Connect with us

LABARAI

Sarkin Gombe Ya Tabbatar Wa Muhammad Baba Sarautar Dan Adalan Gombe

Published

on

A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan uwa da abokan arziki da magoya bayan Alhaji Muhammad Baba Mabanni suka taro a fadar Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar na III dan yin godiya bisa ga tabbatar wa da Alhaji Muhammad Baba Mabanni Sarautar da ya nema a cikin watan Janairu na Dan Adalan Gombe.

Da ya ke godiya a madadin iyalan Muhammad Mabanni, babban Yayan Dan Adalan Gombe na farko Alhaji Gidado Mabanni, a fadar ta Sarkin na Gombe yace  kamar yadda suka nemi wannan sarauta acan baya a watan Janairu yanzu Sarki ya tabbatar musu hakan tasa su ka zo godiya bisa wannan karamci da a ka yi mu su.

Gidado Mabanni, yace adalcin Sarkin ne yasa da suka nemi wannan sarauta aka nemi su jira a duba wacce tafi dacewa da shi cikin ikon Allah kuwa Sarki ya aika musu da cewa an basu shi ne suka zo godiya.

Ya yi amfani da wannan damar ya shaidawa fada cewa in sha Allah za’a samu Alhaji Baba da rikon amana domin tun can ma dama shi mai amana ne bai da yawan fadade dan haka zai rike sirrin masarautar Gombe

Da yake jawabi a madadin Mai Martaba Sarkin Gombe Yeriman Gombe Alhaji Abdulkadir Abubakar, wanda shi ne Hakimin cikin garin Gombe da kewaye ya adalci irin na mai martaba ne yasa da suka nemi wannan sarauta shi kuma da yan   majalisun sa suka duba suka yi nazari suka ga ya dace aka ba shi wannan sarauta da ya nema.

Yeriman Gombe ya kara da cewa yabon da ake yiwa Sarki na kyawawan halayen sa ya yi koyi ne a wajen Mahaifin sa Marigayi Sarki Shehu, wanda duk jihar Gombe kowa yake yabo bisa halin kwarai.

Ya yi kira ga sabon Dan Adalan Gombe da ya kasance mai sirri dan kar suyi shawara da Mai Martaba ya dinga gayawa mutane abunda suka yi dan fada ita tana da sirri.

Ya kuma ce ya gane fa yanzu wani nauyi ya dauro akan sa na yiwa Sarki hidima domin duk lokacin da Sarki ya tashi da wata bukata ko ya yi baki za’a iya neman gudumawar sa domin Sarki bai daukar bukatun sa shi da kan sa.

Daga nan sai ya umurce shi da cewa ita ya shirya cikin watanni uku za’a iya masa wankan nadi idan kuma ya jinkirta to sai ya kai wata shida dan haka ya rage nasa ya duba ya gaggauta shirin sa dan a masa bikin nadi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: