Connect with us

LABARAI

‘Nijeriya Ba Ta Kai Matsayin Da Za Ta Iya Cin Bashin Dala Bilyan 23 Ba’

Published

on

Wani masanin harkokin kudi, kuma shugaban kamfanin harkokin kudin nan na, Cowry Asset Management Limited, Mista Johnson Chukwu, ya ce kasar nan ba ta kai cancantar iya cin bashin tsabar dalar Amurka har bilyan 23 ba a yanzun haka, kamar yanda gwamnatin tarayya ke kokarin ciwowa.

Chukwu ya bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi jiya a Legos, a lokacin da yake amsa tambaya a kan ciwo bashin da gwamnatin ta tarayya ke kokarin yi.

Chukwu y ace, “Kudaden canjin kasar nan da ta samu daga cinikin danyan mai a shekarar 2018 shi ne dalar Amurka bilyan 18.2, sa’ilin da a shekarar 2019 kudaden suka haura zuwa dalar ta Amurka bilyan 20. Bashin da ake bin kasar nan a halin yanzun shi ne naira Tiriliyon 22.2.

“In har gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin dala bilyan 22, hakan zai iya kai tulin bashin da ake bin mu a waje kimanin dala bilyan 47 kenan. Wanda hakan zai sanya, ruwan bashin kadai zai haura kasha 53 na abin da kasar nan take samu.

“Ba zai yiwu mu iya ciwo irin wannan bashin makudan kudaden ba, domin ba za mu iya biyan ruwan da ke cikin sub a ma, ballantana ainihin bashin.

Minister Kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, wacce ta gabatar da bukatar ciwo bashin a madadin gwamnatin tarayya, a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin ciwo basuka a cikin gida da wajen kasar nan, na Majalisar Dattijai, ta yi bayanin cewa gwamnatin tarayya ta yanke shwawarar tunkarar bankin kasar Sin mai suna, China-Edim Bank, domin ciwo bashin dalar Amurka bilyan 17, sa’ilin kuma da wasu kafofin bayar da rancen na Duniya kamar bankin Duniya da bankin bunkasa nahiyar Afrika, suka gaza ranta mata kudaden.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: