Connect with us

LABARAI

Ku Shiga Harkokin Siyasa A Dama Da Ku- Sakon Minista Ga Matasa

Published

on

Karamar ministar sufuri, Sanata Rukayat Saraki, ta shawarci matasan Nijeriya da su shiga siyasa a dama da su.

A wata sanarwa da Jami’ar Ilorin ta fitar a ranar Lititin, ta ce Sanata Saraki ta bayyana hakan ne a yayin da take gabatar da jawabi na shekara-shekara karo na 47 da kungiyar dalibai masu karatun digiri sama da daya na Jami’ar Ilorin din, POGSASS suka shirya.

A jawabinta mai taken; bukatar shigar matasa cikin harkokin siyasar Nijeriya, Sanata Rukayyat ta ce shigar matasa siyasa zai bunkasa kyakkyawan shugabanci a dukkanin bangarorin gwamnatin.

Sanata Rukayyat Saraki, wanda har wala yau it ace Pro-Chancellor kuma shugabar hukumar gudanar da jami’ar Gwamnatin tarayya dake Otuoke, ta ce shigar matasa harkokin siyasa ba wai labari bane, abu ne da ya zama wajibi matasa su yi.

Ta bukaci masu ruwa da tsaki akan harkokin siyasa da su karfafi matasa wajen shiga harkokin siyasa a Nijeriya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: