Connect with us

JAKAR MAGORI

’Yan Sanda Sun Damke ’Yan Daba 12 A Legas

Published

on

Rundunar ‘yan sanda da ke aiki a yankin Lamgbasa, ta samu nasarar damke ‘yan daba guda 12, wadanda suke farmakin mazauna yankin Ado cikin garin Ajah cikin Jihar Legas. An bayyana cewa, ‘yan daban suna yawan yi wa mazauna yankin da mutane masu wucewa fashi wayoyinsu da kudade da kuma kayayyakinsu.

Wata mazauniyar yankin mai suna Bukky, ta bayyana wa manema labarai cewa, ‘yan daban ke da iko da wannan yankin, a halin yanzu dai an daina gudanar da harkokin kasuwanci a yankin. Ta qara da cewa, ‘yan daban sun saci kwamfuta, inda suka sari mai kwamfutan kafin su amshi ta. A cewarta, ‘yan daban suna gudanar da fashi, inda suke ta harbe-harbe a sama, sannan suka yi wa mutane masu wucewa fashin kayayyakinsu.

Bukky ta ce, “ban taba ganin irin abin da ya faru ba a wannan ranar. Yankin Ado ya kasance kamar fagen yaki. Mazauna yankin sun gudu cikin gidajensu domin kada harsashi ya same su. Mun fada cikin birgici inda ba mu taba tunanin za mu rayu ba, amma muna godiya ga Allah da aka kawo mana dauki. “Suna bi titi-titi suna cewa, babu wanda ya isa ya yi musu wani abu har ma da ‘yan sanda.”

Wani ma mazaunin yankin mai suna Uche ya bayyana cewa, ba a taba samun kwanciyar hankali ba a yankin Ajah koda na kwana daya. Ya kara da cewa, a ranar ma sai da suka gudanar da bikin ‘yan kungiyar asirin wanda suka dade suna gudanarwa a yankin Ajah. Ya ce, yana kan hanyar zuwa ganin abokinsa kusa da hanyar da ake gudanar da wannan biki, sai rikici ya barke.

Uche ya ce, “’yan qungiyar asirin ba sun zo wajen da niyyar yin fada ba ne, amma sai dai sun amshe wa mutane wayoyinsu da kudade da kuma kayayyakinsu. “Haka kuma sun yi wa mutane da dama rauni wadanda suka qi ba su hadin kai. Sun firgita mutane musamma ma wadanda suke zaune a yankin. Mutane ba su ma san hanyar da za su bi su tsira ba. Wasu sun kwankwasa mana qofa, yayin da wasu kuma suka haura mana cikin gida ta katanga domin su tsira. Lamarin ya firgita mutane sosai.”

Wani dan sanda ya bayyana wa manema labarai cewa, ‘yan daba ne suka tada rikici domin su yi wa mazauna yankin fashi da sunan ‘yan kungiyar asiri. Ya qara da cewa, ‘yan sanda daga yankin Lamgbasa wanda Adaobi Okafor yake jagoranta, suka samu nasarar damqe ‘yan daba har guda 12, a mamayen da su ka kaddamar a yankin, inda wasu wadanda ake zargin suka gudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSP Bala Elkana, ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne misalin karfe biyu na dare, aka girke tawagar ‘yan sanda a kauyen Ado, bisa bayanai sirri da suka samu na cewa, wasu ‘yan kungiyar asiri sun hada kai a yankin Tranformer da ke cikin garin Baale Ado, suna shirin tada zaune-tsaye.

Ya ce, “lokacin da suka ga ‘yan sanda, sai suka boye, inda ‘yan sanda suka fara harbi sama domin su tarwaza su. Daga baya sun dawo yankin Okeira Nla, inda suka fara yi wa mutane wadanda suke wucewa fashi. Wasu suna da muyagun makamai a hannunsu. “’Yan sanda sun bi su, inda suka samu nasarar damqe guda 12 daga cikin su. A cikin kayayyakin da aka samu a hannunsu dai sun hada da adduna da wukake da harsashi wanda aka yi amfani da shi
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: