Connect with us

CIWON 'YA MACE

Yawan Rokon Saurayi Babbar Illa Ce Mai Kashe Aure

Published

on

Masu karatu assalamu alaikum warahmtullahi taála wa barkatuh. Barkanku da jimirin bibiyarmu a kowane mako. Kamar yadda kuka sani, wannan fili na ciwon ‘ya mace, a kowane lokaci burinsa shi ne ya kawo muku abubuwan da za su fadakar, su ilmantar sannan har ma su nishadantar a fannin darussan rayuwa daban-daban, musamman kan abubuwan da suka shafi ‘yan’uwana mata da yaransu.

To kamar yadda muka fara magana a makon da ya gabata dangane da sakacin da iyaye mata ke yi wajen gaza tarbiyyantar da ‘ya’yansu mata yadda ake zamantakewar aure. Inda hakan kan jawo fitintinu da rashin zaman lafiya a gidajnesu na aure. Kamar yadda na yi bayani a makon da ya gabatan, wasu kan dora laifin hakan ga sauyin zamani, to amma abin da ya kamata mu sake dubawa shi ne, idan fa bera na da sata, to daddawa ma tana da wari, don haka kulawa ya kamata mu bai wa ‘ya’uan namu wajen tarbiyyantar da su dai-dai da yadda zamanin yake.

A wannan zamani iyaye musamman mata,yana da kyau mu kula da wassu abubuwa kafin aure da kuma bayan an yi aure. Duk wata uwa ta gari yakamata ta koyar da yaranta mata akan wannan, Yawan Roko .Wurin manemi aure ko kuma miji. Wasu iyayen dakansu suke kitsa wa yarinya abinda zata roka a wurin saurayi ko miji, wanda yin hakan ba daidai bane. Akwai aurarrarki da yawa da aka fasa ko aka samu tangarda bayan aure akan yawan roko.

 

 

Maigida ya san abin da ya dace ya yi ko saurayi yasan abin da zai yi wa mace ba tare da sai an roke shi ba. Kuma mu sa ni yawan roko na haifar da zubewar mutunci da rashin ganin daraja, ba kuma zai tsaya akan Ita yarinyar ba kawai, zai hada har da iyayenta. Domin gani za’a a yi irin tarbiyyar da ta samu kenan. Ina jan hankalin iyaye masu nunawa yaransu hanyoyin da za su bi su roki miji ko saurayi da su sani suna zubar da kimar su ne a idonsa. Domin idan yau sun roka sun samu, ba Lallai gobe su roka su samu ba daga nan kuma sai matsala ta biyo baya.

 

Hakan kuma ba zai yi tasiri ba har sai uwa ta kasance mai kiyaye wa a wurin maigida sannan yaran ma zasu dauki darasi daga haka. Mu karfafa musu neman na kai a madadin koya musu roko a wurin saurayi ko maigida, yin haka zai daga darajar yarinya da kuma iyayen bakidaya.

 

Allah ya bamu Ikon aikatawa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: