Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Ta Yi Alwala Da Ruwan Fitsari Har Ta Yi Sallah Ba Ta Sani Ba, Yaya Hukuncin Sallarta?

Published

on

Tambaya:

Assalamu alaikum. Na kasance lokacin da Ina bording school idan senior na ya aikeni debo ruwa kafin na kawo masa ruwan sai na yi fitsari a cikin ruwan, kuma ban san adadin mutanen da na yi wa hakan ba, saboda ganin yadda senior yinmu suke gallaza mana da sunan seniority, ga shi yanzu ban san inda zan gansu ba ballantana na nemi afuwarsu, me ya kamata na yi kenan a yanzun, kuma ya hukuncin wacce ta yi yi alwala da ruwan da aka sa fitsari kuma har ta yi sallah alhali ba ta sani ba? Na gode, Allah ya kara maka imani da ilmi mai amfani.

 

Amsa:

Wa’alaikumus salam, To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya kare mu daga irin wannan danyan aikin, Allah ya sa su kuma shawagabannin makarantu su kula da irin wannan cin zalin, ina baki shawara ki yawaita istigfari, mutukar lokacin da kika yi hakan kin balaga, su kam sallarsu da wankansu sun inganta, saboda a zance mafi inganci na malamai duk wanda ya yi alwala da ruwa mai najasa, bai kuma gano hakan ba, sai bayan lokacin sallar ya fita, to ba zai sake sallar ba, haka ma wanda ya yi wankan janaba, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki.

Duba Al’ausad na Ibnul- munzir shafi na 18.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado 151

Tambaya:

Assalamu alaikum, Malam mace ta mutu ta bar ‘ya’yan Goggwanninta da kaninta da suka hada uwa daya da ‘ya’yan kannanta da suka hada uwa kawai, sai kuma dan kaninta da suka hada uba kawai?.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za a raba abin da ta bari gida: 6, kaninta da suka hada uwa daya kashi daya, ragowar kashi biyar din sai a bawa dan kaninta da suka hada uba daya da mahaifinsa

Allah ne mafi sani.

 

Hukuncin Amfani Da Maganin Da Yake Hana Haila

 

 

Tambaya:

Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi daya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al’ada na sha, bayan mun hadu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske?

 

Amsa:

To ‘yar’uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, amma da sharuda guda biyu:

  1. Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda fadin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195.

  2. Ya zama da iznin miji ne, idan hakan ya shafe shi, kamar idan tana iddar da ciyarwa ta wajaba akanshi, to anan bai halatta ta yi amfani da abin da zai hana haila ba saida izninsa, haka nan idan ya zama maganin zai hana daukar ciki to a nan ma dole saida iznin miji.

Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta ta so, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.

Don neman karin bayani, duba: Dima’uddabi’iyya shafi na: 54.

Allah ne mafi sani.

 

 

Ya Halatta Na Sayi Kare Saboda Gadi A Gidana?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum. Dr. Mene ne hukuncin ajiye kare a gida saboda gadi? Allah muke roko ya kara wa Dr lafiya da basira Ameen.

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Ya tabbata a hadisin Bukhari da Muslim cewa: “Mala’iku ba sa shiga gidan da yake akwai hoto ko KARE a ciki.

A wani hadisin mai lamba ta: 2974 da Muslim ya rawaito Annabi s.a.w. yana cewa: “Duk Wanda ya rike KARE, in ba Karen noma ba ko farauta ko kiwo, to Allah zai tauye masa manyan lada guda biyu a kowacce rana.

 

Da yawa daga cikin malamai sun yi kiyasin KAREN GADI akan wadancan nau’ukan guda uku da suka gabata, don haka ya halatta musulmi ya riki Kare saboda gadi in har akwai bukatar hakan.

 

Ba ya halatta a siyar da kare kowanne iri ne, saboda Annabi ﷺ ya hana cin kudin Kare a hadisin da Muslim ya rawaito kuma ya kira Shi da dauda.

 

Duk da cewa an halatta wadancan nau’ukan guda hudu saboda bukata saidai bai halatta a siyar da su ba, saboda Ka’ida sananniya a wajan malaman Fikhu.

Idan mutun yana bukatar daya daga cikin wadanchan nau’uka na karnuka guda huɗu da suke halatta, kuma bai samu wanda zai ba shi kyauta ba, ya halatta ya siya, Amma zunubin sayarwar yana kan wanda ya sayar tun da shi ne bai bayar ba, kamar yadda Ibnu Hazm ya fada a littafinsa na Muhallah 4/793.

 

Fatawar Rabon Gado (152)

Tambaya:

Assalamu Alaikum Dr, Allah ya kara fahimta dan Allah rabon gadone malam yayan mutun dayane su uku sai biyu suka mutu sukabar daya shiwanda yake raye betaba haihuwa ba sukuma wayanda suka rasu sunada yaya ya rabon zai zama .A yayan akwai maza akwai mata mata maza hudu mata shidda Allah yasa mudace.

 

Amsa:

Wa alaikum assalam. Za a raba gadon ne ga ‘ya’yansa kawai.

Yana daga cikin ka’idojin rabon gado wadanda malamai suka cimma daidaito akansu: “Dukkan ‘yan’uwa ba sa gado mutukar a cikin ‘ya’yan mamaci akwai namiji.

Allah ne mafi sani.

 

Wacce Irin Tsintuwa Ce Ake Yi Ma Cigiya?

 

Tambaya:

Wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: ₦500, a wurin kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba… Ya ya kamata yayi da kudin tsintuwar?, suna ajiye yanzu haka kusan wata daya.

 

 

Amsa:

To dan’uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761.

Amma idan abin da ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa, to ya l halatta ya yi amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi ﷺ ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce: In ban da ına tsoron na sadaka ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta: 2527, sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar cigiya.

Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce za’a koma al’adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba, wato daya bisa hudun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare daya ya yi amfani da ita ba tare da yayi cigiya ba.

Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai (₦5,00) din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba kudi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta ba.

Don neman karin bayani duba: Al-mugni 6/351.

Allah ne mafi Sani.

 

Wasu Daga Cikin Abubuwan Da Suke Bata Sallah

 

Tambaya:

Assalamu alaikum malam tambaya dan Allah malam kamar wanne aikine take bata sallah kai tsaye

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Ayyukan da suke bata sallah suna da yawa, daga ciki: akwai dariya Sannnan yawan motsi da soshe-soshe yana bata sallah a wajan wasu malaman, magana wacce ba ta gyaran sallah ba na daga cikin abububuwan da suke bata sallah.

Yin tusa ko fitsari ko cin abinci ko abin sha suma suna ciki. duk abinda yake bata alwala yana bata sallah.

Allah ne mafi sani.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: