Connect with us

KANNYWOOD

Masu Cewa Mun Ki Aure, Su Fito Su Aure Mu – Fati Baffa

Published

on

Tsohuwar Jarumar Fim, wadda tauraruwarta ta yi haske a shekarun baya da suka wuce, Fati Baffa Fagge da aka fi sani da Fati Bararoji, ta bayyana shirinta na yin aure a duk lokacin da ta samu mijin da zai aure ta.

Jarumar ta bayyana haka ne, a lokacin da suke tattaunawa da Jaridar Demakaradiyya, dangane da rashin ganin ta da ba a yi tsawon lokaci a cikin harkar fina-finai na yanzu duk kuwa da cewa a shekarun baya tana cikin Jaruman da ake matukar ji da su a cikin wannan Masana’anta, amma yanzu shiru kwata-kwata an daina jin duriyarta, inda ta fara yin bayani kamar haka:
“To ka san komai yana da nasa dalilin, tsawon lokacin da aka yi ba a ganina, wasu matsaloli ne wadanda kuma zan iya cewa ba matsaloli ba ne. Domin kuwa, ka san cewa ita rayuwa a koda-yaushe ana so a samu ci-gaba a cikinta, duk dai da cewa harkar fim din shi ma akwai ci-gaba a cikinsa, amma idan kana ciki ya kamata a ce ka samu wata hanyar aiwatar da kasuwanci, wadda bayan fim akwai wani abu da mutum yake yi. Wannan shi ne dalilin da ya sa ba a gani na a harkokin fim yanzu, domin kuwa zan iya cewa yanzu haka na kai kusan shekara biyar ba a ganni a cikin fim ba”, in ji ta.

Ta kara da cewa, “duk da cewa yanzu ba a gani na ina shirya fim, amma yanzu ma haka akwai wasu fina-finai guda biyu da nake son zan yi su nan da dan wani lokaci. Don haka, ba wai na bar harkar fim gaba-daya ba ne, duk abin da ake yi a cikin harkar fim ina shiga ana yi da ni, kamar misali abinda ya shafi taronmu na ‘yan fim ko bikii kawaye da sauran Abokan arziki, duk muna haduwa muna yi. Saboda haka, mu ‘yan fim kan mu a hade ya ke.”

Da a ka tambayata akan harkokin kasuwancinta da kuma yadda za ta kwatanta rayuwarta ta baya da ta yanzu, sai Jarumar ta ce,“harkar fim Allah ya yi albarka a cikinta, to kuma yanzu mun raba kafa duk da cewa harkar fim tana da wahala, ita ma kuma haka harkar ta kasuwanci tana da nata irin wahalar. Amma dai dole haka za ka sadaukar da rayuwarka, ka hau jirgi ka tafi wata kasa kana fargabar zuwa ka  saro kaya ka zo ka sayar a nan, don haka kowanne yana da nasa wahalar.”

Haka kuma, da aka yi mata tambaya akan shirinta na yin aure sai Jarumar ta ce, “ai shi aure lokaci ne, kuma a yanzu ina nan ina shirin yi da yardar Allah, idan na samu miji ko yanzu a shirye nake dana yi aure, domin wasu sai ka ji suna cewa mun tsaya yin ruwan ido wanda kuma ba haka abin yake ba, idan da gaske suke yi su masu fadar hakan su fito su gwada mana cewa su na son auren mu. Don haka, duk wanda Allah Ya kawo min, ni zabin Allah nake nema da wanda zai so ni ya kuma girmama iyayena, ya rike ni amana”, a cewar Jarumar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: