Connect with us

MU KOYI ADDINI

Yadda Za A Samu Kariya Daga Mai Hassada

Published

on

Tambaya:

Assalamu alaikum Akaramakallah, ina da wani aboki na kud-da-kud, saidai ba ya so ya ga na fi shi da wani abu, idan na samu wani abin alkairi, sai ya aibanta abin ta yadda mutane ba za su kimanta shi ba, abin yana damuna, shi ne na ke so a taimaka min da hanyoyin da zan samu kariya daga mahassada ?

 

Amsa:

Wa alaikum assalamu, To dan’uwa ya kamata ka san cewa babu yadda za ka yi ka wofantu daga mahassada, domin duk wanda Allah ya yi masa ni’ima, dole sai ya samu mahassada, saidai duk da haka akwai hanyoyin da malamai suka fada, wadanda suke hana hassadar yin tasiri:

 1. Neman tsari a wajan Allah daga sharrinsa.

 2. Tsoron Allah da kiyaye umarninsa, duk wanda ya kiyaye Allah, to zai kiyaye shi.

 

 1. Yin hakuri akan abokin gabansa, kar ya ce zai rama mummunan abin da ya yi masa, domin in har bai rama abin da aka yi masa ba, to tabbas Allah zai rama masa.

 

 1. Karfin dogaro zuwa ga Allah, Allah yana cewa a cikin suratu Addalak aya ta 3 “Duk wanda ya dogara ga Allah, to ya ishe shi” idan ka dogara ga Allah sharrin mahassadi ba zai cutar da kai ba, ko da kuwa ka ga wani abu da yake na cutarwa ne to karshensa zai zama alkairi.

 2. Fuskantar Allah madaukaki sarki da tsarkake aiki zuwa gare shi, da yawan ambatonsa.

 3. Tuba daga zunubai, domin ba za’a dora maka wani ya dinga cutar da kai ba, sai idan akwai wani zunubi da ka aikata, ka san zunubin ko ba ka san shi ba.

 4. Yin sadaka da kyautatawa iya abin da zai iya, saboda da wuya Allah ya dora mai hassada akan wanda yake kyautatawa mutane.

 5. Kyautatawa wanda yake yi maka hassadar, saidai wannan yana da tsananin wahala.

In har ka kiyaye wadannan Allah zai taimaka maka, don neman karin bayani duba Bada’iul fawa’id 2\463

Allah ne ma fi sani.

 

Wane Lokaci Ake Biyan Wanda Ya Yi Aiki Ladansa A Kan Tsarin Musulunci?

 

 

Tambaya:

Assalamu alaikum, Malam idan ka bawa mutum aiki yaushe ya kamata ka biya shi ladan aikinsa?

 

Amsa:

Wa’alaikumus Salam, Ana biyan mutum ladansa daga zarar ya gama aikinsa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “Ku bawa dan kwadugo ladansa kafin guminsa ya bushe” kamar yadda Ibnu-majah ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2443, kuma Albani ya inganta shi a Irwa’ul-galil hadisi mai lamba ta: 1498.

Sannan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana taurin bashi, kamar yadda yake cewa: “Taurin bashin mawadaci zalunci ne, yana halatta mutuncinsa da yi masa ukuba” Bukhari a hadisi mai lamaba ta: 2400.

Don haka ya wajaba mutukar yana da hali, ya biya wanda ya yi masa aiki daga zarar ya gama, kar ya jinkirta.

Allah ne mafi sani.

 

 

Fatawar Rabon Gado (153)

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Mace ta mutu taba miji liummiya 1 liabbiya 1 sai “ya”yan shakikiya maza da mata ta ya tabon Zai kama.

 

Amsa:

Wa’alaikum salam. Za a raba dukiyarta gida bakwai, a bawa miji kashi uku, ‘yar’uwa li’abiya kashi uku, sai kuma wacce aka hada uwa daya a bata kashi daya.

Allah ne mafi sani.

 

Hukuncin Aikin A Bankunan Da Suke Da Kudin Ruwa?

 

Tambaya:

Assalamu Alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. Malam tambayata Itace shin ya hukuncin aikin banki ga musulmi? Da gaskene haramun ne? Don Allah a wayar mana dakai. Bissalam

 

Amsa:

Wa’alaikumus Salam To dan’uwa Annabi ﷺ yana cewa: “Allah ya la’anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka” Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598.

Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu’amala da riba, saboda ma’aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike.

Duba fatawaa Allajanah adda’imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.

Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.

Allah ne mafi sani.

 

Alamomin Ilimi Mai Amfani

 

Tambaya:

Assalamu alaikum. Don Allah malam ayi min bayanin alamomin ilimi mai amfani.

 

Amsa:

Wa’alaikumus Salam To dan’uwa akwai abubuwa da yawa da suke nuna ilimi mai amfani, ga muhimmai daga ciki:

 

 1. Aiki Da Ilimi

Yana daga cikin alamomin ilimi mai amfani aiki da shi, domin duk ilimin da ya zama ba’a aiki da shi, to saidai ya cutar da ma’abocin shi amma ba zai amfane shi da komai ba, kamar yadda Annabi ﷺ ya ke cewa (Al-Kur’ani hujja ne gare ka ko kuma akanka) Muslim ne ya rawaito, ma’ana idan ka yi aiki da shi sai ya zama hujja gareka ranar alkiyama, Allah (s.w.t.) ya shigar da kai aljanna da shi, idan kuma ba ka yi aiki da shi ba, sai ya zama hujja akanka, a fara hura wuta da kai kamar yadda Annabi ﷺ ya fada a hadisi

 1. Rashin Yiwa Mutane Girman Kai

Girman kai kuwa ba sifa ce ta daibin ilimi ba, saboda malamai magada Annabawa ne, kuma daga cikin siffofin Annabi ﷺ akwai kaskantar da kai, kuma yana cewa Allah (s.w.t.) ya yi wahayi zuwa gare ni cewa: ku kaskantar da kai, ta yadda wani ba zai yi alfakhari ga wani ba). Muslim

Sai dai wannan ba ya nufin dalibi ya zama sakarai yadda kowa zai raina shi, ya kamata tare da haka ya zama mai mutunta kansa, mai kare girman iliminsa.

 1. Kyautata Zato Ga Mutane

Ana so dalibin ilimi ya zama mai kyautata zato ga mutane, idan mutane suka yi abu, ya samu hanyar da zai nema musu uzuri, to ya yi hakan, kada ya munana zato ga mutane, saidai idan mutumin ya kasance mai aiyuka ne marasa kyau, to wannan babu laifi don an munana masa zato.

Allah ne mafi sani.

 

Hukuncin Fuskantar Alkibla Yayin Biyan Bukata A Bandaki

 

Tambaya:

salam ga tambaya yaya hukuncin mutumin da ya kalli alkibila yayin da yake biyan bukatarsa amma kuma yana bandaki ba’a fili yake ba ?

 

Amsa:

To kanina, malamai sun yi sabani akan mas’alar, Abu-hanifa ya hana hakan, Malik ya tafi akan cewa mutukar a gida ne to babu laifi, saboda hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake cewa: “Na hau dakin Hafsa sai na ga Annabi ﷺ yana biyan bukatarsa, yana fuskantar Sham ya kuma juyawa alkibla baya”, kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 145.

Saidai abin da ya fi shi ne: kar mutum ya fuskanci alkibla, ko da a gida ne, saboda hadisin Abu-ayyub wanda Annabi ﷺ yake cewa: “Idan kuka zo yin bahaya to kada ku fuskanci alkibla kada kuma ku bata baya” Bukhari a hadisi mai lamba ta: 394 da muslim a hadisi lamba ta: 264.

Duba bidayatul-mujtahid 1\115.

Tabbas rashin kallon alkibla yayin biyan bukata shi ne ya fi, saboda hadisin da ya gabata da kuma fita daga sabanin malamai, don haka idan mutum zai gina shadda a gidansa zai yi kyau ya kautar da ita daga alkibla.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado (154)

Tambaya:

Assalamu alaikum Dr. mutum ne ya rasu yabar ‘ya ‘ya biyu mace da namiji kuma yana da kanne maza da mata uwa daya uba daya Amma iyayenshi duka sun rasu to yaya za’ayi rabon gadonshi? ALLAH yakara lfy da ilmi Dr.

 

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba gadon gida uku, a bawa dansa namijin kashi biyu, ‘yarsa mace kashi daya.

Dukkan ‘yan’uwa ba sa gado mutukar mamaci yana Da namiji.

Allah ne mafi sani.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: