Connect with us

LABARAI

ICPC Ta Bukaci Ma’aikatun Gwamnati Su Yi Koyi Da NIS A Kan Yaki Da Rashawa

Published

on

Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta ICPC ta yi kira ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati a daukacin fadin kasar nan su yi koyi da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa a cikin ayyukansu.

Shugaban Hukumar, Farfesa Bolaji Owasanoye ya yi kiran, sa’ilin da yake jawabi a taron bitar ayyukan kwangiloli da Hukumar NIS ta bayar a sassan kasar nan, da ya gudana a shalkwatar hukumar da ke Sauka a babban titin zuwa filin jiragen sama na Abuja.

Farfesa Bolaji wanda shugaban sashen tattara bayanan sirri da sanya ido na Hukumar ICPC, Mista Lawrence Abuo ya wakilta, ya yi bayanin cewa ba a taba samun wata hukuma ko ma’aikatar gwamnati da ta gayyaci hukumar na musamman domin ta sanya ido a kan yadda ake gabatar da bayanan irin kwangilolin da aka bayar a karkashinta ba, sai NIS.

“Muna da sashe da aka kebe domin sanya ido da bin diddigin al’amuran kwangilolin ayyuka da gwamnati take bayarwa. Amma NIS ita ce hukuma ta farko da take gayyatar ICPC ta zo ta gane wa idonta yadda ta bayar da ayyukan kwangiloli da yadda aka gudanar da su ko ake kan gudanarwa. Hakika NIS ta cancanci yabo a kan wannan. Kuma muna kira ga sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnati su yi koyi da NIS,” in ji shi.

Tun da farko da yake jawabi a wurin taron na yini biyu a kan bitar ayyukan da NIS ta bayar da kwangilolinsu da kuma kara wayar da kai a kan sabon tsarin biza da aka kaddamar kwanan baya, Shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya yi bayanin cewa bisa kudirin gwamnati mai ci yanzu na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da ayyukan gwamnati, sukan gayyaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa zuwa taronsu na bayyana yadda hukumar ta bayar da kwangilolin ayyukanta domin fitar da komai a fili babu kumbiya-kumbiya.

“Mun taru a nan ne domin gabatar da wasu muhimman ayyuka a yau da gobe. A yau za mu yi bitar ayyukan da muka bayar, kuma wannan ne karo na uku da muke yin hakan, dukkanmu a nan shaida ne a kan haka. Makasudin yin hakan a bayyana yake, shi ne domin mu kara karfafa gaskiya da rikon amana a takaninmu wajen tafiyar da shugabanci. Shi ya sa a koyaushe muke gayyatar Hukumar Yaki da Cin-hanci ta Kasa (ICPC). Kuma ina kira ga hukumar ta yi amfani da wannan a matsayin gwaji ga sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnati… Mun gudanar da ayyuka sosai a shekarar 2018 da ta 2019, shi ya sa NIS ta samu muhimman ayyukan da ba a taba gani ba tun kafuwarta,” in ji shi.

Babandede ya ci gaba da bayanin cewa shirya taron bitar ayyukan da NIS ke gudanarwa ya taimaka wajen warware wasu mishkiloli da ka iya tasowa musamman wurin takaddamar abin da ya shafi adadin kudin da aka bayar na aiki da kuma yanayin matsayin da aiki ya kai wajen kammalawa.

“Duk abin da muke yi a nan a bayyane yake, mun magance mishkilolin da ka iya tasowa na cewa kaza muka bayar na aiki, kuma wadanda ake bayar da aikin bisa kulawarsu su ce abin ba haka ba ne. Idan mun hadu wuri daya sai a yi keke-da-keke. Tun da aka nada ni Kwanturola Janar na NIS (shugaban hukumar) ban taba kiran wani Kwanturo na jiha na neme shi ya rattaba hannu a kan takardar shaidar kammala aiki ba saboda na san shi (don neman alfarma). Ban taba ce wa wani ya sanya hannu a takardar shaidar kammala aiki alhali ba a kai ga kammalawa ba sam. Ku ne za ku je ku duba ayyukan da kanku sannan ku tabbatar da cewa kun gamsu da aikin da aka yi, daga bisani ku rattaba hannu kuma daga nan duk abin da zai biyo baya ku za ku dauki alhakinsa. Haka muke gudanar da ayyukanmu.

“A bara mun kira ku wannan taron. A bana ma kowane kwanturola zai gabatar da bayanin ayyukan da aka bayar. Za mu duba adadin kudin da muka biya, kuma na ce a bai wa ICPC kwafin takardar bayanan ayyukan ita ma… Idan an samu matsala cewa aikin da aka yi bai yi dai-dai da adadin kudin da muka bayar ba sai mu yi bincike a kai, ita ma ICPC ta yi nata binciken. Ina tunanin wannan ita ce sahihiyar hanyar da za mu tabbatar da gaskiya da rikon amana wurin tafiyar da shugabanci. Mu fara yi wa kanmu hisabi kafin wasu su yi mana,” in ji Babandede.

Har ila yau, shugaban na NIS ya ce taron bitar ayyukan da hukumar ke bayarwa wata dama ce ta tattauna ire-iren ayyukan da hukumar za ta bayar a wannan shekarar ta 2020 tare da shugabanin hukumar na ressanta, domin a cewarsa su manyan shugabanni da suke Abuja ba su da masaniyar ayyukan da ressan hukumar na shiyyoyi da jihohi suka fi bukata kamar wadannan shugabannin nasu, “don haka za ku bayyana mana abubuwan da za ku fi ba su muhimmanci a 2020. Sai mu duba abubuwan da za mu aiwatar bisa kudin da yake hannu domin tabbatar da cewa mun zabi ayyukan da suka fi cancanta a aiwatar tare da ku, maimakon mu a Abuja mu zaban muku kadai, wannan ma ba zai ba da wata fa’ida ba.”

Taron bitar ayyukan dai wanda Kwanturola Janar na NIS, Muhammad Babandede ya jagoranta na shekarar 2019 da 2020 domin duba ayyukan kwangilolin da aka kammala, da wadanda ake kan gudanarwa da kuma wadanda aka yi watsi da su, ya samu halartar manyan shugabannin sassan hukumar guda takwas, da shugabannin manyan shiyyoyinta na sassan kasa guda takwas da Kwanturololin hukumar na jihohi 36 har da Birnin Tarayya Abuja, da sauran mataimakan kwanturololi na shalkwatar hukumar da kuma wadanda suke sassan hukumar na musamman.

A halin da ake ciki kuma, a cikin wata sanarwa da Jami’in yada labaran NIS, DCI Sunday James ya fitar ga manema labarai, Shugaban na NIS Muhammad Babandede ya bukaci kwanturololin hukumar na jihohi su tabbatar da sanya ido sosai a daukacin ayyukan da hukumar ke gudanarwa domin tabbatar da cewa ana tafiyar da komai bisa ka’ida tare da kai rahoton ‘yan kwangilolin da suke saba ayyukan da aka ba su domin daukar mataki a lokacin da ya dace.

Haka nan sanarwar ta bayyana cewa, Shugaban na NIS Babande, ya yi kira ga ‘yan jarida su rika bayar da rahotanninsu bisa kwararan bayanai na gaskiya bayan sun tantance daga hukumomin da suka dace, domin kauce wa bayar da labaran kanzon kurege.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai game da tsarin bayar da biza nan take yayin shiga kasa, Babandede ya jaddada cewa an bullo da tsarin bizar tare da kara yawan matakinsa daga shida zuwa 79 ne domin cimma muradun kasa da na masu nema, musamman bangaren kwararru da masu zuba jari da kuma saka karamcin da ake yi a duniya ta fuskar difilomasiyya domin tabbatar da tsaro, da bunkasar tattalin arziki da tafiyar da ayyuka bisa gaskiya da adalci.

Domin amintar da wasu ‘Yan Nijeriya a kan fargabar da suke yi ta sabon tsarin zai bai wa wasu bata- gari damar shigowa Nijeriya, CGI Babandede ya ce an dauki kwararan matakai na rigakafin hakan, “duk wanda zai nemi irin wannan bizar wajibi ne ya gabatar da bukatarsa tun kafin ya zo ta shafin intanet. Bayan tantance shi tare da tabbatar da sahihancinsa sai a ba shi takardar gabatarwa, zai zo da wannan takardar a hannu sannan a tantance ingancinta, daga nan sai a dauki bayanansa da tambarin yatsunsa ta kwamfuta, kafin daga bisani a ba shi bizar ta nan take. Don haka ‘Yan Nijeriya su kwantar da hankulansu, an dauki matakan tabbatar da tsaro a kan wannan,” in ji shi.

Har ila yau, Babandede ya nanata cewa bizar ba kyauta ba ce kamar yadda wasu suke yadawa.

Bugu da kari, da yake amsa tambaya game da rufe kan iyakokin kasa na kan-tudu, CGI Babandede ya bayyana cewa gwamnati ba ta rufe iyakokin ba ne bakidaya, illa an takaita abubuwan da ake gudanarwa ne domin ayyukan sintirin tsarkake kan-iyakokin da hadin gwiwar jami’an gwamnati ke yi, kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda yake Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya shi ne kadai zai ayyana lokacin da za a kawo karshen aikin na musamman, yana mai cewar, “ba mu rufe kan-iyakokinmu bakidaya ba, na sha nanata wannan. Illa dai muna budewa ne daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma kuma mu kulle. Kuma ba ana yin hakan ne domin kuntata wa kasashe makota ba kamar yadda wasu ke yamadidi a kai. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin haka ne domin daidaita al’amura ta yadda Nijeriya da mokatanta za su ci gajiyar abin bakidaya.”

Da ya juya kan batun ginin fasahar sadarwa ta zamani da ake gudanarwa a shalkwatar hukumar ta NIS kuwa, CGI Babandede ya bayyana alfanun ginin tare da bayyana cewa ana sa ran kammalawa nan da watan Yuni, “bayan kammala aikin wanda yanzu ma kusan an gama gini sauran kayan aikin da za a zuba, za mu dawo da dukkan bayananmu da muka adana a wurin hukumomin da muke kawance da su. Sannan ginin ba mu kadai a Nijeriya ba har da sauran kasashen duniya duk za su ci gajiyarsa,” ya bayyana.

A ranar Larabar nan za a kammala taron inda ake sa ran shugabannin hukumar ta NIS su ilmantu sosai da kundin sabon tsarin bizar Nijeriya da Shugaba Buhari ya kaddamar a kwanan baya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: