Connect with us

MAKALAR YAU

COMMUNITY POLICING: Mafita Ga Matsalolin ’Yan Sanda!

Published

on

Wannan sanin kowa ne cewa akwai matsaloli jibge a cikin aikin ‘yan sanda; ba wai a tsakankanin ‘yan sandan Nijeriya ba kawai, wannan matsalolin a na samunsu a cikin duk wata hukuma ta ‘yan sanda a fadin duniya.

Sau da yawa idan an ce matsalar ’yan sanda, sai mutum ya yi zaton wannan matsala ta fi kamari a Nijeriya, ko kuma da ‘yan sandan Nijeriya kadai a ke yi. Wanda sam ba haka ba ne, kawai dai saboda na mu a Nijeriya, ya wuce gona da iri ne, abin sai addu’a.

Ba na iya kirga artabun da na yi da ‘yan sanda; a wasu lokutan ni da kai na na ke waskewa don neman sauki, wasu lokutan kuma cijewa na ke yi, don ganin abun da ya turewa buzu nadi.

Wasu lokuta baya, mun je ‘CAFÉ’ tare da wani abokina, bayan mun fito za mu tafi, sai ga wata guguwa, motoci kamar a na yaki, kadan ya rage su bi ta kanmu. Mu ka yi gaggawan komawa. kurar na lafawa kawai sai gani na yi wai a she motocin ‘yan sanda ne har biyu ‘Patrol Van’; abun ya yi matukar daure min kai, wannan ya sa dole na ja gefe don ganin me zai faru.

Su ka diddiro daga cikin mota, kaitsaye su ka je su ka zagaye wata mota kirar ‘Honda’ da a ka ajiye ta a kofar wani Kemis. Ni dai ina kallon ikon Allah. Ba a jima ba, sai wani mutum ya fito daga cikin Kemis din, sai su ka ce mishi motarshi ce, ya ce a’a ta oganshi ce; oganshi din kuma soja ne, shi ma wai kuma soja ne. ‘yan Sandan nan su ka sa ke tayar da kura, su ka ce duk ‘yan kallo su baje. Ina gefe a inda na tsaya, ko gezau ban yi ba. Nan fa wani dan tsamurarre cikinsu ya matso kusa da ni ya ce, kai a na cewa kowa ya bace kai ka na tsaye ne. sai na ce mishi; ‘Ina so ne na ga abun da ke faruwa, saboda ni a wurina labari ne wannan da zafinshi’.

Dan sandan nan ya zaro ido, ya ce min ko in bar wurin ko kuma ya koya min hankali. Duk da ina fargabar rashin sanin irin abun da zai iya yi, amma haka nan na cije, na yi banza da shi. Ni dai ina saurare da kallon abun da ke faruwa tsakanin me motar da ogan ‘yan sanda. Ban ankare ba, kawai na ji wannan tsamurarren dan sanda ya hankade ni, na yi taga – taga zan fadi, ya sake bangaje ni.

Nan da nan fa kallo ya dawo bangarena. Ogansu ya bar waccan tattaunawar ya zo wurin, ya ce lafiya, sai dan sanda ya mayar mishi da zance. Ni kuma na zaro katin shaidar aikin jarida a aljihuna na nuna mishi. Nan da nan labara ya canza. Sai ogan nasu ya ce a dauke motar da su ka zagaye din, sannan kowa ya shiga mota su tafi. Ina tsaye ina kallon ikon Allah, a zuciyata har na fara tunanin da zaran sun yi gab azan bi su sai na ga kwakwaf.

Wancan tsamurarren dan sandan ne ya leko da kai ta bayan mota, ya ce min, ‘Idan ka isa ka biyo mu, mu kashe ka, mu kashe banza’. Hahaha, saboda sanin hali, dole ta sa na hakura da son jin zazzafan labarin harkallar mota tsakanin ‘yan sanda da ‘Sojan karya’.

Na yi ta yiwa kaina wasu tambayoyi, shin wancan dan sanda da gaske ya ke yi, idan na bi su za su iya kisa kawai don na ce ina son bibiyan labarin? Washegari ina karanta jarida, sai ga rahoton wani dan sanda ya harbe mai mota saboda kawai ya hana shi Naira 20. Gabana ya fadi, to mutumin da ya kashe wani saboda naira 20, me a ke tsammanin zai yiwa dan jaridan da ke son kawo cikas ga cucuwar motar da su ke kullawa?

Ina da labarai da yawa na karon batta da ‘yan sanda, amma zan sake bayar da wani kafin na yi bayanin mafita. Wata rana akwai wani abokina da ya kawo min ziyara, dan gidan sarauta ne, don haka a gidansu na garinmu ya sauka. Wuraren karfe 10:30 na dare sai ya kira ni a waya ya ce min motarshi babu man fetur, kuma da asuba ya ke son barin Kaduna, ya za a yi ya samu mai?

Ina gida, sai na ce ya fito ya dauke ni mu je neman man fetur din, duk da ni ma ba wani sanin gidan man da ke su ka kai dare na yi ba, amma ko irin na bumburutun nan mu ka samu sai a siya. Bayan da ya dauke ni, a ka yi min kwatancen inda za mu samu. Mun kma hanya kenan, sai ‘yan sanda su ka tare mu. Ina ganin haka na ce ma abokin nawa kar ya kuskura ya basu komi.

Dan sandan na lekowa cikin motar sai ya ce yallabai ya hanya, mu ka amsa shi da cewa, ai mu ba matafiya ba ne, yawon neman man fetur ma mu ke yi. Ba tsoron Allah kawai sai dan sandan ya ce, me zai samu. Ina gefe, sai na ce, babu abun da za ka samu. Wai wannan maganar ta ba dan sanda haushi. Sai ya wani ja numfashi ya ce a bashi takardun motar da mu ke ciki.

Motar ta na dauke ne da lambar masarauta. Sai abokina din ya ciro katin shaidar masarauta ya nuna ma dan sanda, sannan ya ce mishi, shi dan sarki ne. Dan sanda fay a kekyashe, ya ce, wai sai ya kira wani a gidansu ko kuma a masarautan tukunna. Nan da nan abokina ya kira wani dan uwanshi, wanda babban soja ne. su ka yi magana da dan sanda. Amma fa duk da haka, wai dan sanda neman wani abu ya ke yi, kafin ya bamu makullin mota. Ina ganin haka, na yi sauri na kira wani abokin aikina, wanda shi ne wakilin jaridar Leadership Hausa a garin, na sanar da shi abin da ke faruwa, na kuma bukaci ya aiko min da lambar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar. Ashe wannan wayan ma da na ke ta faman yi, dan sanda yayi matukar jin haushi.

A ka aiko min da lambar jami’in hulda da jama’a, na kira shi, na gabatar da kai na, sannan na gabatar da matsalar da a ke ciki. nan da nan jami’in ya ce min a wanne bangare ne abun ke faruwa, na sanar da shi. Sai ya kashe wayar. Nan da nan wannan dan sanda ya matso inda na ke; kafin ya karaso jami’in hulda da jama’a ya sake kira na. ko da na dauki wayar, shi kuma wancan dan sandan ya fara magana ya na cewa, ‘Idan ka is a ka kira I.G’. sai jami’in hulda da jama’a ya ce min, ‘Me ya ke cewa? Ashe ya ji me dan sanda ya ce…

 

Za a ci gaba mako mai zuwa in sha Allahu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: