Connect with us

KIWON LAFIYA

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka Ta Bayyana Mutane 70 Sun Mutu Sanadiyyar Lassa

Published

on

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa ko kuma (NCDC) ta bayyana cewa cutar zazzabin lassa a yanzu ita cutar ta yi  sanadiyar rasuwar  mutane 70 a Nijeriya.

Hukumar ta sanar da hakan ne a ratotan yaduwar cutar na mako na biyar da ya gabatar ranar Talata .

Rahotan ya nuna cewar mutane 109 ne suka kamu da wannan cuta har  ya zuwa wannan makon da ake tattara su bayanan.

Daga cikin mutane 109 da suka  kamu da cutar akwai ma’aikatan kiwon lafiya hudu daga jihohin Ondo, Delta da Kaduna.

Hukumar ta ce daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 9 ga watan Fabrairu hukumar ta gwada jinin mutane 1708, inda daga ciki kuma ta samu mutane 472 da suka kamu da cutar, sai kuma s wasu 70  da suka mutu daga kananan hukumomi 92 daga cikin jihohi 26.

NCDC ta bayyana cewar har yanzu jihohin Edo, Ondo da Ebonyi ne suka fi fama da ita cutar a kasar Nijeriya.

Sai kuma mata musamman masu shekaru daga 21 zuwa 30 sun fi kamuwa da cutar fiye da maza.

Akan  shi la’akarin da aka yi na wannan rahotan ma’aikatan kiwon lafiya sun yi korafin cewar gwamnati ta kasa taka rawan a zo a ganin wajen hana yaduwar ita cutar a kasar nan.

Ma’aikatan kiwon lafiyan sun ce ana warkewa daga cutar amma duk shekara sai cutar ta bullo a kasar nan inda na wani shekaran yafi na wani shekaran cutar da mutane.

Hanyoyin  kiyaye kamuwa da zazzabin Lassa

Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci kuma a kula da goggoge wuarare.

Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada a rika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin beraye da kuma Birai.

Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na yin magani datti a jikin su.

A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake ajiye abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

Tsafta: A yawaita wanke hannuwa da ruwa da sabulu kafin da kuma bayan an ci abinci sai kuma idan an kammala amfani da ban daki wato Masai

Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar da sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da ita a jikin wanda ya kamu  da cutar ya soke su.

Kona Daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye  daga daji zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

Wanke gawa a cikin daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin hakan a waje ne ko kuma inda ya kamata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: