Connect with us

Hannunka Mai Sanda

Mafita Game Da Dakile Kalaman Kiyayya Da Yada Karairayi A Soshiyal Midiya

Published

on

Kammalawa:

Tun afarkon wannan rubutu, an yi kokarin gabatar da wasu ababe kamar haka;

—Wani abu daga ma’anar Kalaman Kiyayya, a ciki, da wajen wannan Kasa.

—Yunkurin masu mulki da masu mara musu baya, wajen ganin an tabbatar da Dokokin da za su haramta yin Kalaman Kiyayya a Kasa, tare da hukunta duk wani mutumi, ko gungun wasu mutane, da aka samu na yin waccan ta’ada ta yada kalaman na kiyayya a Najeriya.

—An gabatar da kamanceceniyar dake tattare da Kudirin Dokar Kalaman Kiyayya, da kuma Kudirin Dokar dake yunkurin haramta yada bayanan karya a Kafofin Sadarwa na Zamani (Hate Speech Bill & Social Media Bill).

—An gabatar da banbance-banbancen ra’ayoyi da aka rika samu, tsakanin masu mara baya wajen ganin tabbatar wadancan Kudirorin Dokoki biyu (2) da aka ambata a sama, da kuma masu kalubalanta, ko yin Allah-wadai da tabbatarsu.

—A can bayan, an yi kokarin gabatar da irin kallo, da mabanbantan Kasashe a Duniya ke yi wa Kalaman Kiyayya musamman: wasu Kasashe, sun aminta da kafa Dokokin da za su haramta Kalaman, cikinsu akwai Kasar Australia; Belgium; Canada; Croatia; Denmark; Europe; Russia; England da makamantansu. A daya hannun kuwa, akwai hamshakiyar Kasa irin ta Amurka (America), wadda ta fassara duk wani yunkuri na samar da irin wadancan Dokoki, na dakile ko kassara kalaman kiyayya, da tauye ‘yancin da Dan’adam ke da shi, na bayyana ra’ayinsa da fatar baki.

—An gabatar da ra’ayoyin wasu masharhanta a wannan Kasa, dake kallon yunkurin samar da Dokokin a matsayin wani yunkuri, na yi wa ‘yan Jaridun Kasa takunkumi, tare da toshe-bakin masu adawa da manufofin gwamnati ta-karfi.

Bugu da kari, an gabatar da hujjojin da wadanda suka yi imani da muhimmancin kirkirar irin wadannan dokoki suka gabatar, musamman, Sanatan da ya gabatar da Kudirin a Zauren Majalisar Dattijai ta Kasa cewa, Kasashe daban-daban a Duniyar yau, na dabbaka irin wadancan Dokoki saboda tsantsar alfanun dake tattare da su. Haka cikin iyalan masu mulki, da masu yin aiki a karkashinsu, suma sun yi kokarin nusar da jama’ar Kasa game alheran da suke da tunanin za a iya girba karkashin samar da DOKOKIN.

A takaicen takaitawa, duk ma tsagin da mutum ya marawa baya, ba a rasa wani abu da za a ga ya rika, ko runguma, a matsayin hujja. Don takaita rubutun, a nan, za a yi kokarin gabatar da wasu ‘yan hasashe ne, wadanda mai yiwa, da za a dabbaka su, su taimaka wajen magance waccan danbarwa da aka jima a na tafkawa, game da wadancan Kudirori Biyu (2) da aka ambata a sama. Ga wadancan hasashe ko tsokaci kamar haka;

1- Yin La’akari/Nazari Da Dokokin Dake Da Alaka Da Wadancan Kudirori Biyu (2) Wadanda Ke Kunshe Cikin Kundin Tsarin Mulki Na Kasa.

2- Duk Wani Yunkuri Da Za A Yi Na Gabatar Da Makamancin Irin Wadancan Kudirori Na Su Zama Doka A Yi Taka-tsantsan Da ‘yancin Fadin Albarkacin Baki Na Jama’ar Kasa.

3- Kada A Shigar Da Ra’ayin Siyasa Cikin Manyan Batutuwa Irin Wadannan.

4- A Samar Da Ayyukan-yi Ga ‘yan Kasa Musamman Matasa.

5- A Samarwa Da Jama’ar Kasa Da Ababen More Rayuwa.

6- A Yi Duba Na Tsanake Ga Dokokin Kasa Tare Da Samar Ko Kawar Ko Yin Kwaskwarima Idan Da Bukatar Hakan Ga Jerin Dokokin Da Ke Da Jibi Da Wadancan Kudirori Biyu Da A Ke Gwaggwama Numfarfashi A Kansu, “Hate Speech Bill & Social Media Bill”.

Sama-sama, ga dan karin haske da za a gabatar, game da wadancan ababe shida (6) da aka lasafta a matsayin mafita kamar haka;

1- Nazartar Kundin Tsarin Mulki Na Kasa;

Yayin nazartar Kundin, duk wata dokar da ake ganin ta yi magana game da wadancan Kudirori biyu da ake ta husuma a kansu, ke nan, ta raba gardama, sai a yi watsi da wancan Kudiri a karkata zuwa ga samammiyar dokar.

2- A Kaucewa Tauye ‘yancin Fadin Albarkacin Baki;

Wajibi ne duk inda aka je a ka zo, a sakarwa ‘yan Kasa marar fadin albarkacin bakinsu, musamman ma karkashin irin wannan inuwa ta Dimukradiyya.

Da yawan mutane na zargin akasarin mahukuntan Najeriya da son kawo misalan yadda Kasashen waje ke aiwatar da wasu lamuransu, musamman idan wancan gabatar da misali, zai taimakawa gwamnatin, wajen cimma wani muradi nata na kashin-kai.

Masu goyon bayan gwamnati game da aiwatar da irin wadancan Dokoki na Kalaman Kiyayya, da na Kafofin Sadarwa, kan bugi-kirjin kafa misali da Kasar Sin, China. Alhali, a lokaci guda, Kasar Amurka ba ta goyon bayan makamancin Kudirorin, saboda haka, ba za a ji su sun yi maganarta ba.

Da babu damar fadin albarkacin baki ko kalubalantar manufofin gwamnati cikin kakkausan lafazi cikin wannan Kasa, da yawa daga cikin gwamnatocin da aka sami sukunin kafawa a matakan Kananan Hukumomi, da Jihohi, da ma matakin Tarayya, ba za su kafu ba. Na’am, fadin albarkacin baka, na da geji ko a ce iyaka, sai dai akwai iyakokin shimfide cikin Kundin Tsarin Mulki na Kasa.

Babu shakka, ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma ita kanta Dimukradiyyar da Duniyar ke kafulle da ita a yau, tamkar Hasan da Husaini ne, ba su rabuwa, duk kuwa ta inda aka bullo. Ga wanda ya karanta, ko ya taba riskar yanayin Mulkin Soja, zai fi saurin fahimtar wannan tsokaci game da muhimmancin samuwar ‘yancin fadin albarkacin baka.

3- Kaucewa Shigar Da Ra’ayin Siyasa Cikin Sha’anin Kudirorin Biyu (2);

Yayinda aka wayigari, masu mulki a matakan jihohi da tarayya za su riki irin wadannan Kudirori a matsayin takunkumin siyasa, musamman, ga Jam’iyyun Adawa na Siyasa, salon, na iya haifar da mummunan tazgaro ga Tsarin na Dimukradiyya kacokan. Kamar yadda Kudirorin suka bayyana a Zauren Majalisa, sai a bar ‘yan Majalisun, su tattauna a tsakaninsu, su fitar da matsayarsu, ta hanyar tuntubar ra’ayoyin al’umar Mazabunsu da suka zabe su, suka tura su can, don su wakilce su. Saurarar akasarin ra’ayoyin masu zabe game da lamari irin wannan mai rikitarwa, ya fi jin ta bakin Jam’iyya muhimmanci. Ko da yake a baya cikin wannan rubutu, an gabatar da inda ‘yan Zauren Majalisar Wakilai na Kasa ke sukar gabatar da Kudirorin, tare da kafa hujjar cewa, akasarin jama’arsu, ba sa marawa Kudirorin baya.

4- A Samarwa Da Matasa Ayyukan-yi A Kasa;

Da daman Matasa da a yau za a iske na wuni bisa Yanar Gizo suna zage-zage, da sunan Siyasa, ko Addini, ko Kabilanci da Bangarenci, ba abin mamaki ba ne a ce, rashin aikin-yi na taka rawa ainun wajen faruwar hakan.

Da mutum zai tashi da safe a ce ya san inda za shi bidar abinci, zuwa yamma ne ko dare, ba za a same shi ya mayar da zage-zage da cin-fuskar mutane da tamkar wata sana’a ba tsawon rana.

Da yawan ayyukan assha da makamantansu, an fi samunsu tattare da gungun mutane ko daidaikunsu, da ba su da ayyukan-yi. Ko da wajen masana a ka tuntuba, za a sami gamsassun hujjojin dake nuni da yiwuwar aikata laifuka, yayinda yanayin rashin aikin-yi ke dada yin kamari a Kasa.

Dolen dole ne, gwamnatoci cikin wannan Kasa, su tashi haikan, tare da samar da ayyukan-yi ga al’umar Kasa, kamar yadda suka yi alkawarin samarwar a lokutan da suke karkatar da kawuna, suna masu godon Talakawa cikin tattausar murya, cewa su ba su kuri’a, su maishe SHUGABANNINSU.

Ba ka bai wa mutum aiki ba, kuma kana so ka saita tunaninsa, ko kuma kana son tilasa shi salon, irin yadda zai rika aikewa da sakonni a Kafofin Sadarwa!!! Shin, hakan mai yiwuwa ne cikin sauki?.

5- Samar Da Ababen More Rayuwa Ga Jama’ar Kasa;

Kasashen Duniyar da ake son kafa misali da su cewa, irin wadancan Dokoki na gudana a cikinsu sumul-kalau, sai kuma a tambayi mai wannan magana cewa, yaya batun ababen more rayuwa da gwamnatocinsu ke kwararo musu dare da rana?. Irin namu ne yanayin da suke ciki?. A Hausance ma ai an ce, Laifin Yaro Kiwa, Laifin Babba Rowa. A fili yake cewa, shi YARON, an sa shi yin wani abu ne, sai ya ki yi, saboda BABBAN, ya ki ya ba shi abinda yake wajensa na kyautatawa da jinkai.

6- Yin Taza Da Tsifa Ga Kundin Tsarin Mulki Na Kasa;

Babu shakka, Kundin Tsarin Mulkin da Dan’adam ya tsuguna ya kirkira, a ko da yaushe ba a rasa shi da wasu kura-kurai, gyare-gyare tare da bukatar canjawa. Saboda haka, a sake kallonsa a tsefe shi. Shin, dokokin dake yin hani game da Kalaman Kiyayya; Kalaman Batanci; Kalaman Kabilanci da tunzura Jama’ar Kasa, idan akwai su, sun yi rauni ne? Ko kuwa, babu su, akwai bukatar samar da su? Koko a’a, suna bukatar a yi musu kwaskwarima ne? Ko kuwa ba a dabbaka su ne?. Amsoshin wadannan Tambayoyi kam, za su taimaka ainun, wajen shawo-kan da daman tsarmakatan dake tattare da illolin Kalaman Kiyayya da masu alaka da su a Tarayyar Najeriya.

A karshe, akwai hanyoyi iri-iri da muddin za a dabbaka su a inganta su, za su gusar da akasarin matsalolin da ake ta burari a kansu, dangane da Kalaman na Kiyayya. Uwa-uba, dabbaka dokokin a aikace. Sannan, a kawar da batun dan-bora da dan-mowa wajen tsayar da adalci a Kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: