Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Sakkwato Za Ta Yi Amfani Da Bashin Bilyan 65.7 A Ayyukan Raya Jiha

Published

on

tambuwal
Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta bayyana tsarinta na amfani da bashin naira biliyan 65.7 wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya jiha da ci-gaban al’umma da zuba jari a fannoni masu matukar muhimmanci.
Fannonin da Gwamnatin ta bayyana cewar za ta baiwa matukar kulawa sune aikin gona, kiyon lafiya, gina gidaje, shimfida hanyoyin mota da gadoji da kuma bunkasa haujin ilimi.
Da yake bayyana shirin bunkasa tattalin arzikin jiha a taron horaswa na jami’an Ma’aikatar Kudi da aka gudanar karshen mako a Lagas, Kwamishinan Ma’aikatar Kudi, Hon. Abdussamad Dasuki ya bayyana cewar Gwamnati ta fito da wannan tsarin ne domin mayar da jihar wajen da masu zuba jari za su rika zuwa.
Hon. Dasuki ya bayyana cewar bashin na biliyan 65.7 kan muhimman ayyuka a aikin gona, kiyon lafiya, samar da gidaje, inganta ilimi da samar da ruwan sha zai taimaka kwarai ainun wajen bunkasa tattalin arzikin jiha tare da sanya Sakkwato a matsayin jagora a fannin tattalin arziki a Nijeriya da Afrika.
“Kokarin mu na inganta tattalin arziki ta hanyar samar da kamfanoni masu zaman kan su ya fara haifar da da mai ido wanda ya hada da zuwan babban kamfanin takin zamani na duniya da babban kamfanin casar shinkafa na Aliko Dangote.” Ya bayyana.
“Baya ga wannan mun saukakawa al’umma yin kasuwanci cikin sauki a wannan jiha ta hanyar saukaka harkokin kasuwanci samun nasara tare da kirkiro sababbi.” In ji Dasuki.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewar Gwamnatin Tambuwal ta inganta tsarin biyan albashi tare da cire ma’aikatan bogi wanda ya taimakawa Jihar Sakkwato wajen biyan mafi karancin albashi na naira 30, 000 ga ma’aikatan jiha.
Ya ce “Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi nisa kwarai a shirin tallafawa al’umma wanda a yanzu haka an ware naira biliyan 4 domin rarrabawa ‘yan asalin jiha domin gudanar da sana’o’in da suke muradi.
“A kan wannan, ko wane daya daga cikin ‘yan wannan jiha da aka zaba za su samu naira dubu 20, 000. A yanzu haka an rarraba kudaden a Kananan Hukumomi 9 cikin 23.” In ji Dasuki
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: