Connect with us

LABARAI

Rudani A Bayelsa Game Da Hukuncin Kotun Koli

Published

on

  • Jihar Za Ta Zauna Ba Gwamna Daga Yau Juma’a – APC
  • Mun Samu Tsuntsu Daga Sama Gasasshe – PDP

Ga dukkan alamu hukuncin da kotun koli ta yanke ya jefa Jihar Bayelsa cikin rudani sakamakon takaddamar da ta biyo bayan hukuncin a tsakanin jam’iyyar APC mai mulkin kasa da takwararta ta adawa ta PDP.

A yayin da ‘ya’yan PDP da sauran magoya bayanta ke murna har baki saboda fahimtar hukuncin kotun kolin cewa dantakararsu ne za a rantsar da shi sabon Gwamnan Bayelsa, sai kuma ga bayanai daga Shugaban APC, Adams Oshiomhole da yammacin jiya cewa dan takarar na PDP, Sanata Douye Diri bai cika ka’idar da kotun koli ta bayar ba, don haka ba zai yiwu a rantsar da shi a matsayin Gwamnan Bayelsa ba, bisa hukuncin da kotun kolin ta zartar.

Oshiomhole ya nunar da cewa, hukuncin da kotun kolin ta yanke ya yi bayani ne cewa a ba da takardar shaidar lashe zabe ga dan takarar da ya cika sharudda a zaben, baya ga Dabid Lyon.

A cewarsa, idan kuma haka za a bi, to babu wani dan takara da ya cika sharudda na lashe zaben baya ga Lyon, inda ya kara da cewa bisa hakan, Jihar Bayelsa za ta kasance ba ta da Gwamna a halin yanzu.

Kotun koli dai ta soke zaben zababben gwamnan Bayelsa, Dabid Lyon, da mataimakin sa Biobarakuma Degi-Eremieoyo a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

A karkashin jagorancin Mai Shari’a Mary Odili, dukkanin alkalan kotun biyar bakinsu ya zo daya a hukuncin da suka zartas a a jiya Alhamis, inda suka tabbatar da cewa, Degi-Eremieoyo, ya gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta bogi ne ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

Kotun ta ce dukkanin bayanan da Degi-Eremieoyo, ya bayar a fom mai lamba CF 001, ga hukumar zaben domin tsayawa takaran zaben Gwamnan a zaben da ya gudana a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019, a Jihar ta Bayelsa, suna da matsala.

Da yake karanta hukuncin kotun a madadin sauran alkalan kotun, Mai Shari’a Ejembi Degi, ya yi riko da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2019, inda ta bayyana rashin cancantar Degi-Eremieoyo, tsayawa a zaben gwamnan.

Kotun kolin ta yi riko da cewa, Degi-Eremieoyo, suna amfani da tikiti guda daya ne a wajen zaben Gwamnan, don haka rashin cancantar sa ta soke tsayar da shi din da Jam’iyyar APC ta yi.

Kotun kolin ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta bayar da sabuwar takardar shaidar cin zabe ga dan takaran Jam’iyyar da ke biye wa wanda aka soken da mafi yawan kuri’u da kuma samun kuri’un da suka cancantar da shi a dukkanin mazabun Jihar.

‘Yan jiahr ta Bayelsa dai akwai masu goyon bayan Lyon da kuma Sanata Douye na PDP, inda magoya bayan PDP ba a jihar kadai ba har ma da kasa bakidaya ke murnar cewa sun tsinci dami a kale ko kuma tsuntsu ya fado musu daga sama gasasshe.

Dan takar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya karbi wannan hukiuncin da zuciya daya kuma abin ya yi masa dadi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: