Connect with us

TATTAUNAWA

Shekara 45 A Kan Karagar Mulki: Sarkin Zazzau Ya Yi Wa Addinin Musulunci Gaggarumin Hidima – Sheikh Jamilu Albani Samaru

Published

on

A makon jiya ne wakilinmu ya tattauna da Darakta Janar na gwamnatin jihar Kaduna akan harkokin da suka shafi addinin muslunci, (INERFAITH), Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru, in day a yi bayani a kan irin gudummawar da Mai martaba sarkin Zazzauza Alhaji Shehu Idris wajen yada koyarwar addinin kusulunci da kuma yadda ya yi tsaye na ganin ana zaune lafiya a lardin zazzau da jihar kaduna da ma Nijeriya baki daya. Yana wanna tsokacin ne a daidai lokacin da sarkin ke cika shekara 45 a kan karagar mulkin Zazzau, ga yadda hirar ta kasance.

Alhamdulillahi a daidai wannan lokaci mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris ya cika shekara 45 a kan karagar mulki yana sarauta, kuma yana daga cikin masu fada a ji a jihar Kaduna musamman a lardin Zazzau, ko me za ka ce yadda rayuwarsa ta kasance?

Da farko ina taya mai martaba murna na wannan tsawon lokaci, tsawon shekaru yana mulki, muna rokon Allah ya kara wa Sarki lafiya, Allah ya ja zamanin sarki ya kuma bashi ikon cigaba da ikon alkhairi da ya ke yi. Annabi sallallahu alaihi wasallam ya ce, ‘mafi akhairinku shi ne wanda shekarunsa suka yawaita kuma ya yawaita aikin alkhairi cikin shekarun.’ To muna fata Allah ya sa mai martaba cikin wannan da mu gaba daya. Na biyu shi ne mai martaba uba ne, jigo ne wanda ya bayar da gudummuwa da yawa wajen cigaban addini, ya bada gudummuwa ta bangarorin makarantun addini, gina su, da kuma ainihin kulawa da malaman. Akwai makarantar da ya gina wanda yawanci ma malaman daga kasashen Sudan aka kawo su daga kasashen Masar, na biyu ‘ya ‘yansa ma bai barsu ba sai da ya su suka yi karatu na addini mai zurfi ba wai dan shafa- shafa ba haka. To ta nan kenan, na biyu kuma gudummuwa ta wajen samar da zaman lafiya, in ka ji ana rigima a masallaci ko wajen waye za ka ji ana cewa akai wajen mai martaba, mai martaba shine uba shi zai sasanta yana da kwamiti na dattawan malamai masu mutunci a cikin al’umma wanda ko interbiew ne su suke wa limamai sannan a sa limaman sai ka ga an samu zaman lafiya, bayan haka na san da dadewa ya kan tara limamai na lardin bayan wata uku- uku, a zo a tattauna abubuwan da ke damun al’ummar musulmi, bayan an tattauna a samu matsaya kuma a tashi, ko nan na tsaya maka ka san mutum ya yi shekara arba’in da biyar yana wadannan abubuwan ka san ba karamin abu ba ne bayan za ka samu ana hidimomi in an je irin musabaka za a dawo ya sawa yaran albarka ya yi masu addu’a kuma duk shekara za ka ga shi ke nada gwarzon shekara ko dai ya tura ko ya je da kanshi, bare yanzu da shekaru suka dan ja wanda dole ka rage mai wasu abubuwa a cikin ayyukan da ya ke yi, so mutum ne gaskiya mai kima, fadarshi fada ce ta kowa, za ka ga mutanen izala za sa wa’azi na kasa ko na jiha, za ka ga fityanu su ma za su sa wa’azi a wajen su yi na kasa ko na jiha, kuma za a yi a gabanshi to inda ba mai son addini bane ai ba ruwanshi sai dai a zo a yi asharalle a wajen, amma za ka ga an sa wa’azin jiha ko na kasa manyan malamai sun so Kuma shima ya fito an yi da shi, kafin shekarunshi su ja akwai tarurruka da yawa wanda za ka ga shi da kanshi zai tashi ya je wurare; Jos… Ba sa iya kirguwa so wannan zaiji nuna maka gudummuwa shekarun gabadaya an yi su ne wajen ba da gudummuwa ga harkar addini, bayan nan za ka ga yana cikin wadanda suke zama Security Members na jihar Kaduna, Security Council kenan wadanda suke zama su ba da gudummuwa kusan tsarin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi yanzun kusan an dawo wa ma hakimai da kimarsu akan abinda ya shafi tsaro da sauransu da dagatai ma an yi meeting da su kusan mutum dari bakwai akan irin wannan, so wannan yana nuna maka irin gudummuwar da mai martaba ya ke bayarwa har scholarship ya ke bayarwa basu iya faduwa ko kididdiguwa a irin wadannan lokutan fatanmu shine Allah ya kara wa rayuwarsa albarka Allah ya ja kwananshi, Allah ya kara mai lafiya kuma Allah ya sa ya cigaba da shugabancinmu yadda ya ke adalci, abinda za mu yi mashi kenan, addu’o’i na alkhairi amma ba ka iya zuwa ka ce kai za ka kididdige ban sani ba tunda kai dan jarida ne kila kai za ka iys kididdigewa amma mu dai kam bamu iyawa.

To sai dai ban ji ka tabo bangaren yadda ake samun ya samu hadin kai ba har zuwa yanzu

To ai da ka ji abinda na fada da ba ka maimaita ba, mutumin da fadarshi ta zama ta kowanne bangare na addini

Ya Kake Ganin Yadda Mai Maraba Ya Hada Ka Al’umma Zazzau Bag Tare Da Njna Banbaci Ba Duk Kuwa Akwai Yawan Kabilu Daban Daban A Fadin Jihar Kaduna

Wannan magana ce kuma muhimmiya za ka samu a masarautarsa akwai kananan kabilu da idan ba a wannan jihar ba zai yi wahala a wasu jihohi suna da wannan damar, za ka samu an ce akwai sarkin Yarbawan Zazzau, akwai sarkin Zurun Zazzau, akwai sarkin kaza … Kuma duka nashi ne yana tattarasu lokaci daya har Igbo ma suna da nasu sarakunan sabanin yanzu in ka je Akwa Ibom ko wani waje zai yi wahala ka samu sai dai ‘yan kasuwa su tattara su ce ga sarkin kasuwan Hausawa amma ba a ce title a masaurata ba, so mai martaba yana wannan, kuma yana nuna kowacce al’umma dama Kaduna gidan kowa ne ba ka iya cewa ga wani mutum daya a’a kowa da kowa ne. Za ka ga duk wani babba yana sha’awar zama a Kaduna me ya sa saboda ba a nuna mai banbanci jihar Kaduna jiha ce ta samun dama, za ka ga mutum, duk su Adams Oshimhole da sauran mutane ai sun zauna a Kaduna sun rayu a Kaduna suna da gidajensu a Kaduna so in bacin mai martaba ya bada hadin kai a wajen wannan ai ba za a samu cigaba ba saboda gwamna zai zo ya wuce amma mai martaba na nan, yanzu kila za ka lissafo gwamnoni kusan talatin sun yi zamani da mai martaba kowannensu ya wuce tenure shi ya kare amma shi yana nan a mai martabarshi, yana nan a darajarsa shi ya sa kololuwa itace irin kujerarsu, to wannan dai shine kadan cikin abinda zan iya fadi nawa ina fatan Allah ya ja zamanin shi, Allah Ya karama sarki lafiya.

Ranka Ya Dade Mun Gode

Nima na Gode
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: