Connect with us

Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Juma’a 12 Zuwa Alhamis 18 Ga Jimada Sani 1441, Bayan Hijira

Published

on

12 Ga Jimada Sani 1441 (7/2/2020)

Assalamu alaikum, barkanmu da juma’atu babbar rana,za mu fara waiwayen kanun labarunmu na wannan makon ne da ranar goma sha biyu ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga Fabrairun 2020.

 

 1. A yau juma’a shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Adis Ababa ta kasar Ethopia/Itofiya domin halartar taron kungiyar tarayyar kasashen Afirka A.U. a takaice, zai dawo ranar laraba idan Allah Ya kai mu.

 

 1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da wasu sabbin jiragen sama na yaki masu saukar ungulu da ake kiransu da sunan AGUSTA HELICOPTERS, da aka sayo wa sojojin sama na kasar nan don taimaka musu murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram da sauran ‘yan bindiga, da kidinafas da ‘yan tsagera da ke addabar kasar nan.

 

 1. A shirye-shiryen tinkarar zaben shekarar 2023 hukumar zabe ta kasa ta rage jam’iyyun siyasa guda saba’in da hudu, ta bar guda goma sha takwas kadai saboda su ne kadai suka cika sharuddan ci gaba da kasancewa jam’iyyun siyasa.

 

 1. Majalisar wakilai ta bukaci hukumomin da abin ya shafa irin su NAFDAC da ke kula da lafiyar abinci da magunguna ta kasa, su sanya ido ga masu yin abincin saidawa, don hana su amfani da kwayar magani ta fanadol/panadol a girki, saboda illar da hakan ke da ita ga kodar mutum. Wasu kan jega fanadol a girki don girkin ya yi saurin dahuwa.

 2. ‘Yan sanda sun kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga su biyu a jihar Kaduna.

 3. Kotu ta amince likitocin iyalan Shek Zakzaky su duba lafiyar uwargidarsa a gidan gyara hali da ke Kaduna, da sanya ashirin da hudu da ashirin da biyar ga wannan watan su zama ranakun da za a ci gaba da shari’arsu.

 4. NEPA! NEPA!! NEPA!!! Har ina yabonku ashe kwa ce ka ma daina. Jiya dai gabadaya ba mu samu wuta ba sai da daddare. Haka ma shekaranjiya. Talakan Nijeriya na nan yana ci gaba da biyan kudin zama a duhu, a zamanin mulkin Baba Buhari mai kaunar talaka, da talaka ke kauna.

 

 1. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau, da za ta fito yau da safe domin kuwa rubuce-rubucen da na yi a dandalina na soshiyal midiya daga alhamis da ta gabata zuwa jiya alhamis na nan a cikinta.

Af ! Gobe asabar idan Allah Ya kai mu, za a yi bikin cikar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris arba’in da biyar a kan karagar mulkin masarautar Zazzau. Na mu sarkin ba irin nasu ba ne. Allah Ya ja zamanin sarki Amin.

 

13 Ga Jimada Sani 1441 (8/2/2020)

A asabar, goma sha uku ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Fabrairu na 2020.

 

 1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Adis Ababa ta kasar Itofiya, don halartar taro na talatin da uku na kungiyar tarayyar Afirka A.U. a takaice. Sai dai kafin ya bar Nijeriya a jiya juma’a sai da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kano Ganduje tare da ‘yan majalisar dokoki ta jihar. Ganduje ya ce duk a Nijeriya babu inda ake zama lafiya irin jihar Kano.

 

 1. Sarkin musulmi Abubakar Sa’ad na uku, ya nesanta kansa da kungiyoyin matasan Arewa da suka yunkura domin kafa rundunar tsaro mai suna SHEGE KA FASA. Ya ce ba wata kungiya da ta tintibe shi ko ta nemi shawararsa a kan hakan.

 

 1. Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yi kiran a sake duba batun sayar da kamfanonin lantarki da gwamnati ta yi ga ‘yan kasuwa domin kuwa babu wutar, ga talaka na biyan kudin zama a duhu, da kokarin sai ya biya fiye da kudin da yake biya a yanzun na zama a duhu.

 

 1. Kidinafas sun sako ‘ya’ya biyu na wani likita da ke zaune a Kaduna Mista Philip Ataga, da suka yi kidinafin matarsa da ‘ya’yan nasa biyu a a ranar ashirin da biyar ga watan jiya, suka kashe matar tasa.

 

 1. Kudin ajiya na kasashen ketare da Nijeriya ke da su da aka fi sani da EXTERNAL FOREIGN RESERVE, sun ragu zuwa Dala biliyan hudu da ‘yan kai (4.47) a shekarar bara ta 2019.

 

 1. Bayanai na nuna a cikin shekaru biyu da suka gabata, an yanke wa wasu tsofaffin gwamnoni uku da wasunsu ma sun zama sanatoci hukuncin dauri saboda laifuka da suka shafi almunbazzaranci da wawurar kudaden jihohinsu a lokacin da suke kan kujerar gwamna. Akwai Dariye na jihar Filato da aka yankewa hukuncin daurin shekara goma, sai Nyame na jihar Taraba da aka yankewa shekara goma sha biyu, sai Orji Kalu na jihar Abiya da aka yankewa hukuncin daurin shekara goma sha biyu.

 

 1. ‘Yan sanda sun ce harbar musu jirgi mai saukar ungulu da sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda biyu da ‘yan kungiyar Ansaru suka yi a lokacin da suke fafatawa a dajin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, har suka kashe ‘yan kungiyar su dari biyu da hamsin, ba za ta karya musu karfin gwiwa ba. Yanzun ma suka daura damarar yakar ‘yan bindiga da kidinafas da ke addabar jihohi musamman jihar Kaduna da jihohin da ke makwabtaka da ita.

 

 1. Kotun koli ta ki yarda da bukatar iyalan Abacha, su iya kaiwa ga wasu asusun ajiyarsa da ke Ingila da wasu kasashen duniya. Obasanjo ne dai a zamanin mulkinsa ya sa aka dode duk irin wannan ajiya tasu da ke kasashen ketare.

 

 1. Sojojin sama sun kai farmaki wata mabuya ta ‘yan ISWAP da ke da nasaba da kungiyar Boko Haram a Kaza da ke jihar Barno.

 2. Wasu karin ‘yan Nijeriya su dari da sittin da daya sun dawo gida Nijeriya daga Libiya.

 

Af! Kamar yadda na yi bayani a makon jiya, a makon gobe ne zan horas da ma’aikatan gidan rediyon FREEDOM, cikon na goma na gidajen rediyo da talabijin da nake bi ina horas da ma’aikatansu. Su ne kamar haka:

 1. NTA

 2. FRCN

 3. KSMC

 4. LIBERTY RADIO

 5. NEWAGE NETWORK

 6. KASU RADIO FM

 7. DITV/ALHERI RADIO

 8. KAMA

 9. NAGARTA RADIO

 10. FREEDOM RADIO.

Sai na 11 rediyon SPIDER F.M. da nake shirin yi musu nasu.

Wannan dama ce ga duk gidan rediyo ko talabijin ko jarida da ke bukatar in zo in horar/horas masa da ma’aikata bangaren fassara da amfani da daidaitacciyar Hausa a aikin rediyo da talabijin da jarida da intanet, ya tintibe ni.

 

14 Ga Jimada Sani 1441 (9/2/2020)

Muhimman kanun labarun a lahadi, goma sha hudu ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da tara ga watan Fabrairu, na 2020. Su ne:

 

 1. A sabbin jiragen yaki masu saukar ungulu da aka sayo, hukumomin sojan sama sun kawo daya Kaduna da zai taimaka wajen yakar ‘yan bindiga da kidinafas da ke addabar jihar ta Kaduna da jihar Neja.

 

 1. Wasu mahara sun kai hari al’umomi uku da ke yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

 

 1. Kanawa sun goyi bayan matasan Arewa da suka yunkura don kafa rundunar tsaro ta SHEGE KA FASA don taimaka wa tsaron Arewa, shigen AMOTEKUN ta yarbawa. Sai dai zuwa yanzun gwamnan jihar Kano Ganduje, da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku, sun nesanta kansu da rundunar, inda shi Sa’ad ya ce ba a tuntube shi ba. Su kuma matasan na Arewa suka mayarwa masa da martanin ba su yi mamakin jin haka daga bakinsa ba.

 

Jama’a da fatan za a yi hakuri labarun yau ba yawa saboda kasancewar karshen mako.

 

Af sabon salo! Yanzun yayin sakin faifan bidiyo ake yi a soshiyal midiya na wata ga ta tsirara an gama lalata da ita, ko wani ga shi zindir ya gama lalata da wata. Ni dai bakina da goro kuma na yi nan.

 

 

15 Ga Jimada Sani 1441 (10/2/2020)

Idan muka dubi litinin, goma sha biyar ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma ga watan Fabrairun 2020.

 

 1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa sabon yunkirin da shugabnnin kasashen da ke cikin kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS a takaice suka yi na amfani da albarkatun da Allah Ya huwace musu wajen magance matsalolin da ke addabarsu har da bangaren yaki da ta’adanci. Ya yi wannan bayani ne a wajen taron kungiyar tarayyar Afirka A.U. da ke gudana a Adis Ababa. Ya ma gana da firaministan kasar Canada/Kanada Mista Trudeam a wajen, sannan kasashen na Afirka sun samar da wata shalkwata ta wani kwamiti da suka kafa mai suma CISSA a takaice.

 

 1. Kungiyar Dattawan Arewa da aka fi sani da NORTHERN ELDERS’ FORUM sun ce hanyoyin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bi don magance matsalar tsaro ba masu bullewa ba ne, tare da ba shi shawarar ya fatattaki manyan hafsoshin tsaro su tarkata inasu-inasu su san inda dare ya musu. Sai dai fadar shugaban kasa ta bakin Femi Adeshina, ta mayarwa da kungiyar martanin cewa kungiya ce ta ‘yan adawa ta mutum daya wato Farfesa Ango Abdullahi. Femi Adeshina ya ce a zaben 2019 Atiku Abubakar suka rufawa baya ba Buhari ba, saboda haka komai ma Buhari ya yi ba zai burge su ba.

Kungiyar ta dattawan Arewa ta bakin Dafta Hakeem Baba Ahmed ta ankarar da musulmi da kiristoci da kada su yarda kungiyar Boko Haram ta yaudare su cewa wani addini take yi wa aiki.

 

 1. A yau litinin rundunar tsaro ta yankin jihohin kudu maso yammacin kasar nan wato jihohin yarbawa AMOTEKUN za ta fara raba takardun cikewa don daukar dakarunta da za su mata aiki. Su kuma jihohin kudu maso gabashin kasar nan wato jihohin Inyamurai, jiya gwamnonisu suka yi taro a Inugu don kafa tasu rundunar ta tsaro da nan gaba kadan za su bayyana sunanta. Su ma matasan Arewa sun bullo da tasu rundunar mai sunan SHEGE KA FASA, da manyan Arewa suka ce ba ruwansu.

 

 1. ‘Yan sandan jihar Kaduna sun ce tabbas wasu kidinafas sun je har gidan tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Abdullahi Mustafa suka tafi da diyarsa sai dai ba su sha a ta dadi ba saboda ‘yan sanda sun kai dauki har suka bindige daya daga cikin kidinafas din ya sheka barzahu. Wasunsu kuma sun tafi da raunin harbin bindiga.

 

 1. ‘Yan sandan jihar Kaduna sun ce zuwa yanzun sun kama mutum takwas ‘yan kungiyar nan ta ANSARU da suka kai wa sarkin Fataskum hari a hanyar Zariya kwanakin baya, da sauran laifuka na kisa da kidinafin a jihar Kaduna.

 2. Kungiyar kiristoci ta kasa CAN ta ce babu mamaki a ga matasa na tururuwa suna shiga kungiyar Boko Haram.

Af! Ma’aikatan jami’o’i da na kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na nan sun ce suna ci gaba da dakon sabon albashi da ariyas, da ya soma aiki tun watan Afrilun shekarar 2019. Su har yau shiru, suka ce ba amo ba labari.

 

16 Ga Jimada Sani 1441 (11/2/2020)

A talata, goma sha shida ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Fabrairu na shekarar 2020.

 

 1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wata babbar hanya da ke jihar Barno shekaranjiya lahadi da karfe goma na dare, suka kashe fiye da mutum talatin, wasu a motoci suka sa musu wuta, suka kwashi mutane masu yawan gaske, har da mata da yara suka yi gaba da su, a titin Maiduguri zuwa Damaturu. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin za a gama da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi da ke addabar kasar nan. Ya kuma ba da tabbacin za a sako duk wani yaro da ke hannunsu.

 

 1. An sako Mohammed Adoke tsohon ministan shari’a bayan cika sharuddan ba da belinsa da ya hada da naira miliyan hamsin. Ana zarginsa da hannu a wata badakala ta mai ta Malabu.

 

 1. Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin kasar nan wato yankin yarbawa, na shirin rubuta wa gwamnatin tarayya takardar neman izini da lasisin bai wa rundunarsu ta tsaro ta AMOTEKUN bindigogi.

 

 1. Kamfanonin lantarki na nan sun kara himma wajen ganin an kara wa talakan Nijeriya kudin zama a duhu.

 

 1. Ana kokarin kai ruwa rana tsakanin majalisar gudanarwa ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da shugaban jami’ar mai barin gado Farfesa Ibrahim Garba. Majalisar na cewa ya kamata tun yanzun ya mika ragamar mulkin jami’ar ga daya daga cikin mataimakansa ya tafi hutun da ya kamata ya tafi kafin karewar wa’adinsa a watan jibi. Shi kuma ya ce ba inda za shi tunda wa’adinsa bai kare ba da saura.

Af! Na lura wata hanyar da gwamnoninmu na Arewa ke taimaka wa fatara da talauci, ita ce ta kin tallafa wa gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu da ke Arewa. A yanzun haka akwai gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu da ke nan Arewa da na san ma’aikatansu, na bin su albashi na kusan shekara biyu. Gwamnoninmu sun gwammace su biya irin su TVC da CHANNELS na Kudanci miliyoyin naira, don watsa musu shirye-shiryensu. Kuma sai sun biya kudin sannan su musu. Mu kuwa a nan Arewa, ko gwamnonin sun sa a watsa musu, sai ka tarar a bashi aka musu. Sai an kusan shekara ko fiye ana bi ba a biya ba. Kuma a arha. Ana kuma zargin gwamnonin namu da ba ‘yan kudun mukamai na manyan masu taimaka musu ko ba su shawara bangaren labaru. Ta yadda duk wata kwangilar watsa/yada labaru da gwamnonin za su bayar, sai a kai wa kafofin labaru na kudancin kasar nan. Ana tatse arzikin Arewa ana azurta ‘yan Kudu.

 

17 Ga Jimada Sani 1441 (12/2/2020)

Idan muka dubi laraba, goma sha bakwai ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Fabrairu na 2020.

 1. Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta ware dala biliyan daya domin yakar ta’adanci a kasashen.

 2. Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adeshina, ya ce ana ta damun shugaban kasa Buhari ya bayyana wa jama’a kaddarorin da ya mallaka, babu inda shugaban kasa ya taba daukar alkawarin zai yi hakan.

 3. Gwamnatin tarayya ta ce ta hanyar soshiyal midiya ‘yan ta’adda ke daukar matasan da ke tafiya tare da su ta’addanci.

 4. Bishop-bishop na cocin katolika sun yi kiran a sallami manyan hafsoshin tsaro na kasar nan domin magance matsalar tsaron da ke ci gaba da tabarbarewa.

 5. A jibi juma’a idan Allah Ya kai mu, gwamnonin jihohin kudu maso yammacin kasar nan wato jihohin yarbawa, za su sanya hannu a kudirin kafa rundunar tsaron can yankin AMOTEKUN ya zama doka. Kudirin dokar yana da tanade-tanade guda talatin da takwas.

 6. ‘Yan Majalisar Dattawa sun nuna matukar bacin ransu a game da yadda aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano ke tafiyar hawainiya, tare da bayanin za su kira shugaban kamfanin JULIUS BERGER gaban majalisar don jin dalili.

 7. Patience Jonathan ta kai wa Aisha Buhari ziyara fadar shugaban kasa.

 8. Babban bankin Nijeriya ya ce a shekarar 2019 gwamnati ta samu naira tiriliyan daya da yan kai daga harajin tamanin kaya wato VAT a takaice.

 9. Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti na aiwatar da aikin samar da wutar lantarki na Mambila.

 10. Shugaban kungiyar kwadago na kasa Ayuba Wabba ya yi kiran a canza tsarin tsaron kasar nan.

Af! Ma’aikatan jami’o’i da na kwalejojin foliteknik da kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, sun ce suna ci gaba da dakon sabon albashi da ariyas, na karin albashin da aka yi, ya kuma soma aikin tun watan Afrilu na shekarar da ta gabata. Suka ce gwamnatin tarayya ta dau alkawarin kafin watan shekaranjiya na Disamba ya kare, kowa zai ga alat na sabon albashin da kuma ariyas, suka ce amma har yau shiru, ba amo ba labari.

 

18 Ga Jimada Sani 1441 (13/2/2020)

Za mu kammala waiwayen kanun labarun na wannan makon da alhamis, goma sha takwas ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Fabrairu na 2020.

 

 1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Nijeriya daga Adis Ababa ta kasar Itofiya, wajen taron tarayyar kasaahen Afirka da aka yi karo na talatin da uku. Sai dai da jirginsa ya iso gida Nijeriya, bai zarce ko’ina ya sauka ba, sai jihar Barno, inda ya je ya jajanta wa gwamnatin jihar Barno da jama’ar jihar, kisan gillar da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi wa wasu matafiya su fiye da talatin, suka kona motocinsu a can jihar ta Barno. Sai dai wasu bayanai na nuna wasu mutanen na ta yi wa shugaban kasa ihun BA MA SO a lokacin da ya isa can.

 

 1. ‘Yan majalisar wakilai sun bukaci kwamitin majalisat na bangaren soja, ya gudanar da bincike a kan wajen da sojoji suka kafa mai suna SUPER CAMP da a kusa da wajen ne ‘yan Boko Haram suka kashe matafiyan. Har ila yau majalisar ta bukaci bangaren zartaswa ya ayyana dokar ta baci bangaren tsaro a kasar nan.

 

 1. Wasu ‘yan bindiga su fiye da dari sun je kauyen Bakali da ke Fatika, a yankin karamar hukumaf Giwa da ke jihar Kaduna, ranar talata da wuraren karfe hudu na yamma, suka tarwatsa jama’a tare da kulle wasu iyalai su goma sha shida a cikin gida, suka sa musu wuta suka kone gabadaya.

 2. Shugaban Majalisar Wakilai Gbajabiamila ya roki Amurka ta agaza wa Nijeriya yakar ta’adanci da take ta fama da shi a yanzun haka.

 3. Su Wole Soyinka da Sanata Shehu Sani sun yi wa Sowore rakiya kotu jiya, inda kotu ta nemi gwamnati wato bangaren masu tuhuma, su biya naira dubu dari biyu, saboda yawan bata lokaci da suke yi a kan shari’ar, kusan a duk lokacin da aka je kotu sai su ce ba su gama shiryawa ba tukuna.

 4. Ingila ta dakatar da kudaden da take daukar nauyin sakatariyar kungiyar kasashe renon Ingila da aka fi sani da Common Wealth Secretariate.

Af! Shin har ta kai ga haka ne jama’a sun soma maimaita a turen da suka yi wa shugaban kasa Jonathan kafin zaben 2015, ga shugaban kasa Buhari a yanzun?
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: