Connect with us

LABARAI

‘Yan Sanda Sun Kama Shugaban Makarantar Da Ya Yi Wa ‘Yar Bautar Kasa Fyade A Delta

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Delta, ta kama shugaban makarantar, Grace Life International School, da ke Oghara- Efe, ta karamar hukumar Ethiope ta gabas, a Jihar Delta, Mista Michael Anigholor, wanda ake zargi da yi wa wata ‘yar bautar kasa da ba a bayyana sunanta ba, fyade.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Mista Hafiz Inuwa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake nuna wa manema labarai wanda ake tuhumar a tare da wasu mutane 81 da rundunar take tuhuma da aikata laifuka daban-daban a Asaba, babban birnin Jihar ta Delta.

Inuwa y ace daga cikin mutanan da rundunar ta kama akwai wani mamallakin makarantar Grace Life International School, Oghara–Efe, Mista Michael Anigholor, wanda ake zargi da yi wa ‘yar yi wa kasa hidima fyade.

Inuwa ya bayyana cewa wanda ake tuhumar, wanda yake zaune a garin Oghata-Efe, da ke karamar hukumar Ethiope ta gabas, ‘yan sanda sun kama shi ne a bayan da wacce yay i wa fyaden ta kai karar sa a wajen ‘yan sandan.

Ya ce, “A ranar 14/01/2020, wacce ta kai kukan, wacce ‘yar aikin yi wa kasa hidima ce da take aikin nata a makarantar ta Grace Life International School, Oghata-Efe, ta yi zargin cewa a ranar 9 ga watan Janairu, 2020, ta je makarantar domin ta gabatar da kanta ta fara aikin.

“A bayan an dauki bayanan ta, sai wanda ake tuhumar mai suna, Michael Anigholor, wanda shi ne mai makarantar, ya dauke ta zuwa gidansa da ke Sapele, inda ya tursasa mata har yay i lalata da it aba tare da amincewar ta ba.

“An kama wanda ake tuhumar har ma an gabatar da shi a gaban kotun a shari’a mai lamba, MS/MUSC/02c/2020.

“Sauran masu laifukan da rundunar ta gabatar sun hada da wadanda ake tuhuma da aikata fashi da makami su 41, masu satar mutane guda Takwas, ‘Yan kungiyar asiri guda 16, masu kisan kai guda hudu, mutane biyar da ake zargi da sata, sai mutane Takwas da ake tuhuma da aikata yaudara
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: