Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Hafeez’

Published

on

Suna: Hafeez

Tsara Labari: Fauziyya D. Sulaiman

Kamfani: Maishadda Global Production Limited

Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda

Umarni: Ali Nuhu

Jarumai: Umar M. Sharif, Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Hassana Muhammad, Maryam Yahya, Amal Umar, Bilkisu Shema, Aisha Humaira, Abba El-Mustafa, Asma’u Sani, Jamila Umar Nagudu, Aisha Yola da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

 

A farkon fim din an nuna Salma (Aisha Humaira) suna hira da kanwarta Saudat (Amal Umar) a sannan ne kuma mahaifiyar su (Asma’u Sani) ta shigo dakin ta kira Salma da nufin taje wajen bakon saurayin ta Hafeez wanda yazo gidan, jin hakan ne yasa Saudat ta soma yabawa da Hafeez amma sai Salma tayi saurin dakatar da ita ta hanyar gargadin ta akan kada ta shiga sabgar sabon saurayin ta.

Sai dai kuma cikin rashin sa’a, bayan Salma ta fita zuwa wajen Hafeez tun a haduwar farko yaji bata birge shi ba saboda sabanin fahimta da suka samu wanda ya janyo sanadin day a mari Salma din kafin ya bar gidan. Amma kuma duk da wulakancin da yayiwa Salma mahaifiyar ta bata ji haushin abin ba sai ma laifin Salma din da take gani saboda ta bata mata shiri domin ta kasha kudi masu yawa a wajen malamai don a jawo mata hankalin Hafeez zuwa kan ‘yar ta saboda kasancewar shi dan masu kudi, a dalilin haka ne ma yasa bayan kanwar Salma ta samu mahaifiyar tasu da rokon a shawo mata kan Hafeez ko ita zai saurare ta, mahaifiyar ta su bata bata lokaci ba wajen daukar Saudat din suka nufi gidan iyayen Hafeez.

Amma duk da kasancewar mahaifiyar Hafeez wato Azeema (Jamila Nagudu) ta kasance aminiya ga Mahaifiyar su Salma (Asma’u Sani) Hakan bai sa Azeema tayi kokarin tilastawa Hafeez akan yayi soyayya da Saudat ba, domin shi dan gata ne sosai a wajen iyayen nasa wadanda ba sa son ganin abinda zai bata masa rai. Shima kuma Hafeez ko bayan day a shigo gidan ya hadu da Saudat sai ya fice daga gidan saboda ganin yadda take kallon shi, amma duk da haka sai da Saudat tabi bayan shi zuwa waje inda ta nuna masa cewar tana kaunar shi, nan Hafeez ya watsar da ita ba tare daya karbi soyayyar ta ba.

Shi dai Hafeez ya taso mutum me tsananin farin jini a wajen ‘yammata, duk budurwar da ta gan shi sai taji ya birge ta kuma ta fara soyayya da shi, akwai ba don komai ba sai don kyau da iya kwalliyar sa gami da kudin da mahaifin shi ya mallaka wanda ya ke takama da su. Babban abin takaicin kuma shine, Hafeez sam bai taba ganin yarinyar da ta birge shi ba akaf cikin ‘yammatan da suke zub da ajin su wajen nuna masa cewar suna son shi, gaba daya wulakanci yake yi musu bay a basu fuskar da zasu rayu tare, yayin da a kullum iyayen shi ba su da burin da ya wuce su ga yayi aure ya zauna da iyalinsa.

Hakan ne kuma ya sa iyayen shi suka bashi goyon baya wajen zuwa ya ga ‘yar abokin mahaifin sa ko za su daidaita har ya aure ta, amma cikin rashin sa’a Hafeez sai ya ga ita ma yarinyar ba ta birge shi ba, hakan yasa yayi mata kyautar kaya yayi tafiyar sa, wanda ganin haka sai ya yi wa mahaifin yarinyar ciwo (Abba Al-Mustafa) saboda yana matukar son Hafeez ya auri ‘yar shi ko don hakan ya zamo sanadin wani cikar burin sa, dalilin hakan ne yasa yaje ya sanar da mahaifin Hafeez wato (Yakubu Muhammad) cewar Hafeez ya amince da auren ‘yar sa, amma ko da mahaifin Hafeez ya tuntube sa sai ya nuna sam ba haka ba ne.

A na tsaka da haka ne Hafeez ya hadu da Safna (Hassana Muhammad) wadda ta kasance ‘yar talakawa, tun daga sanda ta taimakawa da Hafeez ruwa ya zuba a motar shi sai yaji ta birge shi har ya kamu da son ta, sai dai kuma tun daga lokaci na farko day a fara zuwa hira wajen ta yaci karo da mahaifin ta Malam Sada (Ali Nuhu) sai hankalin Hafeez ya tashi, domin ya taba cin zarafin Malam Sada ya ture shi da mota har yaji masa rauni kuma ya soma kokarin dukan Malam Sada din.

Ko da Hafeez ya fahimci cewar Malam Sada ne mahaifin Safna sai hankalin shi ya tashi, amma son da ya ke ma ta ne ya sa ya kasa hakuri da ita ya yi yunkurin turo iyayensa, sai dai kuma Malam Sada ya ki yarda da auren Hafeez da Safna saboda wulakancin da Hafeez din ya yi ma sa. Ganin yadda Hafeez ya rikice akan son Safna ne hakan ya sa iyayen sa su ke takaici saboda ba ‘yar masu kudi ya nema ba, amma son da suke yiwa Hafeez ne yasa suka yi ta kokarin ganin cewar an daidaita da mahaifin Safna, ana cikin haka kuma sai aka tashi mahaifin Safna wato Malam Sada daga gidan da yake haya, hakan ne yasa ya hada kan iyalan sa gaba daya ya koma kauye, duk da kafin tafiyar shi, mahaifin Hafeez yayi masa tayin muhalli amma Malam Sada ya ki amincewa, domin shi mutum ne me zafin zuciya da gudun abin hannun wasu.

Ko da Hafeez ya samu labarin cewa Safna sun koma kauye sai ya gujewa iyayen sa ya tafi kauyen su Safna don neman soyayyar ta. Bayan zuwan Hafeez kauyen ne da yadda yake yin wahala sai abin ya soma bawa Malam Sada tausayi wato mahaifin Safna har daga karshe ya amince da nadamar Hafeez sannan ya bawa Hafeez din dammar turo magabatan sa don ya aura mishi Safna.

 

Abubuwan Birgewa:

  1. Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa sannan an nuna tsantsar soyayya muhimmancin da jajircewa kan abinda mutum yake so.

  2. Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin bisa tsari ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari sosai.

  3. Sauti ya fita radau, hoto ma ba laifi

  4. Anyi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.

  5. Wakokin fim din sun yi dadi kuma sun nishadantar.

 

Kurakurai:

  1. Lokacin da Malam Sada (Ali Nuhu) ya je neman rancen kudi a wajen wani me kanti, da kuma lokacin da ya dawo gida sa’in da a ka yi ma sa rauni a kafar sa, muryoyin jaruman ba su hau da bakinsu ba a wuraren.

  2. An nuna cewar iyayen Hafeez masu kudi ne kuma su na nuna ma sa gata da tsantsar kulawa, amma kuma lokacin da Hafeez ya gujewa iyayen na sa ya tafi kauye wajen masoyiyar sa, me kallo bai ga sun yi yunkurin neman shi ba. Ya dace a nuna cewar sun watsa cigiyar sa ko da ta kafafen sadarwa ne.

  3. Mai kallo ya ga Hafeez ya taso cikin gata da sangarta daga wajen iyayen sa, wanda hakan ya ba shi damar da ya ke cin mutuncin duk wanda ya so, musamman na sama da shi, amma sai ga shi kuma lokacin da Hafeez ya gane kuskuren da ya yi wajen cin zarafin Malam Sada mahaifin budurwar sa, wanda har Hafeez din yabar gaban iyayen sa don neman soyayya da kuma yafiyar mahaifin budurwar tasa, duk da ganin faruwar hakan amma ba a nuna cewar iyayen Hafeez sun yi nadama ba a bias tafarkin da suka dora dan nasu na rashin tarbiyya, ya dace a nuna cewar sun yi nadama ko don ganin illar da rashin tarbiyya ta ja wa Hafeez wanda abin ya zamo sanadin da Hafeez ya nisance su.

  4. Shin wace irin sana’a mahaifin Hafeez ya ke yi ne? An nuna cewar Hafeez ya taso cikin gata da tunkaho da dukiyar mahaifin shi, sai dai kuma har fim din ya kare ba a nuna irin sana’ar da mahaifin nashi ya ke yi ba wadda ta say a mallaki dukiya me tarin yawan da ake fada.

 

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin yayi nasara wajen rike me kallo, sannan kuma an nuna tsantsar soyayya gami da muhimmin darasi akan wasu matasan masu ji da giyar kudi, wanda hakan ke sa wa su wulakanta makaskanta, yayin da daga karshe su ke yin nadama a kan hakan. Wallahu a’alamu!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: