Connect with us

WASANNI

Yobo Ya Zama Mataimakin Kocin Super Eagles

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta nada tsohon dan wasan tawagar kuma tsohon kyaftin din kasar, Joseph Yobo a matakin mai taimakawa kocin tawagar kwallon kafar kasar a wasannin kungiyar na gaba.

Yobo tsohon dan wasan Super Eagles zai maye gurbin Imama Amapakabo wanda hukumar ta sallama kuma tuni masana da kuma tsofaffin ‘yan wasan tawagar sun nuna farin cikinsu da wanann nadi da akayiwa Yobo.

Yobo ya buga wa Najeriya wasanni 100, bayan da ya fara buga mata wasa a watan Afirilun shekara ta 2001 a wasan shiga gasar kofin Afirka da kasar ta yi da Zambia kuma tun daga nan aka ci gaba da gayyatarsa

Tsohon dan wasan ya buga wa Super Eagles gasar kofin nahiyar Afirka sau shida a shekara ta 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da 2010 da kuma 2013 haka kuma ya buga wa Najeriya gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 2002 da 2010 da kuma 2014.

Tsohon dan wasan mai shekara 39 ya buga wasa a kasashen Turai biyar da ya hada Olympikue Marseille mai buga Ligue 1 da Fenerbahce a gasar Turkiya da kuma Eberton mai buga gasar firimiyar Ingila.

Sannan ya fara buga kwallon kafa a kungiyar kwallon kafa ta Michellin-Harcourt ta jihar Ribers a shekarar 1996, ya kuma yi wasa Standard Liege ta kasar Belgium da Tenerife ta Spaniya da kuma Norwich City ta Ingila.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: