Connect with us

LABARAI

Majalisar Dattawa Ta Nemi A Bi Kadin Kisan Mutum 30 A Maiduguri

Published

on

A jiya Alhamis ne Majalisar Dattawan kasa ta nemi a bincike musabbabin kisan mutum 30 da kone motoci da dama hadi da gidaje a kauyen Auno da ke kusa mashigar garin Maiduguri ta jihar Borno da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi.

Wakazalika, majalisar ta kuma yi shirun minti guda domin alheni da nuna karamci ga wadanda suka rasa rayukansu a harin da Boko Haram din ta kai.

Majalisar Dattaban, ta kuma yi kira ga hukumomin sojin kasar nan da su gaggauta kafa sansaninsu a kauyen Auno domin kare kowace irin harin da ka iya zuwa.

Sannan, ta kuma yi kira ga ma’aikatar kula da harkokin al’umma da kare aukuwar bala’o’i da ta hanzarta fara rabar da kayyakin jin kai don rage radadi ga mazaunan da abin ya shafa hadi kuma da gyara kauyen da harin ya barnata.

Dukkanin wadannan matakan na zuwa ne bayan kudurin da Sanata Kashim Shettima da ke wakiltar Borno ta tsakiya ya gabatar a kwaryar majalisar na dattawa dangane da harin baya-bayan nan da Boko Haram suka aukar a kauyen Auno.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ma da kansa ya halarci garin Maiduguri a ranar Laraba domin jajantawa da nuna alheni kan harin na Auno da ya faru.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: