Connect with us

ADABI

Muguntar Gwaiwa

Published

on

Yayyen mu da su ka girme mana ga shekaru a can gida, kauye, suna ba mu labarin shegantaku iri-iri na daga al’adun Malam Bahaushe da ya yi a da wadanda a yau ga su nan mu na ta ganin gyauron su suna tasowa sun kuma zame mana alakakai, fitina. Tasowar mu ma, mun ga wasu abaibadai da dama, na daga ire-iren wadannan halaye.

Musamman akwai wata al’adar banza da Bahaushe ya yi a da da ake kira kambaltu da mutum za ya yi shiga irin ta kurar daji ya rika tarbe matafiya ya na amshe masu dukiya. A kan zo da tsakar dare a ajiye dammunan layu a bisa gidan turwa. Sai a yi ta al’adu da kulunbotai, sannan a yi birgima a gidan turwar. To sai mutum ya tashi a siffar kura. Amma sai ya ajiye layun a nan ba za ya tafi da su ba. Idan ya tafi ya yi sata ko ya tarbe matafiya ya amshi dukiya ko ya koro dabbobi sai ya dawo ya yi birgima ya koma mutum, sannan ya dauki layunsa. Nan take. Amma an fi yin wannan a Arewacin kasashen Hausa.

Bayan wannan, a cikin sana’o’I masu muni akwai karuwanci da dadaro ko shege-ka-fasa. Akwai kwartanci; shi kuma, a nan, ana iya kiransa al’ada ko hali amma ba sana’a ba ce. Akwai bori da duba da dabo da samara. Akwai sana’ar wala-wala wadda ake yaudarar mutane ana amshe masu kudi a kasuwa. Akwai rawar maita, da sauran su.

Akwai kuma kashin-kasuwa ko zawon-kasuwa wanda masu yin wannan za su shiga jeji su debo wani hakki su ci, shi yana sanya zawo ko gudawa ne. To sai su rika bin kasuwanni suna bin layi-layi suna amsar kudi daga hannun jama’a. Idan mutum ya ki ba su kudi sai su wulkita, kansu na kallon kasa, kafafuwansu na kallon sama, su rika sakin zawo. Sai ya yi tsiri a sama sannan ya dawo ya koma a cikin dubura. A Kasar Sakkwato a na kiran su ‘yan-bashirwa. A wani yankin Katsina ana kiran su ‘yan-raba. Amma dai sun fi karfi a kasar Katsina. Amma dai sunan su na ainihi shine ‘yan kashin kasuwa.

Akwai abubuwa da al’adu na Malam Bahaushe da ma wasu sun saba ma shari’a da suka zama sana’o’I a kasar Hausa kuma an dade ana yin su. Duk wata sana’a ta kazanta da kyama sai ka ga Mallam Bahaushe ya amshe ta ya na yi musamman abin da ma ba ya cikin tsarin shari’a. A yanzu zamani ya zo duk ya kauda mafi yawancin su, saboda ma addini ya shiga cikin zukatan jama’a.Amma dai ‘ya’ya da jikoki ba su yada abubuwan da iyayensu su ka yi ba; sun dauki irin abin da kakanni su ka yi amma a wasu sigogi daban.

Hatta sana’o’in da ba su saba ma shari’a ba kamar su kira da wanzanci da fawa duk sai aka bata su da wasu al’adu wanda kusan sai an ma kauce ma Allah a yayin gabatar da su. To duk Bahaushen dauri ya aminta da wadannan al’adu.

Bari mu dawo kan abin da ya addabi Bahaushen yau kuma a zamanin yanzu-yanzu, watau fashi da makami da kuma garkuwa da mutane. Dama can akwai hanyoyin da ake bi ana yaudarar mutane ko ana kwace masu dukiya da karfi da yaji ba tun yau ba. Tun zamanin bayyanar Bahaushe aka san sata da fashi. Har ma a wancan zamani a kan kira karuwa da sunan uwar mugu ko uwar burgui ko uwar kusa saboda su ne ke boye barayi a dakunan su idan sun yo sata. Kuma har kullum abubuwan ba wai sun canza ba ne, saidai sigogin su ne su ka bambanta. Af, a yanzu ba ga shi ana yin mage-da-wuri ba? Tunda an kawo shari’ar musulunci ?

Fulani marasa addini wadanda ba Ehohi ba su aka fi sani da yawan kutsa kawunan su a cikin sata da fashi da makami, baya ga inyamurai da su ka fara kawo mana wadannan bakin al’adu. Da can, a wasu shekarun baya, kai har ma yanzu, an dauki Fulani sakarkari, wawaye, jakuna, dakikai, jahilai, ana kuma ganin su masu raunin addini da raunin imani.

Don haka ne ma lalatattun Hausawa da ke zaune a gari su ka rika yin lalata ko zina da matansu, masu kawo tallar nono da man shanu a gari suna sayarwa. Duk Bahaushen da ya tashi a Arewa, a karkara dai, ya san matan Fulani mazinata ne, mafi yawancin su. Kuma ba wasu mutane ba ne na daban su ka koya masu zina illa mutanen mu Hausawa; matasa da magidanta marasa tsoron Allah. To zinar da aka rika yi da su ne su ka rika komawa rugagensu suna tsugunnawa suna haihuwar ‘ya’ya shegu.

Yau, ga shi an wayi gari ‘ya’yan su din sun girma sun addabi al’umma sun hana su zama lafiya, sun hana kowa ma zaman lafiya. Dan sunna da aka samu ta hanyar auren da aka shafa fatiha ba zai yi abin da wadannan kafirai, kangararru ke yi ba. Su ne ke satar shanu, su ne ke yin fashi da makami, su ne ke zuwa rugar bafillace dan uwansu su kore masa dabbobi, su yi fasikanci da matarsa ko ‘yarsa. Su ne ke yin duk wasu haramtattun ayyuka na ashsha. Yau abin ya rikide ya koma garkuwa da mutane, da kuma abin da ma ya fi muni: su shigo gari akan babura su yi kan mai-uwa-da-wabi, na kisan wanda duk suka ci karo da shi; ko mace ko tsoho gajiyayye ko yara kanana. To duk illolin zinace-zinace ne suka jawo mana wadannan bala’o’I da fitintinu. Dama ita zina yado ta ke yi. Wannan abu ya kai bala’i. Wa’iyazu billahi.

Na yi imanin cewa kai da ganin wani ko wata bafillatana ka san ba bafillatana ta asali ba ce, wallahi summa tallahi kaduwa ce. Idan an yi mata kallon tsabta za a ga cewa karshe wani kado ne a gari ya yi ma uwarta cikin shege ta haife ta ba bafillatani mijinta ba. Abin da mu ka raina muka dauka sakarai,wanda mu ka kora dawa, a wasu lokutan ma har mu kan ba shi kiwon dabbobin mu, mu sallame shi, yau ya zame mana bala’i.

A yammacin kasar Katsina, a yankin kasar Pauwa an taba yin wasu Fulani a yamma da Kankara da su ka dade suna tarbe mutane matafiya suna yi masu fashi da makami. Wannan zance yana a tsakanin shekaru kusan 55 da suka gabata. Da ba a daukar masu matakin kirki ba ga shi yanzu sun hayayyafa sun yi ‘ya’ya da jikoki, su ne yanzu ke yin garkuwa da mutane. Hukuma ta san su sarai, mutanen wadannan karkaru sun san su. Har ma a wasu lokuta ana mu’amulla da su.

Hakazalika a kuma wasu ‘yan shekarun baya a Kankara, wasu daga cikin fulanin kan shigo cikin gari, amma tare da gudunmuwar samarin gari lalatattu masu kai masu bayanai. Idan sun zo, su kan bi gida-gida suna yin fashi da fasikanci da matan mutane, amma a unguwannin da suke a gefen gari. Amma gwamnati ba ta himmatu wajen maganin su ba. Wasunsu sun gudu zuwa kudancin kasarnan da su ka ga ‘yan banga sun fara mayar masu da martani.

Bugu da kari, ni kai na da ina yaro karami na san wata mata bafillatana mai sayar da nono a Kankara ana ce da ita Ade. Kullum idan ta kawo nono sai ta je wajen wani dan sanda ya yi fasikanci da ita sannan ta shiga gari tallah. Idan kuma ta gama tallar ta kan dawo nan dakinsa, ko da ba ya nan sai ta jira shi, idan ya dawo sai sun sake yin lalata sannan ta tafi rugar su. Kuma aure ke gare ta a lokacin. To akwai Fulani irin su Ade da ba su kirguwa. Daga bisani, da Allah Ya tash kama su da shi da ita duk ciwon sida ko kanjamau suka kashe su.

Fatar mu a anan Allah Ya sanya mana tsoron Sa mu nisanci zina don ita ce tushen ko mafarin duk wata fitina a doron kasa. Akwai hikayar Sheik Albani Zariya, da ya ce yanzu a yi fafutukar tsayar da bala’I ba ma maganin sa ba. Sai an tsayar da shi sannan za a yi maganin sa. Dama ita gwaiwa idan ta kasance a jikin mutum to shi za ta kassara ba wani ba.

Masu karatu, mu kwana nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: