Connect with us

LABARAI

Man Da Aka Gano A Arewa-Maso-Gabas Ya Kai Ganga Miliyan Dubu

Published

on

A ranar Larabar da ta gabata ne, Karamin Ministan Ma’aikatar Man Fetir, Cief Timipre Slyba ya bayyana cewa, an samu nasarar gano arzikin Danyan Man Fetir da yawansa ya kai kusan kimanin ganga biliyan daya a yankunan Arewa Maso Gabacin Nijeriya.

Ministan ya bayyana haka ne, a wajen wani taron karawa juna sani na shekarar 2020, wanda Ma’aikatar Man Fetir ta Nijeriya ta dauki nauyi a Babban Birnin Tarayya Abuja.

“Alkaluman da muke samu a halin yanzu, ba su gama kammaluwa ba, amma dai bisa la’akari da wadanda muka tsefe muka kuma tattara a hannunmu, an samu kimanin gangan kusan biliyan daya a wadannan yankuna na Arewa Maso Gabacin wannan Kasa.”

Ya kara da cewa, sakamakon wadannan alkaluma da ke hannunmu ne ya ba mu damar cigaba da fahimtar yanayin wadannan gurare masu albarkacin wannan Man Fetir. Sannan a cewar tasa, akwai gurare da dama masu albarkar Man Fetir, wadanda har yanzu ba a kai ga gano su a wannan kasa ba.

“Saboda haka, akwai bukatar cigaba da hako ire-iren wannan Danyen Man Fetir a Nijeriya, sakamakon gano gurare da dama da aka yi da ke dauke da arziknsa.”

Da yake yin tsokaci game da dokar nan ta Ma’aikatar Man Fetir, wadda aka gabatar a watan Yuni, ya bayyana karfin gwiwar da yake da ita kan kyakkyawar alakar da ke tsakanin Majalisar Dokokin Nijeriya da kuma bangaren zartarwa.

 

“Yanzu haka a Nijeriya kowa ya yarda cewa, akwai bukatar aiwatar da wannan doka ta Ma’aikatar Man Fetir. Yanzu haka, kusan shekaru 20 kenan muna ta faman fadi-tashi akan tabbatar da wannan doka, wanda hakan ke kawo wa Ma’aikatar nakasu, wajen samun wadanda za su zuba hannun jari a cikinta.

“Bari na dan ba da misali, a shekarar 2002, muna da rarar gangar Man Fetir kusan biliyan 22. Sannan, muna da damar samun karin wannan rara daga ganga biliyan 22 zuwa biliyan 37 zuwa shekara ta 2007.”

“Daga shekarar 2007 zuwa yanzu, karin rarar gangar Man Fetir biliyan 37 zuwa 37.5 kacal muka iya samu a matsayin kari, a sama da shekaru 10 da suka wuce. Idan kuwa har haka ne, me yasa ba za a samu sukunin sanya hannun jari a Nijeriya ba?, a cewar tasa.

“Idan kuwa har haka ne, ai babu wani dan kasuwa ko Kamfani da zai yarda ya zuba hannun jari a Nijeriya, kan kila-wa-kala. Sannan, idan babu wanda ya san lokacin aiwatar da wannan doka, ai babu wanda zai yarda ya sa hannun jari a Nijeriya. Wannan ne ma babban dalilin day a sa kusan komai ba ya garawa yadda ya kamata a wannan Kamfani na Mai a Nijeriya”, in ji shi.

“Kowa yanzu ya yarda cewa, an samu daidaito tsakaninmu baki-daya, kama daga kan Kamfani, ‘Yan Nijeriya da kuma ita kanta gwamnati, kan cewa lallai akwai bukatar samar da daidaito a wannan bangare, domin baiwa masu sha’awar sanya hannun jari damar shigowa a dama da su a wannan kasa.

Har ila yau, akwai damammaki masu tarin yawa a Nijeriya, ina kuma da tabbacin cewa, idan za mu iya daidaita al’amura tare da kawo zaman lafiya a tsakaninmu, harkokin sanya hannun jari zai bunkasa a wannan kasa, cewar Karamin Ministan.

“Sa’annan, ina da tabbaci tare da karfin gwiwar cewa, dukkanin ‘Yan Nijeriya masu kishin kasarsu na da yakinin nan da watanni shida wannan doka za ta tabbata. A bangaren farfado da Matatun Man Fetir Kuma, za a fara gyaran Matatar Man Fetir ta Fatakwal, wadda ita ce Matatar Man Fetir mafi girma a Nijeriya a cikin watanni hudu na farkon shekarar 2020.

“Ko shakka babu, a matsayinmu na gwamnati, idan muka samu damar nasarar kammala gyaran wannan Matata ta Fatakwal, wadda ita ce mafi girma kamar yadda aka sani, mun samu gagarumar nasara ta a zo a gani. Kazalika, muna cigaba da duba Matatar Mai ta Warri, sannan muna cigaba da tattaunawa akan ta Kaduna ”, in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: