Connect with us

JAKAR MAGORI

Mutane Sun Gudu Daga Gidajensu Saboda Arangamar ’Yan Kungiyar Asiri

Published

on

Wasu mazaunan sassan garin Uyo da Jihar Akwa Ibom, sun tsere daga mazaunansu, sakamakon farmakin ‘yan daba wadanda ake kyautata zaton ‘yan qungiyar asiri ne. Bincike ya nuna cewa, yankunan da farmakin ya fi qamari dai sun hada da, yanyar makarantu da yankin Itu da Ikot Ekang da Church road da Nelson Mandela Street da Ikot Ndem da Udoette da dai sauran su. A cikin yankunan da aka bayyana sun hada da jami’ar Uyo da kwalejin kimiya ta Uyo da kuma jami’o’i masu zaman kansu. Bincike ya nuna cewa, mazauna yankin suna zama ne cikin firgici, sakamakon farmakin ‘yan qungiyar asiri, wadanda suke mamaye musu gidaje da shaguna da adduna da kuma muyagun makamai a cikin dare da rana.

Wani mazauna yankin ya bayyana cewa, “wadannan matasa dai ‘yan qungiyar asiri ne, inda suke yawan kai hare-hare a koda yaushi. A wasu lokutan, mutane da kansu suke nuna musu wurin da za su kai hari. “inda lamarin ya fi qamari wurin da suke shiga shagunan mutane suna qwace musu wayoyi da kudade da kayan marmari da kuma wasu kayayyaki. Wannan lamari ya faru ne a dukkan yankunan da na ambata musammam ma yankin Itu da kuma yanyoyin makarantu,” in ji shi.

Wata mai shigo a kusa da makaranta ta bayyana wa manema labarai cewa, tana kai qarfe 10 zuwa 11 na dare a wurin kasuwancinta, amma sakamakon farmakin ‘yan qungiyar asiri ya daidaita lamarin. “Ina bude shagona tun da sanyen safiya har zuwa qarfe 10 zuwa 11 na dare, amma a yanzu ina rufewa da wuri saboda tsoron kar lalatattun yarannan su yi min fashi ko kuma su kashe ni.

“Mafi yawancin masu shaguna a wannan yankin sun rufe. An yi min fashi sau hudu tun lokacin da na bude wannan shagon. Wasu daga cikin masu shaguna sun gudu, domin kar a kashe su. “Akwai wani lauya yana da gida a wannan yankin. Sunan lauyen Barista Umoh, yana aiki a ma’aikatar shari’a ta jihar. Ya gudu ya bar gidansa saboda farmakin ‘yan qungiyar asiri. “A yanzu haka mun samu labarin cewa, lauyan ya na qoqarin saida gidansa. Amma matsalar ita ce, waye zai sayi gida a yankin da babu tsaro,” in ji ta.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSP Odiko MacDon ya bayyana cewa, ‘yan sanda suna sane da lamarin, inda a halin yanzu an girke jami’an tsaro a yankunan jami’ar Uyo da kuma wasu sassan yankuna. “Muna bakin qoqarinmu domin daqile lamarin, sannan muna kira ga mazauna yankunan da lamarin ya fi qamari da su taimaka mana da bayanai sirri da za su kai ga damqe wadannan ‘yan daba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: