Connect with us

NOMA

Turkiyya Za Ta Zuba Jarin Dala Miliyan 15 A Fannin Noman Nijeriya

Published

on

Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya sanar da cewa, Gwamnatin Kasar Turkiyua zata zuba jarin dala miliyan 15 a fannin aikin noman Nijeriya na wa’adin shekaru biyu.

Ministan Ma’aikatar Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya sanar da hakan ne a yayin da ya karbi tawagar masu zuba jari a fannin aikin noma daga kasar Turkiyya.

Wani babban Jami’in hada-hadar kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Turkiyya dake a Nijeriya Mista Onur Akgul ne ya jagoranci tawagar zuwa kai ziyarar ofshin na Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri.

Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya ci gaba da cewa, Nijeriya zata samu mutukar kwarewa a fannin aikin noma irin na kasar Turkiyya, musamman ganin cewar, kasar ta Turkiyya, ta na daya daga cikin kasashen duniya da ta yi fice wajen yin aikin noma na zamani, musamman a tsakanin kasashen dake a Gabas ta tsakiya.

Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha ya kara da cewa, kasar ta Turkiyya ta shafe dimbin shekaru kan yin aikin noma na zamani wanda har ta kaiga wasu kasashen duniya suna yin koyi da ita wajen bunkasa fannin aikin noman su.

A cewar Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri, inda Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya kara da cewa, akwai bangarori da dama Nijeriyar da kasar ta Turkiyya zasu iya yin hadin gwaiwa, musamman ta bangarorin samar da kayan aikin yin noma na zamani, yadda Nijeriya zata iya cimma burin da ta sanya agaba na wadata kasar da wadataccen abin da alummar ta suke bukata.

Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya kuma bai wa tawagar a ofishin jakadancin kasar Turkiryya dake a Nijeriya tabbacin basu dukkan goyon bayan da ya dace kan goyon bayan Ma’aikatar ta Noma da Raya Karya.

Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya ci gaba da cewa, Ma’aikatar Noman da Raya Karkara zata fito da wani kundi da zai taimaka wajen sanya daukacin ma su zuba jari a fannin aikin noma, inda hakan kuma zai bai wa gwamnatin tarayya cika muradin ta ha bunkasa fannin aikin noma a kasar nan.

A cewar Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri ya kuma yi alkwarin cewa, Ma’aikatar Gona da Raya Karkara zata samar da wani kafa da za’a dinga sanar da daukacin masu son zuba jari a fannin na aikin noma a kasar nan da masu son zuja jarin suke bukata, musamman don sanar dasu kan irin dimbin nasarorin da Ma’aikatar Gona da Raya Karkara da kuma hukomin dake a karkashin ta suka samar.

A nasa jawabin tunda farko, babban Jami’in hada-hadar kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Turkiyya dake a Nijeriya Mista Onur Akgul ya godewa Karamin Ministan Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Alhaji Mustapha Baba Shehuri, kan dsmar da Nijeriya ta bai wa kasar ta Turkiyya don ta zuba jarinta a fannin aikin noman Nijeriya.

Babban Jami’in hada-hadar kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Turkiyya dake a Nijeriya Mista Onur Akgul ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Turkiyya zata zuba jarin dala miliyan 15 a fannonin aikin aikin noman Nijeriya.

A karshe, babban Jami’in hada-hadar kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Turkiyya dake a Nijeriya Mista Onur Akgul ya bayyana cewa, har ila yau, kasar ta Turkiyya, zata kuma zuba jari tsarin samar da kayan aikin noma na zamani, bayar da horo, samar da wadataccen abinci, da kuma bayar da dauki ga manoman dake a karkarar dake a cikin Nijeriya a cikin shekaru biyu bayan an fara gudanar da hadakar a tsakanin Nijeriya da kasar ta Turkiyya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: