Connect with us

WASANNI

‘Yan Wasan Damben Da Za Su Wakilci Kano A Gasar Wasanni Ta Kasa

Published

on

Sarkin shirya wasan dambe na Najeriya, Mamman Bashar Danliti, ya ce zai lashe zinare biyar a wasannin damben festibal da za a yi a shekara ta 2020 saboda a wannan shekarar yana jin babu kamarsa.

Jihar Edo ce za ta karbi bakuncin wasannin karo na 20 da za a yi tsakanin ranar 20 ga watan Maris zuwa 1 ga watan Afirilu sannan ana kuma sa ran lashe zinare 3,000 a wasanni 36 da jihohin kasar nan 36 za su kece raini har da babban birnin tarayya Abuja.

Mammam Bashar shi ne zai ja ragamar jihar Kano a wasannin gargajiya da suka hada da dambe da langa da kuma kokawa kuma a wasannin da aka yi a Abuja gasa ta 19, jihar Kano ta lashe zinare uku, inda Bahagon Sanin Kurna da Bahagon Shagon ‘Yan Sanda da kuma Abdurrazak Ebola suka zama gwanaye.

Sai Ali Kanin Bello da ya ci azurfa a nauyin ajin kilo 85, bayan da ya yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Mai Takwasara da ya wakilci jihar Edo sai dai a wannan shekarar Mai Takwasara ba zai halarci gasar ba saboda rashin kafiya.

‘Yan wasan da za su wakilci jihar Kano a damben festibal:

Ajin nauyi kilo 55 Bahagon Sanin Kurna

Ajin nauyi kilo 65 Autan Dan Bunza

Ajin nauyi kilo 75 Bahagon Shagon ‘Yan Sanda

Ajin nauyi kilo 85 Ali Kanin Bello

Ajin nauyi kilo 100 Abdurrazak Ebola
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: