Connect with us

Fadakarwa

Yi Kokari Hankalinka Ya Zama Shi Ke Ma Jagoranci (1)

Published

on

Kiyayi katin gayyata kamar wannan daga sunayen Allah, Addini, siyasa, kabilanci da sauransu.

Mata du kiyaye hijabin su daga goyonsu a ko’ina. Wani fa’idodi mu da ‘ya’yan mu ke samu a kwanakun mako?.

Menene ilimi aiki da shi, gudun duniya da tinkarar lahira. Ba sauke karatun Alkur’ani kamar wannan ne, ba ahli ko fita hakkinsu ga ilimin addini ba, akwai son manzon Allah da yan gidansa, da sanin Allah daya da sifofinSa da yanda za’a bauta maSa, da kuma hakkokin iyaye da makusanta da shugabanni da mallamai da masu shekaru da nakasassu d.m mutum be samun duniya duka be kuma rasa ta duka, ka yawaita godiya ga abin da ka samu kada ka rena, albarka ne ke sa wadata ba yawa ba.

Abin da ka rasa kuma dun duniya ba Aljanna ba ne ka yi ta tuba da yi wa annabi salati sai Allah shi yafe ma zunuban ka ya ba ka Aljanna ya cika mizaninka da ladan zikirinka wanda ya fi ace ka cika bankin duniya da za ka bari, lada ke sababin kai mutum aljanna ba yawan tarin kudi ba, da ke yawaita hisabi ko ba’a wuta ba.

Dalilan Da Suka Jefa Kasa Cikin…

An mayar da addinin kamar yanda aka mayar da kasar, an yarda abu daya ne, amma kuma kowa nasa ko kansa yake ginawa, kuma ba’a yi komi ba.

Addinin mutanin kasa da irin nasu al’adu musamman manyan harsunansu da na addininsu, ba’a son amfani da su, a gida iyaye na koyar da yarensu, amma da ya bar gida shikenan sai ya dawo ya koma yana magana da harshen waje, na addinin kuma ba’a damu da koyon sa da shi ko yin amfani da shi ba, shi kuma turanci da ake gani zai taimaka wajen tarayya a gida da waje, ba kowa ne ke yin koyonsa ko iya shi ba sai ma’aikatan gwamnatu alhali yan kasa na so ne suyi amfani da harsunansu a kasarsu ko na addini a tarayya ko a waje domin larabci ya fi turanci yalwa da hikimomi wanda kusan babu yaren da be are shi ba, kuma a duniya ba inda be kai ba.

Hadisi kowa da fidira na musulumci aka haife shi sai in iyayensa sun mayar da shi bayahude

Ka kiyayi ganganci domin mai yawan karuwa ne da wuyan bari da gaskiya a cikin hankalinka komi tsawon lokaci kada ka saki Allah shi ke sa banna shedan ya same ka, domin kuskure mai zuwa ne ya wuce da sauri ko ya dawo da sauri idan aka gane bannanka kuskure ne to komi saurin aukuwarsa ana iya kar bar hanzarinka a san inda ko abinda ya dace da kai, amma in aka gane gangancinka komi kwarewan ka da cancanta in ba dole ba ba za’a karbi hanzarinka a kyale ka ba.

Kaifin hankalinka a yanzu ba kamar yanda yake dazu bane in ka gane kuren ka na dazu, to, haka za ka gane kuren yanzu amma nan gaba, shi yasa ake son kai ta gyara ma na baya da kai, kana nuna masu abin da ka gane; domin kada su sami koren da ka samu, kuma ka rika bin na gabanka da suke riga ka gyara kura kunanka da zaka gane nan gaba, domin su nuna maka tun kai ba ka sami kuskuren ba, sai kura kurenka su takaita bannanka su ragu, in ba ganganci kake yi ba.

Idan ka sami sababin kaiwa ga wani matsayi, to kada ka banzatar da wanda ya yi maka sababin, da kuma wanda ka samu ko abin da ka samu da kuma wanda ka sami ko abin da ka samu da sababin wanda ya yi maka sababin, da kuma baiwar da ta kai ka ga samun matsayin da ka samu, ka ji tsoron Allah ka rike gaskiya da girmama su wadanda can sosai su kana kallon daragarsu kamar na lokacin farko in ma har baka fifita su fiye da akan na farkon samunsu ba, domin yin haka ne zzai sa ka dore akan masayin ka da albarka, duk yanda ka girmama Allah (T.W.A) a duniya da dogara da shi, ba zai damu da kai ba, in ba kana adu’a da gode masa da neman ci gabanka da ganin darajan masu yi maka sababin ba, koda kowa ta hanyar saduwa da shi Allah (T.W.A) ne, nan ne ma yafi hadari in ba haka ba sai ya raba ka da wannan masayi da ka samu da sanin ka ko ba da sanin ka ba ya mayar da kai na baya da wannan abin ko da sababin wani ko ba da wani sababin da kai za ka gane ba.

Ba’a sauraren na baya in ga na gaba ko da kowa daukansu suna da gaskiya, aurayi da wuya ka sami jayayya tsakanin na gaba da na baya ka sami na bayar ke da gaskiya, sai in na gaban jahili ne ko mai mantuwa da rainin hankali azzalumi, dan hankali na boye ba ya kai na nagaba, kuma shi ba zai sani ba, in ba ya kai lokacin da zai sani ba, sai in nagaban ne ya koma baya ya sa na baya gaba yana nuna masa, shi kuma na bayan da ake sa a gaba ba zai ja da wnada ya gabatar da shi ko suka gabatar da shi ba, domi ba’a yin shugaba biyu in ba iyaye ba.

San da yawa aka samun kwarraru da suka cancanci shgabanci ana ganinsu kamar daidai wa daida dolensu su zabi guda da mataimakin sa, ba’a sanin wanda ya fi wani a tsakaninsu in ba da juriya da yin hakuri ba, in wanda aka gabatar bai jure ya yi hakuri ba su mai da shi baya komi kudinsa a kansu; domin kudi be kai sarauta ba.

Idan zama ya ki dadi dayan uku ne

Akwai wanda ake zalunta

Ko ake son a zalunta

Ko suna zaluntar juna guda y fi jin zafi, ko dai don an fi kwaransa ko kuma an fi shi karfin hali ko an fi shi juriya da hakuri ko an fisu

Rabuwar al, umma kamar ta aure ce, dole sai sun sami damuwa dukansu, sai daina wani ya fi na wani, saboda ba wanda ba za’a tuna ranarsa ba, da ba za’a samu ga wani in ba gare shi ba, ko kuma an sami wanda ya fi nasa ko kuma rasa irin nasa shine kansa in an raba an yi kome a hakura ko kuma a auri na uku a hakuri in an rabu a waiwayi boya a saduda sai mutuwa, ko in an manta, amma tarihi na ganar da mai hankali abin da aka yi bayansa da zai so ko ba zai so a maimaita ba.

Idan wani ya hau mulki yai ta zalumtar ku ko wasu ko ya taimaka ga zulumtar ku ko wasu, to ai ba laifi bane, bane, in kun hau ku rama ma kan ku ko wasunku gwargwado, kuma da fatar ba za ku sake ba.

Nuna kiyayya da wani a fili da mugur hurci ne ke sa in ya cutu ko ya mutu a ce kai ne ko in wani nashi ya mutu yace kai ne kuma in yana da sheda a goyi bayansa a gaban hukuma ko a kotu, in kai ba ka san shari’a ko hukuma ba.

Idan kana yawan cutar da mutum na kusa da kai ne ko na nisa, shi kum yana hakuri zai zo ya rinjaye ka in ba ku mutu ba, ko da kana ganin ka fi karfinsa ka yi hakuri ka rabu da shi ko da ramuwa kake yi, domin akwai mai cutarwa a boye da bayyane wani kawa dayansu yake yi, wani kowa tilas ne ko kuskure ke sa ya cutar da wani, wani ma kyautatawarsa ce cutar wan wani, sai Allah ne ke sanin komi kuma ba ya barin saka ma wanda ya yi zalunci ko aka yi masa tumma ba makusanta ko iyaye ba,

Mai cutar da kai ko wani a boye in kana ramawa a fili sai a ce kai ne ke cutar da shi amma iri kai hakuri kai za ka gane bai cure ko ba.

Wanda ya ba sihiri ko asiri gaskiya shine ke sarrafa shi kuma shine mai sanin makarinsa, in ya saba masa ya karye, amma wanda ya tsaya ma Allah, to, shi Allah a duniya na kowa ne wanda ya kama Allah da kyawo, in ba jaraba shi Allah ya so yi ba, kamar na Annabi musa (A.S) da fir’auna ya iya tsoata shi ko kuma komi ya tsaya kamar na manzon Allah (S.AW) kafin “kul’uzai” amma ba za’a iya halaka na Allah da wata aya ko wani asiri kamar wadanda suka saki Allah ba, in ba shine na ajali ba, amma asiri da sihiri na iya sababin a lalace ko a kasa yin abin da aka yi, shi kowa na Allah muddin bai bar Allah ba, aya da sihiri ko sun yi tasiri kadan ne zai yanke Allah zai bata shi, ba zai dore a kanna Allah ba.

Babu mai iya shiryar da wani sai Allah amma ba wanda ba zai iya batar da wani ba in ba manzon Allah ba.

Ana alfahari da yawan iyali ga mamaci sai dai yanzu ba’a son yaya su wuce uku, jikoki kada sukai goma tattaba kunni kar su kai talatin. Allah ya kiyauta ba.

Ba ka damuwa da mutuwar abin da ka mallaka sai domin yin hasarar da za ka yi sababin rashinsa tare da wasu masu an tana, to, shi Allah (T.W.A) ba ya da wata hasara ko da na sani akan kowa da komi saboda haka mutuwar abin shi ko lalacewar wani halitta da yardansa ne ba kamar ka ne mai hasara da nadama ba.

Wushishi ya rubuto daga Minna

08055736329

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: