aikin ‘yan ta’adda bai zai yiwu ba sai da hadin kai daga masu basu bayanai.”

 

Sannan majalisar ta yi kira ga Gwamnati da ta kara jajircewa wurin kare rayukan jama’a musamman ta hanyar dakile layukan sadarwa saboda ta wannan hanyar ne ‘yan ta’adda ke samun damar cimma burinsu.

 

Majalisar ta kara da cewa, “Muna kira ga hukuma da ta inganta makaman da ke hannun jami’an tsaro ta yadda za su iya fuskantar ‘yan ta’adda.

 

Majalisar ta kuma yi kira ga al’ummar da suke zaune cikin kauyukan da ‘yan ta’adda ke yawan far masu, da su yi kyakkyawan tsari na samar wa da kansu kariyar rayuwa da dukiyoyinsu domin neman sauki daga harin ‘yan ta’addan, in ji Majalisar kolin ta Harkokin Shari’ar Musulunci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: